Allah Wanda Shi ne yake da sunan Arrahamanu wanda Ke saukar da Rahama ga bayin sa a lokacin da yaso hakan. Shine dai ya nufi ya daukaka arzikin Al Mustafa Dan kyana Wanda Al Alamarin cikin kaulasan din ya tabbata wato KUN FA YAKUN
Shagunan Al Mustafa sun samu kafuwa fiye da guda ashirin ko Ina Kuma ka leka zaka same shi dankam da Dan mutum ana ta faman kaiwa da komowa harkar arziki kawai ake inda Allan Kuma ya yarda
Tuni Al Mustafa ya kafa harsashin ginin gida ya Kuma Tamfatsa gida abinda Yake gida ya Kuma tare da matar sa Amina wacce a wannan shekarar ne zasu tafi Aikin farali shi da ita da Kuma baban ta malam musa sai babban Dan malam Haruna wato Bashiru Wanda shine Halifan malam Haruna din a yanzu shi ke Rike da tsangayar makarantar
Shekara uku da auren Alh Mustafa Dan kyana da Haj Amina Amma har zuwa yanzu din shiru Bata yi ko Batan wata ba . A Al adar waccan zamanin ma mace na iya share shekara Goma Bata haihu ba Babu Mai damuwa ba kamar yanzu ba da an shekara ba a haihu ba sai yawon asibito ci neman binkito dalili
Tuni duk wani da Yake da Ruwa da tsaki da Al Mustafa Dan kyana tun daga na cikin gidan su zuwa Yan layin su Al Mustafa ya Basu abunyi a cikin taskar Ubangiji da ya bude mishi .
Shi da kan shi Al Mustafa ya lalubo Dan Uwan sa tukuro ya jawo shi ya saka shi a cikin dukiya don yaga Rayuwar tana neman mutuwa a lalace
Ya soma yiwa tukuro nasiha Wanda a yanzu ne shaid’ancin na shi Yake ka don Babu inda ba a San Sunan shaid’an ba tun Daga Nan kwaryar garin Nasu na Jon zuwa bauci da Gombe Babu inda sunan shaid’an Bai zaga ba don yanzu sunan shi na yanka ma ya bace tukuro ma ya Zama sunan yan gida ne Amma world wide name din sa shaid’an ne sak.
“Haba Yaya tukur yanzu irin wannan Rayuwar ta gamsar da Kai a Haka? Don Allah duk wani Abu a hakura da Shi dubi shekarun ka har yanzu babu aure ga irin wannan Rayuwar da kake na tabbatar da Kai kanka ba Dadin ta kakeji ba. Kazo kayi Sana a ka Zama mutumin kirki Kai da kanka ne zakaji ka aminta da kanka don Allah kazo kayi kasuwa Yaya tukur yadda mahaifin mu ya Tara mu a matsayin zuriar sa muma muna son mu Tara namu zuriar don mu yawaita da yawaitar salatin ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam.
Wannan nasiha ta Al Mustafa ga Yayan sa tukuro yayi mishi ita ne don zatin Ubangiji ba don yaci zarafin sa ba Amma sai tukuro ya ke ganin kanin nashi ya zo mishi da Raini don Haka ya mike Yana motse fusks Yana Fadin
“Kai karamin yaro Ni kake zaunarwa ka Karanta min wannan wulakancin don kutumar Uwar ka ? Ni kake son cewa Dan iska don kaga Ina zuwa nace ka bani wani Abu?
Ya soma nade Hannun Riga Yana Shirin yiwa Al Mustafa mahungurba.
“Yi hakuri Yaya tukur ba Haka nake nufi ba wallahi yanzu Dubi irin wannan zagin da Yake fita bakin ka Babu girma don Allah ka Bari Ni yanzu in baka son nayi maka matashiya to na Bari Amma kazo muyi kasuwa ka Sami abinyi .
