Yaduwa na fadin, “Ai Haj ni ya kamata na karbi komai da na Bata tunda ga komai a Rubuce ai ni zan Harlanta milki Kayan ki don har a Raina banji wani Abu guda Daya tak ya burge ni a cikin Kayan ki ba shiyasa ma da turai ta bayyana da Bayanin ta banja ba na bata komai.
“Ke dai Bari yaduwa shiyasa akace zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ina can Ina ta faman fadin kar kuyi min awon gaba da kaya Ashe sab’anin zatona Abun Yana inda bankai shi ba ku kuma da nake zaton Ashe kune masu kare min kadin.
Yaduwa tayi murmushi a Ranta tana fadin
Cima ce lambar farko da na Bari tayi yadda taso da turai ma ba zata san komai ba Ashe haka mutanen suka koma da karfin tsiya suke son sai hakkin wani ya zama Nasu.
Turai ta soma futo da gwala gwalai da kudaden Riyalan Haj kaltume tana mikawa yaduwa wacce take duban takardar da suka Rubuta komai yaduwa na karantawa turai tana fiddawa har komai ya kammala inda kuma turai ta ce kudaden da ta kashe sai Haj kaltume ta biya ta tunda ita tayiwa.
“Ke yaduwa wuce muje tunda dai na tabbatar da komai nawa ya dawo in taso ta kaini sijin( hukuma kenan da yaren larabci)
Haka suka wuce suka bar turai da cizon yatsa tana ganin ta leko ta koma.
Tunda Haj kaltume ta samu kudaden ta da gwala gwalan ta suka dawo sai tayi ta tunanin wa kuma zata yarda ta bawa ya aika mata gida Nigeria? ta kasa yarda da wani mutum ta wakilta shi tunda dai haka Al umma suka koma dole ka ji tsoron bawa mutum Amana don Haka taga gara kawai ta shirya tafiya ta koma gida har zaman tukarancin ta hakura da Shi tunda ga Rahamar da Ubangiji ya saukar musu ta Al Mustafa wanda ya zama uban marar Uba Mai uban ma shine gatan sa abunda Basu tab’a zato ba Dan mijin su na karshe ya zama gagara badau don haka ta shirya komawa gida Nigeria amma kudin da zata kashe ma tana tsoron biyan su don ta gama lissafa kudaden Ya’yan Sani da na Al Mustafa har dai da na Rabi u da zata bashi kudin sa sauran kudin kuma tayi jarin sana a. Sai ya kasance dukkan dukiyar Haj kaltume tana kugunta tana fatan gari ya baci askar su matsa lamba ayi kame wanda za a kawo ka gida baby ko sisin ka . Kamar kuwa askar din sun Sha Rad’a sai gashi sati biyu an kuma kamen kan mai uwa da wabi inda haj kaltume ta fice da son tayi taho mu gama da askar din duk yadda ajnabai ke gudun ceton Rayuwa amma haj kaltume su take durfafa ai kuwa sukayi awon Gaba da ita.sai jirgi suka auno ta Nigeria gamu nan ga mu nan sai kanon dabo inda kuma tsautsayin ya auku inda Haj kaltume ta manta da tarin dukiyar da ta sha goyo da kyar a garin Saudi sai gashi ta subuce a garin Kano kuma duk bata gane asarar da ta tafka ba sai da ta iso jos ta lalubi lalita da nufin ta biya direban da ya kwaso Mata gumamar da zata fara kasuwa da ita taji wayam babu Lalita babu labarin ta ai sai ta kwartsa ihu tana rusa kuka ga direba ya ja ya dake kudin sa Yake so.
Kuka Haj kaltume take har da sharbe tana ta Fadin
“Ni kam shiga uku ta same ni duk yakin da nayi da turai na samu na kwato dukiyar marayu Ashe a wofi zan zubar da su a jirgi sai yanzu na tuna da na kwance lalitar nan na biya kudin hubxa Ashe tsautsayi ya kaini ni kaltume da na barwa turai ma ta taho min da su in yaso sai naje can garin nasu na karbo yanzu yan jirgi na can suna murna ni kam da na san haka da ban tsaya jiran kamen askar ba yau mai gari ya wayar mini? Sai ta fashe da kuka inda Rabi u yake kallon ta yana Jin abinda take fada bayan ta gama zayyane mishi yadda komai ya faru tun daga Saudi Arabia wurin turai har kawo zuwan su Kano .
