“To naji sayyada Amma gida ma na Rufe shi in ta dawo ta buga a bude Mata kofar.
“Zalunci kenan idan Kika ce sai ta dawo Zaki bude mata kofa in askar din sun biyo ta har su Kama ta ma kenan.
Da sauri yaduwa ta mike ta fita ta bude kofar gidan har tana dan lekawa ko zata hango Haj kaltume Amma har tsayin minti talatin babu ita Babu Dalilin ta har yaduwa ta gaji da tsayuwa ta koma ciki tana Fadin
“Allah dai yasa tsautsayin Nan bai Rutsa da matar Nan ba .
Cima tana jin ta tana ta jajen Haj kaltume Amma Bata ko bi ta kanta ba har Dare ya Raba yaduwa na Fadin wallahi ba lafiya ba matar Nan ta hadu da tsautsayin askar.
Wasa Wasa har kwanaki biyar Babu Haj kaltume inda inda aminyar Haj kaltume ta iso gidan nasu don dauke kayan Haj kaltume don habi ta fadawa aminiyar Haj kaltume wato turai cewa da idon ta taga yadda askar suka cika Hannu da kaltume ai ko sai ga turai s guje ta Isa gidan tana fadawa su yaduwa da cima askar sunyi Gaba da Haj kaltume don Haka zata dauki kayan ta ta tura Mata can Nigeria.
Babu komai a Ran turai sai manuba da makirci da son tayi sama da Fadi da dukiyar Haj kaltume don Haka take ta bare bare da son kwashe komsi Amma abinda Bata sani ba shine tuni cima ta Soma bin dare Tana lalube kayan Haj kaltume inda tayi arba da tarin Riyalan ta a Lalita ta soma tatuke ta Amma da Yake Allah gwanin adalci ne sai ya Tayar da yaduwa wacce ga Alama akwai kamshin I’mani a tare da ita ta kuma ga makircin da cima take kitsawa na lalube kayan baiwar Allah Haj kaltume.
“Haba cima don Allah ya sunan abinda kikayi yanzu ? Anya kuwa gumin wani ya tab’a zama na wani Haka siddan? Me yasa matar Nan ta tsaya Miki a Rai? Wallahi in Kika ce abinda tayi Miki Zaki Mata ku Duka zakuyi mutuwar kasko in ta biki da sharri ke bita da alheri sai kiga Aniyar kowa ta bishi Amma yanzu kina kallon yadda take ta Fadi tashin Tara dukiyar ta Amma Kika biyo dare kina sanewa ? Yanzu in Kika ci kudin Nan don Allah ke da kanki kice me Kika ci? To bani su Nan wallahi cima ba Zaki ci komai na kaltume ba in kikayi Haka ai kin tabbatar Mata da yadda take daukar mu Amma ace musulmi Bai iya karewa Dan uwan ka musulmi Amana ba in anci taka Amanar biyan bashi ne Kuma yanzu idan aka kira ki da sunan barauniya sai kice an kala miki Sharri?
Ta Mika hannu ta finciko tarin kudaden Riyalan da cima ta tattare tana Shirin sakawa a Lalita ta dauko Lalitar da kudaden suke ciki ta bude adakarta ta zuba su inda kuma ta hangi ma adanin gwala gwalan Haj kaltume Suma ta dauko su ta saka a adakarta ta kulle da Dan makulli ta saka a tata Lalitar ta kwanta tana Mamakin cima da Bata iya banbance halal da Haram. Yayin da cima Kuma kunya ta Hana ta motsin kirki har ta Rika ganin yaduwa a matsayin surukarta.
Kwanaki biyar sai ga turai ta garzayo ta na gwama numfashi tana Fadin Kayan aminyar ta ta biyo har take fadawa su yaduwa an Kama haj kaltume ne tuni ta Isa Nigeria Wai har sunyi waya ma tace akwai dunkiyar ta a Dakin da Kuma koman ta a Bawa turan ta tura Mata. .
