Skip to content
Part 93 of 98 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Ke yanzu nake maganar ki Yar duniya Ashe kin Shiga Venus din Nan? Kai gaskiya kina wuta tawan har ina zuba miki fetur.

Yanayin da keens ta gani a fuskar Nadiya ne yasa ta Dan nutsu tana Fadin

“Yaya dai tawan ko akwai damuwane?.

“Keena kin san gayen Nan da ake cewa shaid’an?

Nadiya ta tambaye ta Babu sassauci.

Keena da har kudin shaid’an din ta karba da niyar xata Kai mishi Nadiya amma ta Rasa dukkan damar ta har ta kashe wayoyin ta don gujewa kiran shaid’an sai  gashi yanzu Nadiya na tambayar ta ta san shi.

“Ni kuwa na San shi Nadiya wani Abu ne?

Nadiya ta hadiye yawu da kyar tana Fadin

“A wane gari yake keena?

tayi maza tace mata Jos Yake.

“Zaki iya kaini inda yake Yanzu?

Da wata irin murna keens ke fadin

“Me kuwa zai Hana,? tashi ma muje yanzu na kai ki ko ya sakar miki dalolin ne don shi in dai Yana son mace babu abinda ba zai iya yi mata ba.

“Nice dai zan sakar mishi dalolin keens muje don Allah sauri nake .

Keena bata fahimci komai a maganar Nadiya ba ta mike tana daukar jakar ta tayi shiri ko luba bata kira ba suka fice mota ta kwashe su zuwa garin Jos.

Tukuro ya dubi kwalo yana fadin.

“Kai banji abinda kace ba fa? A Ina ka samo mahaukaciyar? kuma Yaya take?.

Kwalo ya zauna yana daukar Ruwan sanyi ya Sha ya aje yana fadin

“Billahilazi wata sabuwar mahaukaciya na Nemo maka mutumi na sabuwa ce gal a ledar ta yasin za ayi harka wurin nan don yadda nagan ta ban zaci ma ta San namiji ba full option wacce zata dace da tsarin ka kuma ga Alama haukan  nata bai jima da kama ta ba don ko Kazantar nan irin ta mahaukata Bata da ita sosai bana jin Kuma daga nan yankin ta fito don na tambaye wani wacece ita? yace suma basu san ta ba sun wayi gari dai sun ganta tana kwana a makarantar Bokon can ta kusan fita gari .

Da wani irin sauri tukuro ya figi hannun kwalo suka fice tukuro yana Fadin

“Ai har ka gama zana min ita a zuciya ta kwalo har naji Ina son ganin ta naga ta yaya ta zama mace a wurin ka. Kace za a kwashi abubuwa?

Ya bude mota suka shiga kwalo yana afdin

“Kai din ne ban sani ba? Ai in dai mace ta mallaki kirji da kuturi shaid’an to ta gama Kama ka ba kwanaki da ka dafewa wata matar aure ba saboda kawai tana da dirin da kake so? .

Shaid’an yayi Dariya Yana tashin motar ya fige ta da karfi tamkar zai tashi sama ta bakwai Yana Fadin.

“Kuma ka San kwalo sai da na shimfide matar Nan ? Ai shaid’anci na nuna Mata na Kuma sakar Mata kudadeAshe mijin nata Dan Napep ne tuni na fasa Mata Kai sai gata tana Bina har hotel muna zage zogale har Kira na take Wai yaushe zamu Hadu? Ni Kuma Bata San matukar na ci bredi na yaga Leda ba to za a Jima ban juyo ba sai Kuma wani sabon buredin Amma shegiyar nan ta isheni da Kiran waya tana tura min account lamba sai da ta kuma  yaga ta Kai Daga karshe fa sai da ta kashe auren ta fito tana ce min sun Rabu da dan Napep din Wai ba zai iya Rike ta ba Ni kuma nace in dai a kaina kikayi Haka kinyi gwari don ni Kam bana a yadda take kallo na tuni na saka lambar tata a me ake cewa inda ko ka Kira ba zaka Samu ba? Kwalo yace

“Black list?

