Skip to content
Part 8 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Yadda Nadiya ta taho a guje tamkar zata tashi sama saboda haushin sakin Tero da akayi wanda yayi matukar bata mata rai don yadda taso a batar mata da Tero ya gane ya tabo yar GIDAN KUDI amma kuma shi waye da ake fada mata shima ZINARE ne irin ta?

Sai tsaki take ta ja tamkar wata tsaka ko wacce zata tsige harshen ta inda wayar ta take ta kara show yana kira amma bata ko bi ta kan wayar ba.

Wani tsoho da yake bara kan titin kallo daya zaka yi mishi ka gane bashi da cikakkiyar lafiya ma yana tafe dogare da sanda Yana tafiyar a hankali Alamar banda ciwon tsufa ma akwai ciwon gangar jiki don haka yake tafe sannu a hankali yana fadin,

“Allazi wahidun Allah da girma yake.

Can tsallake ya hangi almajirai sunyi layi layi ana raba musu sadakar waina don haka ya soma duba hanyar da son tsallake wa ya samo wainar inda kuma Nadiya ta auno a guje tamkar walkiya daidai da tsohon ya raba kafa zuwa ketare titin tamkar walkiya haka nadiya ta darzo ta kumayi gaba da tsohon nan wanda tarin gajiya ma kadai yana iya kaishi k’asa amma haka Nadiya tayi mishi dauka daya ta watsar a gefen titi ta kuma wuce abinta tamkar ta shuri iskan kan titin ko ta juyo duk da taga tahowar tsohon amma a haka tayi mishi wannan daukar ta rashin mutunci kuma ta wuce abinta .

Wata irin murginawa da tsohon yayi ya kuma kifa Yana hantsilawa dole ta tab’a zuciyar mai Imani yayin da goshin sa da gefen fuskar shi ya fashe jini ya wanke fuskar yayin da sashi sashi na jikin shi ya goje wani wuri kuma karaya har da su tsagewar k’ashi dai tsohon yayi domin kuwa lokacin da mutanen suka kawo mishi taimakon agaji tuni ya some baya ko numfashi.

Wasu daga cikin fusataccin matasan da akayi hakan akan idon su tuni suka dauki mashi na suka rufawa motar  Nadiya baya a fusace da son su riske ta a hanya

tuni aka kwashi tsohon zuwa asibiti don fuskar shi sai zubar jini take yayin da hannun shi ma yake Lilo Alamar karaya ce a hannun.

motar Nadiya tana cikin sheka uban gudu yayin da matasan nan  suka kurewa mashin nan gudu sai gasu wani dan ta kife yasha gaban motar Nadiya babu ko tsoron mai zai je yazo .

wani Uban burki da ya dauki amo da karar kuuuuwwww duk da babu zato nadiya taga mashin din wanda rashin sani yasa ta tsaya wa da ta san muguntar da ta baro baya ce ta biyo ta da babu ko shakka ta yi ciki da mai tsautsayin da ya fado gaban ta ta mutsuke shi fiye da wanda tayi a baya.

kan kace me? taji an daki gilashin bayan motar yayi wata irin Kara ta rashin mutunci tatss tatsss.

ta juyo da sauri In da taga wani matashi ne rike da katon icce ya daga yana makawa.

kafin ta san abinyi taga wani shima ya makawa gilashin gaban icce .

“Sakawa shegiya taya ta K’one shegiya azzaluma in Uban ta ne akayiwa hakan zata ji dadi ? shegiya yar ta shegiya yau kwanan ki ya kare wallahi.

haka ta jiyo wani tantiri yana fada yana Mai shirin bankawa motar fetur ya kyasta Ashana.

tuni mutane sukayi tsuntsuma suna kallon ikon Allah yayin da masu hankalin ciki kuma suke ta neman kashe rigamar don ganin ana shirin migun Aikin.

Aka rike mai shirin kwara fetur a motar yayin da Nadiya kuma tayi kuru kuru a motar ido kwal kwal bakin rashin kunya ya mutu taga iyayen ta a rashin kirki.

Ana janye matashin da yake shirin kyasta mata wuta wanda bakin shi baiyi shiru daga auna mata manyan asharai marasa tsarki ba yana hararo ta tana tabbatar da wancan in aka barshi zai iya fiye da abinda yake nufi.

tana ji matashin yana fadin wani tsoho ta banke kuma bata iya tsayawa ba taga halin da yake ita tsinanniyar ta tako mota ta gudu ta baro tsohon wanda ake kyautata zaton ma ya mutu.

tana jin hakan ta figi motar da wani irin matsiyacin gudu ta bace daga wurin don ta tabbatar a yanzu kam wancan fusataccen matashin idan ya samu dama ita kam sai wata ba ita ba don haka ta zabi samfewa.

“Kaga yar ta shegiyar ta samfe ko? ka gani ka gani? .

“Ku barta da Allah dama haka mafi yawan su sake   su banke mutun kuma su gudu Allah ya hada su da daidai su.

tuni Nadiya ta bacewa ganin su dole suka koma suka kyale ta amma kan ta sha zagi fiye da zagar zogale

tana dosowa gidan su ta sauke ajiyar zuciya don sanin ta sha tunda tazo gida

Kaisar yana zaune akan shillo shi da king wanda ya zo mishi ziyara suna cikin fira sai ga shigowar motar Nadiya wacce bata kula dasu ba saboda hankalin ta a tashe yake don haka da sauri ta fice daga motar har tana waiwaye.

da sauri king ya mike tsaye yana fadin

“Kai ? Wallahi wata kamar yarinyar nan da muka hadu da ita a gold and silver kaisar? .

