Skip to content
Part 81 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Abinda kuma baiyi musu dadi ba kenan sai Aka sami wasu mara’s tsoron Allah suka kullaci farar Aniyar sa tare da shan alwashin sai an ga bayan sa ba tare da in ya juya zaiyi tafiya ba

Bai San abinda ake shirya mishi ba bawan Allah yana ta hidimar gaban sa har Allah yasa Yana da Rabon karuwa da wanda zasuyi mishi Dakon kayan zunubin .

Al Amarin Allah wanda yake a cikin kaulasan zanen kaddarar bawa kuwa baya sauyawa Allah ya zanawa Alh Sani wannan kaddarar wadda muke fatan ta zame mishi alheri

Da sannu sannu asarori suka soma bibiyar bawan Allah wanda suka zamo sanadin tafka asara wacce ta fara girgiza tattalin arzikin sa bawan Allah sai yace daga Allah muke kuma ga Allah zamu koma.

Asarar farko atamfa ce yar ingila mai daraja akayi oder ta contener guda amma ana sauke ta aka ganta dauke da sunan Allah mai girma shi da kanshi ya bayar da umurnin toye ta don baya fatan kafuran da sukayi hakan su cimma nasara don haka ya barwa Allah wanna kaddarar ya kuma gwammace gara ya Rasa koma me ya sami da ace anci zarafin musulunci Yana da yadda zaiyi bai yi ba.

Haka ya tafka wannan asarar ya kuma roki Allah yasa hakan ya zama silar wani alherin ne zai saukar gareshi.

Ba a rufe wata biyu da samun wannan kaddarar ba sai kuma ga wata wacce ta shafe wacce sau linkin ba linkin . shima oder ce akayi ta madarar ruwa ta gwangwani mallakin k’asar faransa wacce tazo daidai da batancin da sukayiwa shugaban halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam wanda har aka juyawa kayan su baya ba a siyen duk wani Abu da ya fito daga k’asar ta faransa shima nan Alh Sani yace a juya da tarin kayan wanda tarragon jirgin kasa ya kwaso nan ma Alh Sani ya kare janabin manzon Allah ya yarda gara asarar da dai tab’a mutuncin ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam.

Idan lamarin Allah  ya sauka to abar shi  da ikon sa kawai. domin kuwa idan ya sakarwa bawa kaddara babu nai hana wanzar da hakan kamar yadda ya so ya wanzar wa Alh Sani kaddara mai Rad’ad’i wacce I’mani kurum ke tseratar da bawa.

Haka Al amura sukayi ta faruwa ga bawan Allah Alh Sani Wandw kaddarorin sa sukayi ta sauka tamkar ya’yan carbi wata biye da wata amma duka karfin I’mani ya tabbatar da shi akan komai daga Allah yake kuma zai wuce . ko ma Bai wuce ba matukar dai baiyi kan tafi da I’mani ba to mai sauki ne . lamarin da zai sa a rasa I’mani wannan kam shine asara mafi muni.,.

Aka samu da kyar da kyar aka harhada kudaden da aka siyo kayan bulawun na yara saboda kasantowar sallar azumi wacce ake neman kayan yara don bikin salla . kayan da suka taho kuma costume suka Rike su suka hana kasuwar da ba ayi ba kenan gashi duk an narka dukiya an suyi kayan Babu kuma wasu kudi da za a juya wani jari.

Kai Al amarin Alh Sani ya soma zama Allah sarki domin kuwa Abincin da za aci a rana sau uku Yana neman gagara ga tarin yan uwa da dangi wanda suke cike da Jin sauki da afuwa amma aka kasa samun wani guda daya da zai agazawa Alh Sani duk da kuwa alwai Alh Rabi u dan uwan sa ne dan dakin Haj kaltume ne  shima yana cike da jin saukin garin amma bai da wannan zuciyar zumuncin bare kuma taimako da yanzu sai wane da wane duk wanda kaga yayi shi ma ta mai rabon rabauta ne a duniya.

Tuni Dija da haj kaltume suka soma yada halin da alh Sani yake ciki da cewa hanne ce wai ta zamo musu zuwan balaki Sani ya jawowa kansa mai farar kafa gashi nan sai tsiyacewa Yake

Bai kula da wadan nan maganganun ba don shi yanzu yafi son ya ga ta yadda za ayi kayan can da costume suka kama su fita amma ba maganganun jahilci ba.

