Skip to content
Part 82 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Jikin kowa yayi sanyi amma banda haj kaltume wacce take ganin komai ya same shi shi ya jawo, yayin da Hanne kuwa kuka take don ta gama karaya da kalaman nasa masu kama da wasiyyar tafiya.

Kwanaki biyu da yin hakan ranar juma a alh Sani ya tashi babu wani ciwo a tare da shi ashe sauki na tafiya ne . Har masallacin juma a yaje ya dawo amma yana shiga Daki yaji zuciyar sa ta tsaya cik ya kwanta Akan shimfida yana ambatar kalamar shahada abinda ya fito da hanne daga daki tana xuwa yana dafe da gurbin zuciyar sa ta kama shi tana bashi Ruwa yasha tamkar wanda bacci ya dauka shikenan tafiya ta tafi Allah ta ala kayi mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma don mutuncin manzon Allah.

Kan kace me? gida ya dunke da dan mutum ya Kuma amsa sunan a gidan makoki yayin da Haj kaltume ce tazo ta kankane komai ana karbar gaisuwa ita kuma tana zuba iko da bude hanci Abu kad’an zata kyari hanne tana mata masifa da tijara kamar ba mutuwa akayi Mata ba .

Haj gaji da Haj hauwa da suka zo zaman gaisuwar ba a kwashe ta dadi ba don haj gaji dai har da Arashi ta saki wai girman kuka uwa binne Ya’ya saura kad’an ayi tsufan kwando.

Ai kuwa sai da aka shiga tsakanin Haj kaltume da Haj gaji fada kamar wasu yara .

Haka akayi kwanaki uku aka share makoki amma Haj kaltume tace a raba gadon Ya’yan Sani don ita zata karbe su in yaso mai da daya ta kara gaba a sallame ta.

A lokacin da Al Mustafa Dan kyana ya hattama Rubuta Al kur Ani mai girma ne akayi mishi gagarumar walima  a garin Gombe. walimar da ta Tara manyan shehunan malamai a ciki kuwa har da malamin Al Mustafa wato malam Haruna na garin bauci shima ya zo walimar ta Al Mustafa inda gwamnatin garin Gombe ma ta halacci bikin walimar ta kuma ga yaro Al Mustafa Dan kyana Mai shekara goma Sha biyu da haihuwa shine  Ubangiji yayiwa wannan nasibin dole Al amarin Mustafa ya zama na mamaki

Walima ta kayatar inda Al Mustafa ya samu tagomsshin alheri mai yawa don gwamnatin garin Gombe ta dauki nauyin karatun sa a ko wace k’asa Yake so yayin da ta tallafa mishi da kudi masu nauyi ta Kuma Bashi kyautar kujerar hajji uku kyauta wanda aka ce dashi da mahaifiyar sa da mahaifin sa  Al smarin da yasa ka Al Mustafa kuka don tunawa da yayi da a yanzu kam Babu iyayen sa a fadin duniya sai dai wasu su Amsa mishi wannan Sunan don haka sai ya Bawa malaman shi kujera biyun wato malam Haruna da malam Musa wanda ya tabbatar da sun mutunta shi sun maye mishi gurbin da ya Rasa  Bashi da su wato na Uwa da na Uba don haka ya bawa malam Haruna da malam Musa kujerun iyayen sa da fatan Aikin Nasu ya zama hadaya ga iyayen sa

Kyaututtuka Al Mustafa ya samu a wanna walima manyan mutane da manyan masu kudi sukayi mishi da ya bawa bajintar sa

Malam Haruna ya taho da Al Mustafa bauci tare da tarin kyaututtuka da kudaden sa . Bai manta da Rahane matar malam ba itama ya bata kyauta haka kuma yake fatan yaje ya samu hanne da Yan Uwan sa su yaya Fatima da salim da muhd wanda suke Ranshi da kewa da bege

Tare suka zo da malam Haruna garin bauci inda ya sauka gidan hanne wacce tayi auren ta mai sunan malam ma ya girma

Hanne ta karbe su tana Fadin

“Al kaine nake gani ?

Ta rungume shi tana fidda kwallar tausayi . Anan ya kwashe labarin komai ya sanar da ita na kaishi almajirci da Alh Rabi u yayi  da kuma tagomsshin alherin da ya samu a tsakanin bauci da Gombe na samun nasarar hardace Al kur Ani mai girma da Rubuta shi har ya samu kudaden sa sa kuma tallafin karatu a kowace k’asa Yake so.