Al Mustafa ne yaxo ya Sami labarin abinda y faru ya bawa Haj kaltume hakuri yace zai buga waya a can filin jirgin ya sanar akwai mutumin sa a can in sha Allah komai kenan za ayi da wannan haj kaltume ta hakura amma kullum sai tace alhaki ne ke bibiyar ta.
Tukuro kam da Rabi u sun cika sun tumbatsa don kullum suna cike da wawashe dukiyar Al Mustafa wanda ya soma gane halin da ake ciki musamman akan Black market din da ake wa dunkiyar sa wacce Allah ke buds mishi ya gani Babu zato bare tsammani Amma Bai tab’a nuna musu ba Kuma Allah Bai gajiyar da shi ba ko yayi k’asa kullum dukiyar sa gaba take saboda tarin alherin da yakeyiwa duban dubatar Al ummar musulmi don yanzu haka ma ya soma sakawa a Nemo mishi yaran da Rashin gata Yake hanawa ci gaba da karatu don taimaka musu .
A kuma cikin wannan lokacin ne allah ya nufe Ni da zuwa garin Jos inda aka tura Ni service na Kuma sauka a wata makaranta ta gaba da primary inda nan kuma Allah ya hada ni da alh Al Mustafa Dan kyana Wanda yazo makarantar da nake service da nufin ganawa da malaman makarantar don su sanar da shi adadin yawan yaran da Rashin gata ya Hana ci gaba da karatu.
Tun a Ranar da muka fara haduwa yake tambaya ta daga bauci na fito? nace mishi Eh shine duk ya bani wannan labarin da nake Baku saboda Allah ya hada jini na da shi sosai munyi maganganu sosai Akan yadda za a taimaka wa Al ummar musulmi musamman marasa galihu ni kuma nayi mishi Bayani da irin hange na na kuma Bashi shawarar wani foundation ya kamata ya bude inda za a ga mabukata.bai yada shawara ta ba ya kuma dauka sai gashi dubun dubatar Al ummar suna zuwa kawo kukan su ya kuma share musu hawaye
Al Mustafa Dan kyana yayi min alheri Mai yawa a zama na jos yayin bautar k’asa har na cika shekara daya bawan Allah nan shi Yake daukar nauyi na hatta da gidan da na zauna shi ya bani don ban zauna a campus ba haka dukkan Wata dawainiya tawa da abinci na a gidan sa nake karba matar sa kuma Haj Amina mace mai mutunci Bata tab’a gajiyawa da ni ba shiyasa ma da na gama bautar k’asa nayi mishi sallama yace min idan na koma gida zaiyi min magana idan na Samu Aiki Yana min fatan alheri Idan kuma ban samu ba to Yana roko na na dawo Jos tunda gashi da kamfunna ko Nan nayi Aiki da shi nake Kuma Bashi shawara tunda a zaman da mukayi na Bashi shawarwari ya kuma ga amfanin su don Allah naje nayi shawara. Mukayi sallama bawan Allah Nan ya cika Ni da kayan arziki na dawo bauci da tunanin sa .
Allah da ikon sa sai da nayi shekara cur Babu batun aiki shine yaxo har bauci ya dauke ni muka koma Jos Inda ya kaini cikin dukiyar sa a matsayin mai kula da duk wani shige da fice zai wakana a dukkan kamfunnan nasa
Kalubalen da na fara fuskanta shine Yan uwan sa irin su tukuro da alh Rabi u wanda suke fadar ba zai yuwu nazo daga sama taka haye ba a cikin dukiyar Dan uwan su kuma nace zan taka musu burki ni a wa? Ban San Yaya dangin Al Mustafa suke ba Amma nasan basu da kirki sai da tafiya tayi tafiya kafin Al Mustafa ya zayyane mini wannan labarin da nake Baku tun daga shigar mahaifiyar sa gidan su har kawo inda na zo na tara’s ni kuma na Sha alwashin ba Zan tab’a Bari a cuce shi ta Bak’ar kasuwa ba tunda har yarda da Aminci yasa ya jawo ni cikin arzikin sa ni kuma zan nuna mishi ni din dan halal ne
Ana cikin wannan taskun ne matar sa Haj Amina ta soma Rashin lafiya inda aka kaita asibiti sai aka gano ciki ne Allah ya albarkace ta da samu a tsayin shekarun auren su kusan Tara .