Alh Sani ya soma kokarin neman Rance don a rike wani abu yayin tunkarar costume

Ya sami da kyar ya samu Rancen kudi aka shiga Yaya za ayi,? har Allah yasa aka samu wani da Yake da wani a cikin gwamnati ya shiga gaba har aka samu kayan Alh Sani suka fito amma fa an badda kudade amma anyi ta barka kaya sun fito sai dai me,? fitar kayan ya sa suka gane kayan ma sun zama Expired da ka ike irga kaja ta ko yaya ne zata dare ta kece . gaba daya kayan sun lalace da an Sani ma ba a kad’ar da kudade masu daraja don karbo su ba amma yaya Bawa ya iya da kaddarar sa? sai dai in Alkalamin Bai zana ba.

Wannan al amari ya tab’a zuciyar Alh Sani bawan Allah amma yayi fata da burin Ubangiji ya mayar mishi da mafi alheri abinda ya tsaya mishi kuwa shine kudaden mutane da yaci bashi duk da yana kyautata zaton zasu daga mishi kafa kasancewar Babu wanda bai ci alfarmar sa ba amma abunda Alh Sani ya manta dan Adam a yau bakin kaza gareshi yaci ya goge baki wanda ka taimaka shi ke son ya ga tashin hankalin ka koma asirin ka ya tonu. Bai sha mamaki ba sai da mutanen da Yake bawa tabbaccin zasu iya Rufa mishi asiri suka addabe shi da son kudaden su .

Al Amarin da ya motsa zuciyar sa matuka gaya domin kuwa shi da kanshi ya san bashi da halin kudaden nan a yanzu amma Allah mai suna arrahamanu wanda ya sa shi yayi hikimar siyen kaddarori lokacin da duniyar take garawa Sai yaga da abin sa ba zaiji kunya ba sai ya siyar da wata haraba da ya siya can da dadewa sai ga kudi masu nauyi sun sauka abin haushi Alh Rabi u dan uwa na Alh Sani shine ya siyi harabar ya biya bai iya fidda dan uwan sa saga wannan taskun ba amma an fiddo kaddara ya siye kai Anya kuwa muna neman tsira a Ranar gobe Alkiyama? Kai kamar da wuya wallahi sai munyi kamar munayi in kuwa ba haka ba to wallahi sai yadda ta yuwu wai dan daudu a LAHIRA.

Alh Sani ya biya mutane kudaden su ya zauna lafiya sauran kudi kuma aka siyi abinci aka aje

Sauyin Rayuwa sosai ya samu Alh Sani yayin da Dija ta soma fidda mugun halin ta a fili na kasawa da gajiyawa akan wannan Rayuwar da take ganin an tauye ta.

Wulakanci kala kala Dija bata Jin wahalar wanke Alh Sani da kowane irin kalar wulakanci wanda yake nuna ta gaji da zama dashi amma yayi mata uzurin bata saba ganin abinda take gani a yanzu ba.

Hanne ce mai bashi baki da magana akan komai ya samu bawa da sanin Allah kuma kowace kaddara da alherin ta sai dai wani alherin ba na nan duniya bane na Ranar gobe Alkiyama ne. Wanna matashiya da hanne take mishi tana kara burge shi ya gane kowa da kalar baiwar sa .

Rayuwa ta tafi cike da tarin kalubale amma Alh Sani Yana ta godiya ga Ubangiji wanda ya tufa asirin sa matuka gaya baije ga yan uwa yana rokon a taimaka mishi da abunda zai bawa iyalan sa ba

Baya zuwa ko ina yana gida yana karatun Al kur Ani mai girma dai daiku daga cikin wanda basu zama masu bakin kaza ba wanda suka cika yan halal sukan zo su gaishe shi wasu su bashi kudi wasu kuma Kayan abinci zasu sauke mishi hakan ke tabbatar mishi da lallai alheri alheri ne bai kumayi kama da sharri ba ko a Suna da suffa.

Ciwo ya soma sarkar Alh Sani wanda ya fara kamar wasa har dai aka dangana asibiti amma duk want gwaji aune aune babu inda want ciwo ya fito. babu hawan jini Babu suga babu diabetes smma kuma lafiya tayi karanci.