Hawaye ya wanke fuskar hanne tana fadin

“ALLAHU AKBAR kabeeran Al Mustafa Allah ya jikan lahirar iyayen ka yau da suna Raye da sunyi farin ciki da kai Amma a yanzu ma Ubangiji ya sanya su  farin ciki a makwancin su nayi maka murna Al Mustafa hakikatan mai tunani zai gane kai din ajiyar Allah ne yau Ina Haj kaltume Ina Alh Rabi u? Ina yan uwan ka suzo suga ikon Allah ya tabbatar

Tayiwa malam Haruna Godiya da ADDU A tana Fadin

“Ni kam Al Mustafa da zaka yarda da nace ka Rike karatu ka kuma tafi neman ilimi na addini da na islama Allan ya daukaka ka ya yiwa Rayuwar ka albarka yau Ina ma Alh Sani yana Raye? Ina ma ace Dija tayi tsayin kwana taga abinda da takewa ciwon Rai da hassada? Kai mai tunani ma baya zura jiki da duk wani lamari matukar dai ba fatan alheri zaiyi ba dama dan hakin da ka raina shine mai tsone maka Ido. .

Al Mustafa yaji dadin ADDU AR da ani hanne tayi mishi yayi mata alheri mai yawa ya nufi gidan kakanin su Yaya Fatima inda ya same su makaranta ma ta gagara a biya saboda Babu kudin ga Rayuwar tayi tsanani . shine ya cire KUDI ya biya musu na tsayin shekara ya Kuma bawa kakanin su kudi don hidimar yau da gobe.

Ya ya Fatima da Salim suna zagaye da shi suna ta murna yana basu labarin inda alh Rabi u ya kaishi da abubuwan da suka biyo baya wanda suka zama alheri har ma Yana niyar tafiya karatu India ko malaysia ko Saudi Arabia

Har gidan kawu garbati dai Al Mustafa yaje ya kai mishi hasafi inda ya samu kawu garbati ya Kara tsufa sai fitinar shi da tayi gaba Amma da Yake kawowa Al Mustafa yayi sai ya sami ADDU AR kirki har ana yaba mishi uwa Yana Fadin

“ALLAHU AKBAR Al Mustafa ne? Ai uwar ka mutuniyar kirki ce Allah yasa Tana aljanna haka ma uban ka bare kuma marikin ka Alh Sani shima mutumin kirki amma kaga tsinanniya nan wannan kaltumen haka wannan Rabi un shima bai nuna ya zubar da no-non uwar sa ba Amma ai naji ance ya gudu ko ya dawo? Al Mustafa yace bai dawo ba.

Haka Al Mustafa ya zaga yan uwa da dangi hatta da su haj gaji da haj hauwa sai da ya zaga ya gaishe su yayi musu alheri mai yawa ya Kuma Roki su saka shi ADDU AR su don zai tafi karatu. Haka Yan uwan sa su tukuro Wanda ya zama tantin dan iska yaki karatu sai shaye shaye da latsa yan mata har ma in an ga garara garara a sane a sace Wani lokacin ma har dare ake bibiya don kwatar hakkin bayin Allah

Da wannan Al Mustafa ya koma bauci bayan yayi sallama da mutanen Plato abinda kuma yake saka shi kaunar mutumin duk da ya fito daga yankin bauci da Gombe shine saboda karimcin da akayi mishi a garuruwan shiyasa ko mutum zai gani in dai Dan bauci ne ko na garin Gombe to sai yayi mishi alheri kamar yadda nima ta haka ne muka hadu da Al Mustafa Dan kyana kasancewar na fito daga bauci har muka shaku ya zama uban gida na . cewaar daddy Alh iro da Yake Basu labarin.

Abu kamar wasa Al Mustafa ya zabi k’asar da Yake son yaje yayi karatun sa wato  Saudi Arabia babu tsaitsayawa kuwa gwamnati ta shirya mishi tafiya tare da scholarship mai nauyi zuwa k’asar Saudi Arabia

Al Mustafa yayi sallama da malaman sa wanda suka zamo mishi iyaye kuma almajirci ya zamar mishi sanadin alheri.