Haj Amina tayi ta rashin lafiya har dai waje an fidda ita kafin ta samu sauki suka dawo gida sai dai maganar da ta bullo ba mai dadin ji ba ce don tukuro Kam ya cika babban shaid’an don ya gwada shaid’ancin sa kasancewar basu Shiri da Haj Amina wacce Rashin shirin su ya samo asali daga mugun halin da ya nuna Mata na son ya keta haddin ta ita Kuma taji Bata kaunar sa Amma Bata fadawa Al Mustafa ba don tana ganin kuskure ne ta sanar da shi Amma ganin tukuro Bai samu fuskar haj Amina ba sai ya zaga ya fadawa kanin sa cewa matar sa fa tana neman shi da lalacewa shi kuma yaki don haka yayi mata magana
Al Mustafa yayi mamaki Amma da yake ya san Halin yayan shi tukuro sai ya bashi hakuri ya kuma ce Amina ba zatayi haka ba amma ba a shawa mutumin duniya zai bincike ta
Haj Amina tayi shiru tana sauraren mijin nata da abunda yake tambayar ta na ko wani Abu ya faru tsakanin ta da Yaya tukuro?
Ta jima kafin ta sanar da shi abinda ya faru ta Kuma ce tayi shiru ne don kar abun ya zama na tashin hankali.
“Na San za ayi haka Amina kiyi hakuri da dangi na nasan yadda suke kallo na kema kin San wani Abu a cikin Rayuwa ta da ta mahaifiya ta na San shaid’ancin yaya tukuro abinda yafi Haka ma zaiyi shiyasa na bashi hakuri kema na Roke ki da girman Ubangiji ki Rufe maganar nan mu Barta a tsakanin mu ni dai Allah ya San yadda nake son su sune dai basa sona to ni Allah ya ishe ni na Rasa uwa ta da Uba na gashi kuma ina Rayuwa fata na Ubangiji ya azurta mu da Samun iyali su zama cikon farin ciki.
Haka aka Rufe babin maganar nan amma iuma Haj Amina ta Rufe tukuro gaisuwa ce kswai abinda ke hada su . Sai ga shigar saurin da iro nayi musu Wanda na samu aka rage kaso tamanin daga cikin dari na zambar da akewa Al Mustafa dan kyana inda kuma dukkan mugayen kudirin tukuro da Rabi u suka komo kaina da son a tarwatse ni do haka suka shiga shiri na musamman alkaina ni kuma dama bana Wasa da azkarin Safiya da maraice ga taimako muna samu don ba a zama haka bare kuma ni da na baro jihar mu nazo cikon farin wasu ahalin da Babu tsoron Allah a tare da su .
Fitar maganar cikin Haj Amina sai ga tukuro ya iso gidan Al Mustafa Wanda yake fadawa wai yana Aikin me da zai karbi cikin matar sa da Bata haihuwar shekara da shekaru sai yanzu Rana tsaka za a kawo mishi ciki ? bai san abinda kenan ba tsakanin matar sa da zindikin da ya kawo Yana mishi Aikin duba kamfunna? To sun hada Baki ne yayi mata ciki don suyi kashe mu Raba tunda matar ka ta gane Kaine baka haihuwar ai gashi yanzu da ta samu mai haihuwa har tayi ciki ko? ni da kaina na fada maka matar ka tana jawarci na Bata da buri sai na ta gaje dukiyar ka Amma da yake ks zama salamamme baka dauki wani mataki ba to in Kai ka yarda Ni ba zan yarda ba sai na matsi wannan shegen itsma sai tayi Mana bayanin yadda Kai da baka haihuwa kayi mata ciki in ma tana ganin baka san komai ba to ni na sani tunda ta nuna min halin ta.