Ya amsa da cewa

“Shi fa Ni fa ka San kwalo ban San komai a Boko ba don Babu abinda na tsana ma irin turanci don Sai Naga kamar ana son a munafunce Ni in aka juya harshe shiyasa ban waye da komai ba sai Exactly shima saboda ina Jin Yaya Rabe Yana yawan fadar ta.

Suna dab da Isa makarantar Bokon ta fita gari suka hango mahaukaciyar Saman bola tana ta tsince tsince a Saman bolar har tayi nasarar tono wani busasshen buredi ta Kuma dafe Tana dariya ta soma bantara Tana ci .

“Kwalo ? Ba dai itace waccan ba?

Tukuro ya fada Yana sauke idon shi Akan mahaukaciyar.

Da sauri kwalo ya dubi inda Yake Mishi nuni sai ya hango ta Zaune dafa an tana ta kamtsar busasshen buredin Nan da ya lalace har aka zubar Shara.

“Wallahi itace shaid’an ka ganta ko? Dube ta komai ya Kai .

Da sauri shaid’an ya dauko take a way din da Yake cikin motar shi Wanda yaci ya Rage abuncin ya taka burki ya bude motar ya fito Yana karewwa mahaukaciyar kallo inda Kuma ya ga abinda kwalo Yake fada mishi don Rigar jikin ta ta soma yagewa ya ga kirjin ta har Yana Shirin Kai hannu Amma ya Mika Mata Robar take a way din ta kuwa cabe tana cin abincin abinda zai tabbatar maka da yunwa take ji.

Tukuro ya koma mota ya dayko gorar Ruwan faro ya kawo Mata ta kuwa Karbe kamar da tsiya ta daga tana Sha ta Gama Sha ta kankame Robar tana kallon tukuro tana Dariya har tana daga mishi hannu.

Tukuro ya dawo mota inda kwalo Yake Yana Fadin

“Kwalo fito ka kamo min yarinyar Nan don wallahi yadda na ganta ba zan iya barin ta a Nan ba Dole na gabatar da Aikin malam tunda ka kawo min kayan Nan.

“A a mutumi na ba yanzu ba ai zaka nuna zalama ne kawai daga yau zuwa gobe da jibi zaka Rika zuwa Nan kana Bawa mahaukaciyar Nan abinci ta Haka zata Saba da Kai Amma yanzu zuwa daya ai zaka sa mutane su tuhume ka a can ma cikin makaranta take kwana ko Nan bakin bolar Nan zaka same ta muje anjima ma ka kawo Mata abinci yanzu ne zaka dauki hankalin ta har ta dafe maka Amma yanzu da gamo da kasawa?.

Haka kuwa akayi tukuro ya soma zaryar kaiwa mahaukaciyar Nan abinci ta Kuma dafe mishi yayin da Yake zuwa da mota Amma da kusa da inda take zai aje motar ya tafi a k’asa da Kuma ta hango shi zata auno aguje ta zo ya Bata ta juya tana sambatu.

A cikin kwanaki uku tukuro ya samu zuciyar mahaukaciyar Nan dama da yaro da mahaukaci da ungo ake Samo su don Haka tukuro ya samu mahaukaciyar Nan sai Kuma ya shiga Yaya za ayi a Samu a farke ta don tuni an Gama hada Mata yawu ko da Babu Aikin malam bare Kuma da burin Hakan.

Washe gari jikin Al Mustafa ya matsa ana ta Karin Ruwa da allurai Amma kuma jiki kam sai Godiyar Ubangiji. Dakin asibitin ya cika dankam da Yan uwan sa inda ya ce na taysr da shi ya zauna Yana duban Yan Uwan sa Wanda kusan dukkan su suna Nan sunzo duba shi. A Nan ya soma magana Yana Fadin a Kira mishi sauran Yan Uwan sa Wanda basa Nan don Haka aka shiga Kiran wayoyin su suna Hallara har da tukuro shima ya iso da su kawu garbati da Haj kaltume har da hanne da su Mai sunan malam da salim da muhd har da Yaya Fatima wace itama a yanzu take aure har da Ya’yan ta a cikin dukiyar Al Mustafa yayin da Al Mustafa yayiwa su salim gida shi da muhd sukayi aure hatta da Mai Sunan malam yayi aure Kuma duk Al Mustafa ne yayi musu gidaje tare da tallafar su yayin bikin