A Saudi Arabia Al Mustafa bai sha wahala ba saboda yana da Al kur Ani a kansa kuma yana da bokon ma duk da makarantar da ya sauka a Duka fanni uku ya samu Arabic da boko sai kuma fannin larabci don haka bai sha wuya ba a komai saboda ya San wani Abu sai dai dori.

Kan kace me? Al Mustafa yaro Dan kyana ya zama balarabe. Hutu da ilimi sun nuna shi ga Shiga irin ta larabawa tuni fatar shi ta saje da larabawa bakin sa ma larabci ya zauna hasken ilimi kuma ya Ratsa shi

Sai da ya shekara tara a Saudi Arabia kafin ya kammala karatuttukan sa duka ya kuma fito da takardun shaida masu daraja ya iso garin bauci zuwa lokacin kuma shekara uku kenan da Rasuwar malamin sa malam Haruna sai fa Mai dakin sa rahane ya samu da Ya’yan malam Haruna din Wanda sune suke rike da tsangayar makarantar

Yayi kuka ba kad’an ba Amma yayi mishi ADDU AR ALLAH ta ala yasa kwanciya hutawa. Bai tsaya a garin bauci ba ya nufi nasu garin wato Jon inda ya sauka wurin su salim da ya zama surayi kamar sa yaya Fatima kuma tuni tayi aure har da yaran ta biyu

A dakin Salim suke inda Salim yake aikin bakanike yana gyaran mashin da mota shi kuma Al mustafa kasuwa yake so don haka baiji girman kai ba duk da tarin ilimin sa da Kyawawan takardun sa wanda yan Nigeria ke burin aikin gwamnati amma Al mustafa bai ji Yana son Aikin ba duk da Babu irin Aikin da takardun sa ba zasu sama mishi ba Amma a haka bawan Allah nan yake daukar kayan talla irin su omo sabulu macklin da sauran kayan shago irin na tireda Akan sa yake zaga gari Yana tallatawa da yake Allah shine Allah tunda ya fara tallar nan Allah ta ala ya zuba mishi nasibi Mai yawa

Kan kace me ? kayan da Al Mustafa yake dauka akan sa suka fara fin karfin sa dole wani daga cikin wanda yake bashi sarin kayan ya bashi aron wani dan kyaus a cikin kasuwar koli Al Mustafa ya zuba kayan sa ya fara kasuwa.

Kasuwar Al Mustafa kasuwa ce irin ta mai ilimi wacce take cike da tsafta da kiyaye Riiba da Haram kuma gaskiya itace abinda al Mustafa yafi sani akan mafi yawan yan kasuwar min yanzu sunfi son hauma hauma da son a karewa talauci shiyasa ba a tara yaki halal yaki haram  amma a gun al Mustafa babu wannan gaskiya da gaskiya ne shiyasa Allah ya sakawa Abun albarka baya neman yawan Riba sai dai yawan albarka. Sau tari akwai abinda yake siyarwa ya fadi idan ya lura da mai siyen gajiyayye ne yakan ce sannu Bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba in Allah yaso sai ya kai bawa inda kafa bata isa zuwa ba.

Sannu sannu gaba gaba sai ga kyaus ya kasa daukar kayan Al Mustafa dole sai shago . tuni kuwa aka  sami shagon inda Al mustafa ya jawo salim da muhd a cikin dukiyar sa ana ta kasuwa mai albarka da Nagarta .

Tafi tayi sai ga wasu bangarori an bude  na shaguna har mai sunan malam dan wurin Nani hanne shima Al Mustafa ya jawo shi cikin harkar arziki inda kuma Yan Uwan Al mustafa irin su tukuro shaid’an d wasun su Wanda ba alheri ne ma ya shiga tsakanin su ba sun soma yiwa Al Mustafa layi layi da son karbar wani abu kuma baya dubawa yake basu duk abinda suke so yayin da su Haj gaji da Haj hauwa duk karshen wata ne Yake musu Aiken kayan masarufi . haka duk wata Yana aikewa da Kaya zuwa ga iyalan marigayi malam Haruna a bauci da kuma ga malam Musa a Gombe.