Kaisar yayi murmushi yana Fadin

“In ka fidda kamar ma king zan iya ce maka itace.

“Kace shiyasa baka kuma min sambatun ta ba amma ta yaya akayi hakan? nan gidan take ? Ko kuwa yaya abin yake?.

“Ai yar gidan ce king sunan ta Nadiya baka ga har kiba nayi ba saboda kwanciyar hankali da fidda shakku da fargaba tunda gani ga sweetie dealing?.

“Kai wai tsaya da Allah meye alakar ka da mai gidan nan?.

“Mu rufe wannan maganar king ba yanzu ba taso mu shiga ciki ku gaisa da masoyiya ta.

“Kana nufin ka samo kanta kenan?

“Ina fa ? Ai yakin soyayya king a biyu yakke ko Kai ko shi amma na san zanyi nasara don haka taso muje ciki.

Ya figi hannun king suka shiga cikin gidan inda fati ke ta shirya tebur da abincin rana tana ganin kaisar tayi murmushi tana fadin

“Yaya kaisar yanzu na leka kofar ka ban same ka ba ko kayi bak’o ne? ta fada tana gaishe da king wanda ya amsa Yana murmushi don yarinyar ta burge shi tana da wayewa.

“Wallahi Ina bakin get fatima aboki na ne yaxo muna can muna fira .

“Dama abincin ka ne na mika maka ko kana son wani Abu ne?

“Nagode sosai sister bana bukatar komai Ina mama ina nadiya? Mama tana sallah Nadiya kuma yanzu naga ta shigo kana son ganin ta ne?.

“Eh da Ina so su gaisa da king ne amma barta kawai kice mata Ina son ganin ta in ta fito.

“Ok to bari ma na sanar mata .

ta wuce dakin su shi kuma shi da king suka fice zuwa dakin nashi.

fati ta shiga dakin inda ta iske Nadiya na waya tana fadin

“Wai fa daga na banke wani gajiyayyen tsoho shikenan akayi min wannan wulakancin to ko kudin tsiya akayi mishi ba zan iya siye shi ba? sun fasa min gilashin mota duk sai dai nace daddy ya canza min wata don na gama hawa waccan motar wallahi .

fati ta tayar da sallar ta har Nadiya ta gama wayar inda take isar da sakon kaisar na son ganin Nadiya.

“To munafukar karshen duniya kin labe ne kiji abinda nake fada don kije ki yaya ta ni ki shelantaww duniya halin da nake ciki hala? waye kuma haka kaisar ? In dai wancan matsiyacin ne Wanda talauci ya koro daga shiyyar su sai nace uban ku ke da shi mai sakon da ke yar Aiken  ki fada mishi uwar shi da uban shi idan ya kuma Kama sunana a bakin shi .

“Allah ya baki hakuri anty Nadiya amma don Allah don annabi ki daina cewa musulmi matsiyaci babu fa matsiyaci sai dan wuta kuma cika bakin da kike kin San abinda gobe zatayi? babu fa wanda ya san gobe sai allah.

“In ba matsiyacin bane meye? Ai ke da shi duk jirgi daya ya kwaso ku wai ku kam wane irin laifi kukayi wa Ubangiji ya yi ku matsiyata? .

“Bama tare da tsiya wallahi tunda yayi mu cikin Al ummar ANNABI ya kuma yi mu cikin musulunci wallahi munyiwa tsiya tazara ba kudi ne arziki ba arzikin yana nan ga zuciya mai k’ana A da sanin cewa samu da rashi duka na Allah ne ai tsiya ta na nan ga mai yi yayi gori ko kuma ya nunawa mutane gadara da izza akan abinda bai da tsimi balle dabara Allah ta ala yayi mana tsari da talauci ya kuma azurta mu da arzikin sa madaukaki ko a haka alhamdulillahi mun gama babban arziki tunda muka samu kalmar la ilaha illallah Muhammadur Rasulullah .

“Ni kike gayawa wannan maganar? to zaki ga abinda zai faru .

“Babu abunda zai faru sai alheri.

eewar fati wacce ta fice daga dakin.

Daddy wanda ya biyo hanyar da aka tare Nadiya inda ake mayar da zancen cewa wani dattijo ta banke  kuma ta gudu Bata tsaya ba shiyasa ma fusataccin matasan suka biyo bayan ta suna shirin kona motar ta .

ya fito daga motar shi yana shiga cikin masu bayar da hakuri kafin ya juyo yaji matashin yana fadin

“Kaga ta gudu ko?

ya juyo yaga nadiya ta suna a guje ya cika da mamaki kafin ya ajiye mamakin shi a gefe guda yace da matasan suje ya ga tsohon da ta banke.

Ai kuwa suna zuwa suka tara’s an wuce tsohon asibiti amma jinin da ya gani a k’asa shi ya tabbatar mishi da ba karamin buguwa yayi ba don hakan da sauri ya nemi asibitin da aka tafi kai tsohon ya kuma Isa asibitin sai dai ya tara’s da wani abun mamaki domin kuwa mutanen da suka kawo tsohon ne suke ta ta ajibin inda tsohon ya shige don an neme shi sama da kasa babu shi babu dalilin shi a cikin dakin bayan kuma sun tabbatar da har kan gadon suka dora shi ana jiran likita ya karaso amma tamkar mai layer zana babu shi babu dalilin sa  abinda ya daurewa kowa kai da mamaki tsohon da aka kawo a sume ta yaya ya farka har ya fice daga dakin babu wanda ya ganshi?

<< Azurfa Da Zinari 7Azurfa Da Zinari 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×