Cima dai sai a Nan taji kunya tamkar ta nutse don tana ganin kamar yaduwa zata fadawa turan abinda ya faru Amma sai tayi tsit inda yaduwa ke ta Fadin
“Wallahi har Bayan ta nabi don cima ta dawo wurjanjan askar sun fafaro ta har tana zubar da kayan Miya Ashe baiwar Allah tsautsayi ya hada da ita kamar mun Sani muka tattare Mata kayan ta gu Daya gasu Nan Bari na bude Miki komai sai ki Rubuta abinda muka baki don abin Amana wuya gareshi.
Akayi komai a Rubuce aka Bawa turai kayan Haj kaltume tarin gwala gwalai da kudaden ta ta wuce Ashe akwai tsamin munafunci a Ran matar Nan turai wacce ta Shiga cuku cukun yadda zata Samu Visa ta samfe garin su sokoto da ganimar Haj kaltume da take ganin ta Samu.
Sai dai an samu jinkiri na Rashin Samun visar saboda mahukuntan k’asar sun mayar da hankali ne Akan Kame duk ajnaban k’asar su mayar da su k’asar su saboda mugun Aikin da suke tafkaww a k’asar
Cikar mako biyu da faruwar kamun Haj kaltume sai gata Allah Mai girma da buwaya ya nufe ta da dawowa inda take cike da doki da murna da Kuma fargabar Kar ya zamo Bata samu su cima da yaduwa ba don ta tabbatar da in suka Samu ganimar kayan ta to ba zasu yarda su Zauna a garin Saudi ba.
Fiye da irin gudun da zuciya keyi ne Haj kaltume ta diro Saudi tana faman lissafin dokin Rano ta hau motar da ta sadar da ita zuwa gidan Nasu da wani irin sauri da doki inda har tana gwabza tuntube ta banka kofar da son taji ta bude aikuwa ta fada ta Shiga da sauri tana Rafka sallama yaduwa ta fito tana fadin.
“Kai Haj kece tafe? Kai masha Allah sannu da zuwa Haj ba dai cuku cukun dawowa Kika Samu yi ba?
Haj kaltume ta banka kofar tana Fadin.
“Yaduwa ba Dole nayi cuku cukun dawowa ba na bar tarin dukiya ta Ina kayana?
Ta fada tana duban yaduwa da son taji yaya akayi don Bata ga Alamar komai nata ba.
“Kayan ki suna Nan Haj kwantar da Hankalin ki Zauna ki huta tukuna.
“Kayya bar hutun yaduwa kin San yadda akayi na iso Saudi kuwa? Taimaka mini ki dauko min Kaya na na duba Naga komai a muhallan sa.
“Kar ki Damu haj ba kin turo aminiyar ki turai ta karba Miki ba? To na min Bata komai naki kinga takardar da muka Rubuta komai a Rubuce.
“Wace turan yaduwa,? Ni banyi magana da turai ba ita tazo tace Ni na Aiko ta? Wallahi Haram Bari ki ga na tashi Zama Bai ganni ba yadda na San turai da hauma hauma Akan kudi yaushe Zan tsaya? Daga Aron kudi fa matar nan ta cuce Ni tayi min Rinto .
Da sauri Haj kaltume ta mike ta figi mayafin ta inda yaduwa tace Mata.
“Jira ni kaltume mu tafi tare ai Ni na bata kaya tunda har ta iya wanna Karyar komai ma zai iya faruwa to muje ta bani komai da na Bata.
Haka suka bazama gidan su turai inda Haj kaltume sai cewa take.
“Allah ka agaza min dukiyar marayu nake nufin Mayarwa ka ga zuciya ta kaga abunda na gani na wa azi ga yaron Nan Al Mustafa Wanda nayiwa sharri nayiwa uwar sa sharri yau shine mafificin Ya’yan mu kuma Bai duba komai ba yayi min abinda zato Bai zata ba Allah ka Sani Naga wa azi da izina tunda turai ta shigo cikin Al Amarin Nan tana da wata nufaka ne ta son ta cuce Ni Allah ka Kar ka bari dukiyar marayu ta tafi a zalunci da cin Amana.
Sai Kuma ta fara kuka yayin da yaduwa take tallon ta da sauraren abinda take fada Wanda ya nuna Mata hauma haumar da itama tayi kafin ta iso Saudi .
Da Haka suka iso gidan da turai take Amma me? Suna zuwa tsaiba take fada musu ai kuwa yau yau din Nan turai tayi bankwana da Saudi ta tafi garin su sokoto .