A wannan lokacin ne da Yake da shakara Sha bakwai malam musa ya bashi yarsa Amina auren da akayi cike da albarka da kuma fata da buri

Gadon Al Mustafa kaf Bai samu komai ba don Alh Rabi u da Haj kaltume ne sukayi kwance kansu kai hatta da gadon su Salim Alh Rabi u da haj kaltume sun handame amma Allah da ikon sa sai Al Mustafa ya kama haya suka zauna shi da Amina Yar malamin sa malam Musa

Tafi tafi arziki na kara yaduwa Al Mustafa Kuma yana Raba taimako a ko ina inda kuma a wannan lokacin ne tsufa ya makantar da kawu garbati wanda Ido ya Rufe baya ganin komai sai duhu .

 Al Mustafa ne tsaye akan kawu garbati wurin magani da abunda za aci a haular ta kawu garbati duk an gama kalmashe hakkin bayin Allah yau da inda karshen ya zamo 

Duk zaryar asibiti da akyi ta tayi bai dawo wa da garbati idon sa ba dama kuma idon in ya mutu kwalli baya tashin sa haka ma kaddara in ta sauka bata da mahani. dole kawu garbati ya tsaya a haka kullum Yana sanye da katon google din gilashin ido Wanda ya mamaye fiye da Rabin fuskar sa amma Kuma sai kace a lokacin ne aka zuba mishi masifa da tijara kar ma tsautsayi ya kaika ce mishi makaho wayyo Allah yanzu zakaji zagi da neman balaki gareka har ma zai kintaci inda maganar taka take fitowa ya kai duka da sandar jagoran sa . Sai ya zamo makantar kawu garbati Bata saka shi gane Allah daya ne ba sai Karin masifa da ya samu ga ciwon tsufa ga makanta amma bakin sa Bai mutu daga zagi da la anta ba maimakon a samu yana istigifari da salatin ANNABI smma Ina bai saba da hakan ba kasancewar dama yadda aka faro kuruciyar Haka za ayi tsufan yaron kirki to zai zamo tsohon kirki . yaron banza kuma dama tsohon banza ne Babu ko Wai.

s

Alh Rabi u da yake can lagos yayi mafaka ana shiga kasuwa ayi yan buga buga a amu na Rufin asiri. tunda yazo lagos bai kuma tunawa da jos ba musamman da ya San ya baro matan sa biyu da ciki tuni Kuma ya san sun sauka amma babu halin komawa gida bare kuma Ya’yan Sani da suka taru shi da mahaifiyar sa Haj kaltume suka cinyewa hakkin gadon su ya kuma tura su gidan kakanin su babu wani Bayani ai da kunya a Raka bak’o ya gudu

Babu abunda yake fata a kullum irin Allah yasa askar din Saudi su damko mahaifiyar tasa Haj kaltume su watso ta Nigeria tunda har ta iya cin amanar sa . ko da yake shi da ita sunci Amanar marayun allah ba Ya’yan Sani ba ba Dan maraya Al Mustafa ba.

Haka yayi ta Rayuwar a garin lagos amma lamarin nashi babu tsiya Babu arziki sai ma tarin tsiyar don har zuwa wannan lokacin bai Aje dubu goma ba da ya samu a abinci suke karewa don ma yayi hikimar zuwa gada ya kwana amma da kudin inda zai kwana ma ba zai iya Samu ba.

A Lagos din ma saukalen manyan motoci yake ko fidda kaya a contener a bakin ruwa shine aikin na Rabi u Yana samun kudin abinci . kai in aka ce maka shi ne Alh Rabi u din nan zaka karyata.to dama kuma duk Rayuwar da Mai ita baiji tsoron Allah ba to hakikatan zai ji tsoron juyin duniya. Mai nazari ne yake alheri ko don ya tsira da shi to Alh Rabi u dai basuyi zaton Haka ba shi da uwar tasa Haj kaltume sukayi ta dubga Rashin kirki da zamba cikin aminci karshe kuma suka zo suka ci dukiyar maraya wacce mai cinta yake wulakanta a duniya a lahira kuma ya Amayar da ita da harshen wuta Allan ta ala kayi mana tsari da cin hakkin da ba namu ba kayi mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma ka jikan lahirar iyayen mu ks yafe mana kayi mana saukin cikin Rayuwa don mutuncin manzon Allah ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam.

<< Azurfa Da Zinari 81Azurfa Da Zinari 83 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×