Priyanka Nick Chopra
Gaisheki Jaruma Priyanka
Bakokwanto wuyarki ta isa yanka.
Giwa kike kin fi gaban karnuka
Daddawa ke kike gyara miyar kuka.
Hasken rana kike abin biɗa gun shuka
Alfaharin Bollywood kike jaruma Priyanka.
Ke mata suke shayi yau ba ki da tamka
Amaryar ɗan Jonas yau gare ki nake baituka.
Ke ce abin girmamawar mutanen Kudu
Ke ce abar alfaharin mutanen arewa.
Ke ce abar son jama’ar gabasawa
Ke ce mai sanyaya ruhin jama’ar yammawa.
Sarauniyar Bollywood babu mai tankawa
In ta fito dole mata su yiyo rusunawa.
Ko ba sa so dole su yo gaisuwar girmamawa
Jinjinar ban girma nake a gareki Priyanka.
Kyakkywa ce ita jaruma Priyanka
Attajira ce ita jaruma Priyanka.
Shahararriya ce ita jaruma Priyanka
Kuma gwana ce ita jaruma Priyanka.
Ta riga ta karɓu a Indiya Priyanka
Ta shahara tai suna a Amurka.
Ko ba ka sonta ka san ta ƙware Priyanka
Hakan ya sa a yau nake waƙe wacce bata da tamka.
Ni ne Jamilun nan na Kaduna
Al-katib da ke a Kaduna.
Salon aiki ne yau na nuna
A cikin saƙon wake daga guna.
Shekarar nan ta dubu biyu
Da ashirin har ma da biyu.
Sannu da kokari 👍
Though dai ni jarumar bata cika burgeni ba lol
Na gode sosai. Kin san dama haka rayuwar take. Amma wace jaruma ce ta fi burge ki?
Wow! Priyanka tana birgeni. Yaushe zaayi na hrithik Roshan?
Na gode sosai. Yana nan tafe in sha Allah
Dakyau.
Ina godiya
Yayi. Allah ya ƙara basira.
Na gode sosai
Hmmmmm to yayi.
Na gode sosai.
Sannu da ƙoƙari.
Yauwa na gode.