Tukuro ya soma mayar da numfashi kamar Wanda yayi tsere saboda masifa Yana zare idanu. Da Haka Al Mustafa ya Samu ya shawo Kan sa yazo ake kasuwar tare da shi Amma abinda Al Mustafa Bai Sani ba shine tukuro mugun dangi ne Wanda Baya nufar kowa da alheri Kuma Babu abunda yake sakawa sai ta Yaya zai kassara Al Mustafa? Bai shigo cikin dukiyar Al Mustafa da nufin kasuwa ba ya shigo ne da mugun nufin sa da kuma neman mafitar sa ta son Sai ya mayar da daukakar Al Mustafa Akan sa Amma Allah arraheemu sai ya ke duba zukata da abinda suke kullawa.
Kan kace me kuwa? Sai ga tukuro a kasuwa ka in da na in Kuma Al Mustafa Yana biyan su abinda yafi na Wahalar su Kuma Baya shamaki ga kowa shi abinda Yake so ma yagani in har kana tare da shi to so Yake yaga Rayuwar ka sauya ka na cikin samu ba Wai yaga kamar Yana tauye ka don Haka Babu keta a tafiyar Al Mustafa.
Tafiya tayi nisa Al Amura suna ta hauhawa Al Mustafa ya soma harkar cinikayya da manyan Yan kasuwar da suke Africa Yana siyen Kaya Hannun su Yana Kuma samun Riba inda ya Kuma shiga wata harkar ta man fetur Yana samu kuma.
Jin shaharar Al Mustafa Dan kyana wacce ta ke Amsa Amon sauti a duniya don sunan sa ya fara zaga duniya don Haka sai ga Alh Rabi u ya garzayo ya Baro Lagos wurjanjan ya nufo Jos Jin Bayyanar Dan Uwan nashi Wanda duk duniya take Amsa Amon sautin sa
Ya shigo Jos da fata da buri inda ya fara sauka a sabon gidan sa Wanda ya Gina filin gadon Al Mustafa ya saka Amaryar sa inda ya iske Uwar gidan sa habiba ce kadai a gidan yayin da Amarya sholy ta kama gaban ta Bayan ta Haife cikin ta inda kuma Al Mustafa ya Samu labarin Halin da matar Yaya Rabi u take ciki Sai Yake tallafa Mata da abinci da karatun Ya’yan su don har Wanda sholy ta Haifa ma Nan ta maido shi wurin habiba ta Kuma karba ta hada nata Ya’yan su biyar suka tashi su shida sai ga Rahamar Allah Daga Al Mustafa. lallai Bawa aikata alheri baka San inda zaka fada ba in kayi sharri karshen ta ka fada hannun wanda kayiwa sharri me kake zato idan ka Tara’s da Mai bakar Aniya?
Habiba ta zuba mishi ido tana kallon shi da son taga irin ci gaban da ya Samu Amma sai taga want irin matsiyacin tsufa da ya tasar Masa kallo guda Daya talk zakayi mishi ka Gane Halin Babu da ake ciki to in Haka ne meye Ranar abunda yayi? Me gudun ya amfanar dashi baya ga daukar alhaki?
Ya ajiye Yar jakar sa ta Ghana mazgo sai Yan kwarorin doyar da basu Kai takwas ba Wai tafiyar shekara kusan Tara Amma a dawo maka da kwayoyin doya takwas.
“Habiba Ina sholy ne ? Ina yara ? Wannan shine cikin da Kika Haifa? Ya fada Yana jawo yaron da ya Zama bakuwar fuska a idon sa.
Ta dube shi tana Fadin
“Gashi Nan Dan da baka damu da ya ya yazo ba bare Halin da uwar sa take ciki. Ga wannan ma Umar ne shine Dan suolyn taka wacce kake wa nacin tambaya kamar ita kadai ka Bari a Baya.
Ya hade yaran Yan Samari Yana kallon su cike da kauna da soyayya Yana Fadin
“Kuna Raina habiba Dole na na bar garin Nan tunda Haj ta saka Ni a Goran da Babu fafi yanzu ma na gaji ne da bulayi shine na juyo gida don naji Ana ta fadar Al Mustafa da irin shaharar da yayi shine na dawo ko Aikin gadi ya bani .