Tukuro yayi ta kumfar baki yana tijara da hayaniya tamkar zai rufe Al Mustafa da duka inda Al mustafan yayi murmushi yana fadin.
“Haba Yaya tukur me ya kawo wannan maganar don Allah? shi fa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Kai ka tab’a kama iro da Amina ne? shaidar zina tana da Wahala sai an tara mutum hudu wanda suka gani Rara ainin da idon su kuma amintattu wanda duniya ta shaida mutanen kirki ne ba zasuyi karya ko k’age da son zuciya ba.idan a cikin mutum hudun Nan uku suka ce sun gani Daya yace bai gani turmi dd tabarya ba to duka shaida ukun ta watse . To mu bar maganar nan don Allah ni na san wacece Amina na kuma san shi kan shi Ibrahim din . Ban kasance na tsawon lokaci da shi ba Amma a cikin shekara biyu na fahimce shi Yaya tukur ba zaiyi abinda kake zargi ba in Kuma ka kama su da idon ka sanar mini?.
A fusace tukuro ya soma fadin
“Har sai na kama su da ido na ne zaka yarda bayan ni na san wacece matar ka? ka manta da kad’an ya Rage ta harde Ni da son lalata ni nine dai ban yarda na ci Amanar ka ba? ko kuwa don Ina Rufe asiri ban fada maka ba ne yasa kake zaton zan mata Sharri? To bari na fada maka abinda baka Sani ba. Iyayen ta ma da suka baka ita manufa gare su ta son mallakar dukiyar ka. Sai akayi rashin sa a Kai din juya ne baka haihuwa sai suka shiga Yaya za ayi a kawo maka cikin wani a matsayin naka? Da ni matar ka ta soma gwada sa ar ta saboda tana kallo na dan iska. Da bakin ta tace zata biya Ni adadin kudin da nake so idan na yarda nayi Mata ciki.Ni Kuma tsoron Allah da tuna Kai din Kane na ne ba zan yi ba nayi nifin Rufe asirin ta idan ta bar maganar Ashe ta zaga ita da wannan shegen shine kuma na kawo maka Bayani kana ce min ga zance ga magana? To babu shegen da zai karbi cikin ta in Kai an makanta ma ka tunani mu dangin ka ba zamu yarda ba wallahi da shi iron da ita matar taka sai sunyi Mana Bayani da yaren larabci wallahi .
Da Haka tukuro ya fice Yana kumfar Baki Al Mustafa yabi shi da kallon mamaki . Da ace tukuro ya kasance mutumin kirkin da duniya ta yarda da kirkin sa to da ba zai Dora zargi Akan bayin Allah ba. Haka kuma da ya kawar da Kai Koda wani ya kawo zancen. To Amma sanin waye da abunda yace amina tayi mishi Wanda kaf abinda ya faru Babu Wanda Al Mustafa Bai Sani ba don Amina ita ta Rufa mishi asiri Bata Sanar ba sai da tura ta Kai bango ya tambaye ta ta Kuma fada mishi Masha ar da tukuron yaso yi da ita tunda ai ya San Halin tukuron don kwanan Nan har wata yarinyar yayiwa ciki sai shi Al Mustafan ne ya dauki nauyin biyan iyayen yarinyar kudin ciyarwa har ta haihu a kawo yaron to ko magani iyayen yarinyar suka Bata suka zubar da cikin ko kuwa dai zubewa yayi daga Allah? ALLAHU a a lam sun dai ce ciki ya zube to me wannan Halin ne zai ce wata ta neme shi?
Sai dai me ? Kan kace kwabo tukuro ya Tara taron dangin su ya fesa musu Al amarin na cikin matar Al Mustafa Amina Wanda ya karawa miyar gishiri tare da hada fitinar Ibrahim ne Mai cikin Aminar.