Al Mustafa ya dubi tarin ahalin nasa inda yace ayiwa ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam salati a Kuma bude taron da ADDU A akayi Hakan aka shafa

Ya soma magana Yana Fadin

“Kuyi hakuri na sa an Kira ku na katse muku uzuri to ku yafe Ni Sak’o gare Ni ko na ce sauke wani nauyi koma Kai tsaye nace wasiyya. Ina son na Sanar da ku na siyar da kamfunna na Duka saboda ina Jin kamar ana umurta ta da nayi hakan . to Allah shi kadai ya barwa Kansa Sani don haka nake Rokon ku don Allah don ANNABI duk Wanda nayiwa wani laifi a Sani ko a Rashin Sani da ya yafe mini Ni dai Babu Wanda yayi min in ma anyi mini na yafe Amma Nima don girman Allah ku yafe mini .

Suka soma Fadin Babu komai sun yafe mishi irin su hanne da kawu garbati da su Salim Amma irin su tukuro sai suka soma Jan tsaki Amma Basu tanka ba.

Al Mustafa ya dauko wata takarda Yana Fadin

“Wannan takardar itace ta shaidar na siyar da kamfunna ga Kuma kudin Nan na Gama Lissafa su dukkan ku Nan kowa da sunan sa da Kuma yawan abunda Zan bashi Amma akwai wasu mutane da suke da hakki kaina irin su Mai sunan malam da Kuma Salim da muhd sai Yaya Fatima da Yan Uwan marigayiya Amina da hanne gata sai kawu garbati da Ya’yan sa da sukayiwa dukiya hidima Suma ga hakkin su na na ware musu don suja jari. Ya Shiga Mika wa kowa cek din banki don ya Gama tsara komai hatta da su tukuro da Yaya Rabi u sai da ya zana musu cek na milyon biyar biyar Amma yaran da suke cikin dukiyar kowa ya samu miloyon Sha biyar biyar don yace suyi jari. Abinda kawai yayi saura shine shagunan shi da ake siyar da kayan tireda wanda suke guda goma Sha biyu su Kuma wannan yace ba na kowa bane ko Babu Rayuwar sa basa cikin gado sai dai kawai ana tallafawa marayun allah da kuma Gina mishi massalatai da Rijiyoyi da Kuma Kai tallafi asibitoci . Haka ma gidan shi yace ayi makaranta sauran kudin da suke account Kuma a siyi Al kur Anai a Raba sadaka a duk Ranar da Allah ya karbi Rayuwar sa .

Da yawan su kuka suke irin su Mai sunan malam da su yaya Fatima da salim da muhd har da hanne da girma ya soma kamata Amma Dan ta Mai sunan malam Yana dauke da takalifin ta Kuma Al Mustafa Bai man ta ta ba har Saudi dai ya kaita.

Da yawan su Kuma Yan uwan sa murna suke da suka Samu kyautar kudaden Nan Babu ma Wanda ya damu da ciwon na Al Mustafa Haka suka soma ficewa yayin da wasun su suka tssya suna mishi ADDU A tare da fatan alheri Mai yawa

Yaya Rabe Kam tuni ya saka kudin sa inda zasu yadu wato Sana a tukuro Kuma tsaki yayi Yana Fadin

“Tun Aiki Bai fara ba ? Ai da yaren larabci zakayi Bayani sauran abinda ya Rage din ma zaka neme shi ka Rasa ne wannan kuma kudin da ka bayar Zan canja su zuwa dala na biya kudin Aikin da za a karasa tsiya ta ka.

Ya fuce Yana Kiran kwalo Don yau Kam sai ya kwana da mahaukaciyar Nan.