“Uhum ai gudun kaddara Rabe guxurin tasshe ta ne dubi dai yadda Uwar yaron Nan Al Mustafa ta Rayu a gidan ku ? Dubi irin Yadda shi Kansa yaron ya Rayu a haular ku? Yau ga yadda Allah yayi ikon sa akan sa shine Wanda kukayiwa handama da babakere Kai da Haj hatta fulotin gidan Nan gadon yaron Nan ne kayi gida ka kawo Amarya duk da kudin su Dana Ya’yan marigayi Alh Sani Rabe yau Ina Mai farin cikin sanar da Kai Mustafa shine cin mu da Shan mu har da suturar Rufe tsiraicin mu . Ko a mafarki kaga Haka na San zaka karyata don yadda kuka Mayar da yaron Nan kayan Banza da wofi Baku zaci Allah zai martaba shi irin Haka ba . Sau tari dama abinda kuka Raina shine madaukaki a wurin Ubangiji yau ku kuka zalunce shi amma zaluncin da kukayi mishi Bai Rage shi da komai ba ku Kuma maimakon kuyi gaba sai tsiya ta Doka muku sallama Dolen ku Kuma kuka bude Mata kofa har kuka marabce ta gashi Nan kazo da son ko Aikin gadi Al Mustafa ya baka Kai Mai tsunkaye ne ma Yake bin duniya a sannu Anya idon ku da kunya ma?
Rabi u yayi shiru Yana Jin lallai abunda habiba ta fada gaskiya ne Babu ko coge a cikin maganar ta.
“Hakika munyi kuskure habiba amma Ni ba kowa ne ya cuce Ni ba sai haj ta tattare kudade na da kaddarori na ta siyar da komai ta tafi Saudi Arabia Allah ya Sani nafi shekara ina Rokawa Haj janhurun askar din Saudi su damko ta su watso Nigeria don ta saka Ni a Shiga uku ba kad’an ba ke har azumin nafila dai nayi duk Akan Allah yasa a damko Haj. Amma yanzu tunda Allah ya sakawa Al Mustafa zuciyar I’mani na San ba zai duba dukkan abinda mukayi mishi a Baya ba tunda da zai duba da Bai taimaka muku irin taimakon da mu bamuyi musu ba shi da Uwar sa hakika Allah ya aje Mana wa azi da izina.
“Uhum ai da baka wahalar da kanka Rokawa Haj janhurun askar ba kana Nan zaka ga yadda Al Amarin zai kasance ba dai yadda kuke so kukayi ba? To ku saurari zuwan yadda bakwa so Kai ai yanzu Kaine Mai Bawa wani shawarar yadda za ayi tunda Akan idon ka komai ya faru to haj ma in dai tayi Aiki irin naka na cuta da danne hakkin marayu to zaka ga yadda duk zaku Zama ba sai ka Roka Mata janhurun masifa ba allah ai ba azzalumi bane duk abinda Bawa ya gani daga gareshi ne alkheri ne ke zuwa daga Ubangiji amma akasin hakan Daga kayi ne.
Alh Rabi u ya taka har katafaren kantinan Al Mustafa ya Kuma ga Yadda ake ta Shiga da fita sai yayi tsaye Yana kallon kudurar Allah.
Ya jima a tsaye Yana zancen zuci kafin ya hango tukuro ya fito cikin wata dakakkiyar shaddar gizna yasha wanka don Haka da mamaki ya Isa ga tukuro Yana Fadin.
“Tukuro ne ko kuwa Kama ce?
Tukuro ya juyo Yana Fadin.
“Ba Kama bace shine sai dai yanzu Sunan ya tashi daga tukuro ya koma Alh tukuro shaid’an waye Kai da kake min wannan shigar?.
Tukuro ya tambaya Yana kallon Alh Rabi u don kamannin sa sun juye ba zaka fahimci waye ba sai ka nutsu sosai zaka Gane shi.
Alh Rabi u yayi murmushi Yana Fadin
“Baka Gane Ni bane tukuro? Rabi u ne fa tukuro kaje hajji ne?.
Da sauri tukuro ya juyo Yana Fadin
“Wai Yaya Rabi u Kaine Haka? Ka Samu barnar mota ne ? Yasin ban Gane ka ba yi hakuri don Allah sannu da zuwa shigo ka Sha Ruwan Sanyi ka huta don da ganin ka agajiye kayi Kama da gajiyayye.
Tukuro ya fada Yana Dariyar iya shege don har yanzu Yana Nan da Rashin kirkin sa Yana Nan Bai canja ba.