Haka aka dawo gida hanne ce kan gaba wurin kulawa da shi yayin da Dija take ganin anzo gabar da zata fahimtar dasu ta gaji in ma basu gane da yaren da take magana ba zatayi musu hausar da suke fahimta don babu hadi bare mahadin da zata zauna zaman jinya ko kuma tsautsayin takaba ya zaunar da ita

Kullum ciwon Alh Sani sauya salo yake don haka hanne ta ga dacewar a koma na hausa da Al kur Ani sai ake na hausa wanda yau za a tashi garau kamar ba ayi ciwo ba gobe kuma a koma gidan jiya koma fin jiyan.

Dija ta Isa gidan Haj kaltume tana fada mata ita kam ta gaji da wannan zaman wabda babu ranar tashi gara a sallame ta ta kara gaba.

“Banga laifin ki ba Dija tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa zai doka Yana zaune lami lafiya da matar sa ta rufin asiri yaje ya kwaso kwai tara tsinana gashi nan ai ga irin ta nan an tatuke shi har babun sa ni ba shiyasa na shafawa kaina lafiya akan Sani ba ? yaushe rabon ma da ki ganni gidan ku? Ciwo ne zan mishi ADDU AR Ubangiji ya bashi lafiya hanne kuma gashi ga ta nan in ma mayyace in ta lashe mishi kurwa ya mace ba shikenan ba?

Dija ta dawo gida tana harhada kayan ta don da gaske take ta gama zama da alh Sani. haka kuma tayi mishi attack din karbar takardar sakin auren ta

Yayi murmushi yana duban ta yana fadin

“Dija na sahale miki igiyar auren ki daya rai da Rayuwa duka na Allah ne mai yuwuwa kece mai Riga na mutuwa cuta bata zama mutuwa sai ta cimma lokaci ko mu jima ko mu dade dole zamu bar duniya Amma tunda kina da zabi nima kuma ba zan tauye ku ba wata Kil nine kawai nake yarda da kaddara nake kallon komai daga Allah ne Kuma zai wuce ko mu wuce mu bar shi hannatu kema in kina da bukatar matsawa zan sauwake miki.

“Ni kam na yarda da ALLAH Ni da kai goben mu tana hannun Ubangiji yadda duk yayi mana fatan alheri ne biye.

Da haka Dija ta wuce gida amma bata bayyana wa iyayen ta gaskiyar abinda ya faru ba sai da fatima tazo gidan ta fadawa su haj yayin da mahaifiyar Dija ta rika kuka tana fadin Dija tayi butulci kuma sai Allah ya nuna mata ishara

Haka iyayen Dija sukayi ta zuwa duba Alh Sani suna bashi hakuri akan abinda Dija tayi mishi yace babu komai cuta ba ta zama mutuwa sai ta cimma lokaci ba mutuwa Dija take gudu ba sai don ta ga ya talauce shine ta gudu in da don ciwo ne matukar akwai daula zata jure amma gudun talauci tayi a yanzu.

Ciwon Alh Sani ya zamo kamar iska yanzu yanzu ciwo zai murde shi yanzu kuma ka ganshi lafiya lau . Al amarin da ya ganar da shi akwai sihiri a cikin ciwon nashi ya Kuma nemi masana hakan suka shiga bashi taimako aka kuma gano har wanda sukayi abin wanda har ran mutum sun dauka yayin gabatar da aikin su amma malaman suka ce dole ayi musu kaikai koma kan mashekiya amma Alh Sani yace kar ayi musu komai a bar su da zatin Ubangiji kuma Banda an riga an fadi sunan su  shi kam bai so aka sanar da shi su ba kuma ko a hakan ya barsu da wanda yayi shi yayi su duniya dai duk Yadda aka dade a cikin ta barin ta za ayi.

Yana shan magunguna Yana kuma samun sauki sosai

Kwanakin da basu haura talatin da fitar Dija daga gidan shi ba aka sanar dashi Bata da lafiya tana dab da auren wani mai akwai wanda ya tab’a son ta a lokacin tana budurwa  wanda ta guda saboda a lokacin bashi da kudi sai Sani ne take so don kudin sa amma tana jin wancan  yayi kudin dare daya ta  matsa da sai sun rabu da Alh  sani da tana ganin ba zai tashi ciwon shi ba  shiyasa take shirin auren kudi  tana cike da burin  daura auren su amma kan kace me? Sai ga ciwo ya riske ta   ganga ganga ya kayar da Dija

Aka ce ciwo idan abokin tafiya ne to baya jin komai sai tafiya don Haka kwanan Dija uku tace ga garin ku nan.