Wani irin kuka da Haj kaltume ta fasa tana Dora hannun ta biyu akan ta tana fadin
“Yau Ni na Shiga uku na lalace turai ta cuce Ni ta yaudare ni ina Zan saka kaina Ni kaltume? Sai kuma ta juyo a guje tana duban tsaiba tana Fadin.
“Tsaiba sammako tayi ko kuwa can ta kwana?
Tsaiba da abin ya Tayar Mata da hankali musamman ganin kukan Haj kaltume da Shiga ukun da take Kirawo kanta .
“Don Allah ki daina kukan Nan kaltume.
“Ta Yaya Zan daina kuka tsaiba? Ko kuwa kin San inda Zan Samu turai a sokoto? .
“Wallahi ban sani ba Amma wani Abu ya faru?.
Yaduwa ta dubi tsaiba tana fadin
“Yaushe turai ta bar gida?
Tsaiba tace asubanci tayi don tun shekaran jiya take ta fafutukar neman visa Bata samu ba duk da tana ta kashe kudi da son samun don ko a dazun din Kiran ta akayi akace tazo an samu idan zata iya biya tace zata iya biya shine fa mukayi bankwana to Ni sai yanzu ma nake jin ko dai matar Nan ta bar baya da k’ura ne shiyasa take neman visa Wurjanjan?.
Kuka sosai Haj kaltume take inda yaduwa tace Mata .
“Taso Haj mu Shiga neman turai don Nima a yanzu naji a Raina ta shirya wani Abu ne a Ranta tunda Kika ce min bakuyi waya ba na Gane abinda naso hanawa ne a dakin mu shine ya faru ga turai to Amma kamar Yadda Kika ce hakkin marayu in Sha Allah munyi tawassuli Allah da ya haramtawa Kansa zalunci ya Kuma Sanya shi Haram a tsakanin bayin sa in Sha Allah turai ba zata ci hakkin marayu ta kwana lafiya ba taso mu gani ko akwai wata hikima da zanyi .
Abin tausayi abin Dariya Haj kaltume ta mike tana dauke kwallar idon ta tabi Bayan yaduwa suka fice suka Dauki tasi suka nufi filin jirgi na king abdulazeez da nufin buncike inda zasu Samu turai.
Haka suka filin jirgin sukayi ta bulayin neman turai Amma ko Mai Kama da ita Basu gani ba yayin da Haj kaltume ke ta Kuka tana Fadin.
“Dame wanna yayi Kama ? Kaci Amana aci Amanar ka? Ja ya Fado ja ya dauka kenan kudade masu yawa aka batar kafin na Sami zuwa Nan Amma Allah ya tsinewa turai albarka Ashe munafukin ka yana gindin ka nayi kaicon sanin ki a Rayuwa ta turai.
Haka haj kaltume ke ta sambatu har suka gaji da zagaye filin jirgin inda yaduwa taji an kwala Mata Kira ta juyo sai taga shafa ce wata Yar garin su wacce suka zo Saudi a tare don Haka suka cafke suna gaisawa inda shafa taga Haj kaltume sai matsar Ido take tana fidda kwalla ta ce
“Yaduwa tafiya gida zakuyi ne ?
Yaduwa ta fada mata turai suke nema ta yaudare matar Nan ne shine suka zo Nan ko Allah zai sa su ganta.
“To maza ku Garzaya jidda don yau Kam akwai jirgin da zai tashi a yau karfe hudu in Sha Allah a can wata Kil ku Dace don yanzu Haka Daga can nake na Kuma ga Mata da yawa wata Kil tana cikin su.
Da sauri Haj kaltume ta mike ta figi Hannun yaduwa suka Haye mota sai jidda inda suka hango matafiyan a filin jirgin inda Haj kaltume da yaduwa suka Soma Raba Ido da son su hango turai yayin da turai dake Zaune Rufe da fuska ta Yane idon ta tayi maza zata Kara Rufe idon ta ta yadda ba za a Gane fuskar ta ba sai nikabin ya zame sai kawai sukayi ido hudu da Haj kaltume sai tayi maza ta mike zata sulale da sauri Haj kaltume ta auna aguje tana Fadin.
