Page 4
Ummi ce ta fito tana faɗin “ ke maman fahat maza ki shiga tai tayinki kisan inda kike don kika nemi yiman masifa a gida yanzu zan lakaɗa maki shegen duka naga mai ƙwatarki don kinsan ko a jaraba ni uwarkice gaba nake da ke, ko kunya bakiji wai ina Fatima, ƙatuwar banza ƴar yarinya tai maki wayo, gaki kamar zaki wayo Amma ƙatuwar garace ke, to ki ƙara buɗe kunnuwanki da kyau kijini tun jiya munci nama da kuɗin nan kuma munci banza harda wofi, sai dai zanbaki albushir da zai maye maki raɗaɗin kuɗinki shine babu auren. . .