Mutuwar da ta girgiza Alh Sani tare da Ya’yan Dija Fatima da Salim da muhd. hatta Al mustafa yaji babu dadi musamman da yaga Fatima wacce suke cewa Yaya tana kuka kashirban

Haka aka share makokin Dija  wacce Ashe tsakanin ta da mijin nata tafiyar ba mai nisa bace

Samun saukin Alh Sani sai ya zamo an gane ya warware mugun kullin da akay mishi don haka aka sake mishi sabon zubi wanna karon Kam da Yake an cimma sa I  wadan can malamai magada annabawa basu yi nasara ba domin an kauce hanya sosai a wannan karon da son lallai sai an kawar da alh Sani Allah kuma Ra ufurrahim mai bawa kowa sa a idan ya nema ya basu sa a akan Alh Sani Wanda wata Kil hakan shine sanadin shiga Aljannar sa muna Masa fatan hakan ALLAHU ya Sha A.

Sannu kan hankali dukkan yan kaddarorin da ya mallaka ya siyar su Kare wurin magani da abinci kuma har yau din Babu wani Dan uwa guda daya da ya tab’a dukan kirji y kawo mishi abinda zai ciyar da iyalan sa sai dai suzo a tsaitsaye su ganshi su wuce shi bai roka ba su kuma basuyiwa zumunci kara ba

Shaguna hudu ne ya siyawa Al Mustafa da kudin da mahaifiyar sa ta turo mishi sai gidan su Wanda har yanzu yana nan a kulle bai siyar ba sai kuma fili guda daya shima dai duk mallakin Al Mustafa dan kyana Wanda ya zama gadon mahaifiyar sa da na mahaifin sa . Abinda ya tsayawa Alh Sani a Rai shine har gobe yan uwan sa Basu dauki Al Mustafa a matsayin dan uwan su ba . Babu mai neman sa bare yaji Yaya Yake? bare kuma ace suyi mishi kara ko alkunya da yadi ko falle daya a matsayin sa na dan uwan su .

Sai ya zama Sani yana cikin tashin hankali ba don komai ba don yaji Yana son ya samu wanda zai tsayawa Al Mustafa bayan shi don shi kam ciwo na nuna mishi lokaci na kusanto shi to amma waye zai iya daukar nauyin Al Mustafa da takalifin sa a  matsayin sa na maraya? kaf Yan uwan nasa  bai ga gwani ba gara salisu da nura amma ya san in ya bayar da amanar Al Mustafa ga dan Haj gaji to ya ballo fitina tsakanin sa da mahaifiyar sa  dole Rabi u da haj zai dankawa amanar dukiyar Al Mustafa in sun Rike Ruwan su in kuma sunci shima ruwan su shi dai Allah ya Sani yayi bakin iyawar sa ba kuma zai bawa kawu garbati ba don ya San gidan jiya za a koma

Kwana biyu ya tattare komai ya tara matar sa hanne da makocin sa malam shitu ya kuma kira mahaifiyar sa  haj kaltume da kawu garbati tare da dan uwan sa Alh Rabi u har da su nuran sai da ya tara ya kuma Sanar dasu dalilin kiran da yayi musu na bawa Rabi u amanar dukiyar Al Mustafa ya kuma yi musu bayanin kudi da Rabi ta turo mishi tace ya siyawa Al Mustafa kaddara shine ya siya mishi shaguna da fili ga kuma gidan su na jajere ya danka komai hannun Alh Rabi u yan uwa suka zama shaida wannan shine nauyin da alh Sani Yake kansa ya kuma sauke shi sai na mutanen da yake bi bashi wanda yace kar a tayar musu da hankali ko bayan ranshi idan sun kawo a karba ayiwa marayun Ya’yan sa hidima idan kuma basu bayar da a kyale su amma shi kam babu mai bin sa bashi ya siyar da kaddarar sa ya biya bashi duk wanda yace Yana bin sa bashi to yayi mishi sharri ne kawai kuma ko anzo ance ana bin sa to a bawa wanda yace yana bin .

<< Azurfa Da Zinari 80Azurfa Da Zinari 82 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×