Alh Rabi u ya bishi suka Shiga office din tukuro Wanda ya kawo mishi lemu da Ruwa Mai Sanyi kafin ya sauke mishi Naman kaji ya kuwa dafe Yana aunawa don ya Jima Bai hadu da Naman kaji ba shiyasa yanzu yayi musu cin keta ya Hauda da lemu da Ruwa ya Gama ya samu nutsuwa yayin da sanyin AC ya Soma Ratsa shi yayi daidaiya Yana Shirin bacci Amma tukuro ya ce mishi.
“A a Rabi u Kar kayi min bacci a Nan ka ishe Ni da tusa gara ka karasa gida ka kwanta ka huta .
Rabi u ya mike Zaune Yana Fadin
“Ai wurin Al Mustafa Nazo Nima a sama min Aiki ko na gadi ne Yaya za ayi na ganshi? Naga ku Kam tukuro kun Samu Shiga kaga yadda kake walkiya? Allah ya maida mu a danshin ku.
Tukuro ya mike Yana Fadin
“Taso muje na Kai ka office din sa.
Alh Rabi u ya mike yabi Bayan tukuro suka nufi office din Al Mustafa inda suka Samu Al Mustafa cike da Baki Amma Yana ganin Yaya Rabi u ya ce su shigo suka Shiga ya Bawa bakin sa hakuri ya kebe da su a falon hutun shi inda su tukuro da Yaya Rabi u suka Zauna Rabi u Yana gaishe shi kamar zai Goya shi don zumudi.
“Haba dai Yaya Rabi u ka gaishe Ni? Allah ya sauwake wallahi ban Kai wannan matsayin ba.
“Wallahi ka Kai Al Mustafa Nazo habiba take fada min irin hidimar da kayi da su Al Mustafa Allah ya jikan iyayen ka da Rahama Ni wallahi kunyar ka nake ji da wane idon da Zan dube ka? Na cinye gadon ka nayi nufin fidda ka daga jiki na na kaika almajirci Ashe silar arzikin ne ka tafi ka tako .
“Abunda ya wuce ya wuce Ni bana Rike da kowa da komai nayi Mamaki ma da anty habiba ta fada min ka gudu ne ka bar su.
“Dole na gudu Al Mustafa baka San makircin da Haj ta kulla min ba ne? Ai Haj ta siyar min da komai ta Haye Saudi ta barni da saukar talauci Dole na gudu na bar gari.
“Kar ka damu Yaya Rabi u abinda ya wuce ya wuce har Abada.
“To Alhamdulillahi dama wannan zuwan naka ne gaskiya Nima Aiki Nazo ka bani ko na gadi ne don garin yaci wuta wallahi.
“Kafi karfin gadi yaya Rabi u kazo sai kake kamawa Yaya tukuro ka Zama Mai taimaka mishi ai ka wuce da Aikin gadi.
Ai kuwa Yaya Rabi u har da Hawaye Yana ta Godiya ya Duka gaban Al Mustafa har Sai da ya ce Baya son Haka Yana Duka mishi a matsayin sa na Yayan sa dole ya bashi hakuri shi kuma Al Mustafa ya komawa bakin da suke jiran sa.
Yana fita tukuro ya dubi Rabi u Yana Fadin
“Ni fa ban so ya hada ni da kai ba Yaya Rabi u don zaka saka min Ido ne a harka ta smma Bari na ga irin takun naka na San irin taka burkin da zanyi maka wallahi don ba zan dauki nonsense ba.
Tun daga wannan Rana Yaya Rabi u ya soma fitowa Aiki duk da shi ne wanda ya san boko fiye da tukuro wanda bai tsaya yayi karatun ba bare ya san sikin sosai don haka sai Rabi u ya so fin tukuro abinda Kuma tukuro Bai ji zai lamunta ba .
Kamar wata biyu da dawowar Rabi u daga lagos zuwa jos ya kama aiki da Al Mustafa inda albashin sa Mai daraja tuni ya soma farfadowa kudi suna samuwa don ma tukuro ya kankane komai Amma Dole ayi mishi ta yan duniya.