“Yaduwa taho gata a can zata gudu wallahi . Yadda tayi maganar da karfi yasa hankali ya juyo kansu yaduwa Kuma ta Rufawa Haj kaltume baya wacce take gudu da son ta Danko turai Kai ba kace tsohuwa ce Mai shekarun ta ba Amma ta dage sai falla gudu take yaduwa ma ta Rufe mata baya. A guje da wani irin sauri Haj kaltume ta nufi turai da take kokarin bacewa cikin dandazon Al umma don ta gama gane shirin ta ya baje manubar da take kokarin aikatawa Allah ya watsa shirin nata.
“Taho da gudu yaduwa ga bakar munafukar ga can tawo a guje ki tara min ita don Allah kar ta sulale mini da kayan marayun Allah !
Cewar Haj kaltume wacce ta daka wani uban tsalle ta cacumo Bak’ar Rigar turai wacce take mayar da nikabin fuskar ta wai ita a dole Sai tayi musu basaja.
Yaduwa ta iso da gudu suka saka turai a kwana wacce tayi wuri wuri tana zare nikabin fuskar ta tana fadin.
“Don Allah bani hanya kaltume zawayi nake kina tare min hanya wake naci ciki na ya lalace sai kwara zawayi nake .
“Ai sai dai kiyi shi a nan zawayin turai amma wallahi ba zan bari ki matsa ko Nan da can ba in kuwa Nayi hakan Ni na tabbata gallafiri don barin ki daidai Yake da kasa Rayuwa ta a bakin teku shine kike shirin tsallake k’asa ki tafi gida Amma ko ki fada min zaki zo ga zance ga magana bakiyi ba to muje ki tattare min Kaya na da Kika karba Hannun yaduwa ga takarda Nan a Rubuce karyar da kikayi min Kuma na yafe miki Amma dukiya ta ko hakkin Ashana sai kin aje shi tunda haka Aminci ya zama munafunci.
“Sharri zaki kala min kaltume? Yanzu da na karbar miki dukiyar taki har kin dora min janhurun masifa Akan zan cuce ki? Saboda fa dukiyar ki nayi nufin zuwa Nigeria in kai miki shine har kin lakaya min SATA?.
“Karya kike ba don kaya na zaki gida ba kinyi dai nufin guduwa sokoto ne saboda samun ganima in da don ni zaki je Nigeria da tuni kin kira ni kin shaida min zuwan ki kamar yadda kikayiwa yaduwa karyar cewar munyi magana da ke ki karba min dukiya ta to in ma dai hakan ne gani na zo na hutar da ke dogon sharhin nan da Kuma zuwan da baki shirya ba.
“Ai fa dama alheri bai karbi bakin mutum ba kaltume dama duk Wanda kayiwa alheri sharri ne sakamakon ka meye banyi miki ba zuwan Saudi? amma yau ni kike kalawa SATA saboda kawai Baki tsaya kinji kadin zance ba.
“Yo me kikayi min turai da kike min gori? Ina ce ma ko a cikin abinda kike nufin kinyi min din cuta ta kikayi? Kome kika min da kudi na kikayi min ke jeki ma kinyi din ai kin farke har da Riba yanzu dai muje ki bani kaya na kawai koma me zaki ce zai bi ta bayan kunnuwa.
Turai taja kwata tana Fadin
“Dama kuma Dan Adam butulu mai zama kaza a ci a goge Baki kaltume? Muje na Baki kayan ki da na San hakan ai da ban yarda na karba ba tunda kina can kina yayata ni zan gudu da kayan ki dama yaushe alheri kewa bakin mutum kyau?.
“Duka dai naji turai abinda yafi wannan ma ki fada na dauka kaya na dai Basu zama ganimar da za a kai garin sokoto a dakawa warwaso ba bani da bakin iyaye shiyasa Babu Ni Babu dogon tagumi.
Dole turai tayi ta kwance jakunkunan da ta Lodi kayan tafiya tana fidda kayan Haj kaltume da ta kammale da nufin cin zahamar su Amma fa zuciyar ta cike fal da tarin kunci da bak’in cikin Rashin warwaso akan kayan aminiyar Tata don Haka ne ma tayi nufin manuba wa kaltumen.