A can ya dauki kwalon suka nufi bakin bolar da mahaukaciyar ke zaman Dakon tukuro sai kuwa gashi da abinci Wanda ya ki fitowa daga motar ya nuno Mata ta kuwa taso aguje tazo karba daga Nan fa kwalo ya hankado ta motar tukuro ya Tayar da gilas ya Rufe ruf don Haka Babu Wanda yaji ihun baiwar Allah Nan tukuro kuwa yayi Mata kaca kaca Babu tausayi Babu I’mani ya kuwa Karbe mutuncin ta baiwar Allah tun tana ihu da kwararato har Abun yafi karfin ta ta hakura tana shidewa.

A Nan tukuro ya zubar da ita a bakin bolar yaja mota suka wuce shi da kwalo Bayan ya cika umurnin malam na daukar Kazantar tarayyar su da mahaukaciyar ya nufi gida don yayi wanka.

Suna tafe a mota tukuro Yana fadawa kwalo irin artabun da yasha kafin ya cika buri yasha yagu da cizo Amma duk Bai Hana ya Nuna Mata Rashin I’mani ba .

A Ranar kuwa da dare tukuro ya nufi gidan malam da nufin Kai mishi kayan da Kazantar tarayyar su da mahaukaciyar sai dai ya Samu gidan malam a Rufe inda ya Kira wayar malam din yace mishi a yau ne wani babban mutum a kasar Niger yaxo ya dauke shi Amma zuwa safe zai dawo sai yazo .

Tukuro ya kwana Yana begen mahaukaciyar Nan don tunda Yake neme nemen matan shi Bai tab’a samun irin ta ba don Haka ya kwana Yana tuna ta da tunanin komawa gareta.

Kwanaki biyu da wannan wasiyya ta Al Mustafa tamkar Wanda Ubangiji ya haskawa Al amarin sa ko da Yake yace min Yana ji ne a jikin sa ya kusa mutuwa. Ashe kuwa Allah ne ya nuna mishi. Ranar Laraba ne yayi wasiyyar Amma juma a har ana Shirin sallamar sa don sauki ya samu sosai har muje juma a mun dawo likitan yana Fadin da akwai maganin da zai bashi ya aika a kawo Ashe duk da gawa Muke tare . Kwanciyar da Al Mustafa yayi wacce yace Yana Jin bacci Ashe itace sallamar bankwana garemu da duk Wanda Yake da Rabon ganin sa . Ashe farkawa sai a Alkiyama

Har yamma Bai farka ba inda likitan yace a Tayar da shi amma tashin da ba zai yuwu a nan duniya ba Allah kayi Mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma don mutuncin manzon Allah.

Tukuro Yana tare da malam Yana gabatar mishi da kayan Al Mustafa da Kuma Kazantar tarayyar su da mahaukaciyar har malam ya Gama abinda zaiyi ya Bawa tukuro kayan Yana Fadin

“Ka San duk yadda zakayi ya saka kayan Nan a tsakanin yau ko gobe . Wannan kuma ka bunne inda Yake wucewa na baka sati Daya idan baka ga koman shi ya Kare ba kazo na biya ka kudin ka.

“Nagode malam ai shegen Yana gadon asibiti ma Bari ma Daga nan can zan wuce naje na saka mishi kayan Nan ko da tsiya ne malam ga kudin da kace na canja su izuwa dala nagode sosai malam Allah ya Kara girma

Malam ya nuna mishi wata sabuwar tukunyar kasa Yana Fadin

“Saka su Nan ciki masu su zasu Dauka Nagode kome kenan kazo ka Sanar min.

Tukuro ya taho Yana Rike da kayan Al Mustafa Wanda akayiwa tsafi da siddabarun ya nufi asibiti inda ya Tara’s da Babu Al Mustafa a asibitin ya tambaya akace mishi sun taho gida sai ya biyo Bayan su inda kuma ya iske wani sabon labarin Wai Al Mustafa ya Rasu.

<< Azurfa Da Zinari 92Azurfa Da Zinari 94 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×