Watanni hudu daidai sai ga haj kaltume askar sun Danko ta sun watso Nigeria duk da ba wata lafiya ce ta ishe ta ba don Haka babba tashin Hankalin Haj kaltume Wanda ya haddasa mata tashin hawwn jinin ta domin kuwa duk kudaden da ta Tara a Saudi anyi mata kamen takaici domin kuwa ta baro komai a can Saudi haka aka watso ta Nigeria daga ita sai zanin jikin ta sai Kuma akayi Rashin sa a jirgin da ya kwaso su ya watsar da kayan wofi a legos dole sai ta biyo mota ta iso Jos sai da bara ta hada kudin motar zuwa gida don Haka kai tsaye ta nufi gidan Rabi u don nan kawai take ta ke da garantin samun wurin da zata Adana kafadun ta.
Wurjanjan Haj kaltume ta iso garin Jos ba don komai ba kuma sai don tsananin bak’in cikin da take ciki na baro tarin dukiyar da akayi ta Fadi tashin Tarawa ta yaki halal yaki Haram Amma abin haushi dubi yadda askar din k’asar Saudi suka auno ta zuwa Nigeria ba tare da yi mata uzurin kankamto dukiyar ta ba Haka suka aunota zuwa k’asar su abinda kuma ya Tayar Mata da hankali kenan take hango gwala gwalan da ta mallaka da Kuma tarin Riyalai na Saudi Arabia Wanda su cima da yaduwa abokan zaman ta a dakin hadakar su zasu ci zahamar su koma su ci ganimar su a Banza a wofi wannan Al Amari shine ya tashi hawan jinin alhajiya kaltume wacce Bata tab’a sanin tana da cutar hawan jini ba sai da ya tasar Mata a Lagos din da jirgin askar din k’asar Saudi ya kawo su Nan ya watsar ya juya abin sa don ita k’asar Saudi duk wani bakar fata a wurin ta Dan Nigeria ne Kuma idan ta kamo su Lagos take watsar da su kowa ya Gane gidan gyatumin sa . Masu sa ar gaske ne ake watsarwa a Kano koma Ina ce k’asar ku sai ka lalubo ta don Haka a Lagos aka sauke su Haj kaltume wacce tsabar bak’in cikin baro dukiyar ta yasa ciwo Wanda ta samu isa asibiti inda aka tabbatar Mata da ciwon ta hawan jini ne don Haka Yan Riyalan da suke Lalitar ta su ta Mika akayi Mata magana har aka biyo ta bashi Amma da ta sanar ko daga Ina take da Kuma irin asarar da ta baro sai suka tausaya Mata Basu nemi cikon kudin su ba sukayi Mata fatan samun lafiya
Dole haj kaltume ta tuke a Bakin gada neman sabil din da ta Baro a Saudi don samun kudin motar zuwa Jos inda take ta imagin din abinda Kuma zata siyar don ta koma Saudi da gaggawa ta kwaso dukiyar ta tun kafin su cima da yaduwa suyi Mata dirar mikiya Akan gwala gwalan ta da tarin Riyalan ta da suke damfare a cikin Lalitar bujenta.
Sai kuma ta Gano Babu wani Abu da yayi saura tunda duk hauma haumar da tayi ta dukiyar Al Mustafa da na jikokin ta Ya’yan Sani. Kai har da na Raben ta dai Bata Bari ba duk ta tattare ta killace ta kammale ta kalmashe ta haye Saudi sai gata a yau ta Zama Allah sarki a bakin gadar Lagos tana Mika hannu da sunan bara Kai zalunci ma bashi da Riba wallahi .
Kwananta biyar a gadar Lagos a Nan take kwana a Nan take Rayuwa inda taga keta da manuba da Kuma tsantsar iskanci a matattarar mutane da yaruka
Ta samu da kyar ta hada kudin motar Jos yayin da sauron da yake a gada ya sakar Mata zazzabi ga sickness din blood pressure ciwo dai Yana Shirin tasar Mata shiyasa ta iso garin Jos wurjanjan tamkar Mai tafiyar dibar wuta.
Habiba ce ta dago kanta Jin an shigo Babu ko sallama sai taga Haj kaltume tana shigowa.
“Oyoyo haj sannu da zuwa
Ta fada tana kamo Haj kaltume wacce take son kwantawa ta huta.