Skip to content
Part 14 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Akshay Kumar

Na gaida gwani na gwanaye 

wajen aiki ka wuce jaki, 

Namijin duniya kake 

sha-kundum kai ne tafki.

Majaujawar nasara ku ji 

Wannan ai shi ne Akki,

Balbela da farinta 

Kun san bata biɗar wanki.

Gwarzon maza sannu 

Da ƙara shekaru nawa,

Tabbas ka yi mun gani 

Kuma dole mu yo tafawa.

Ka yi haƙuri ya zam nasara 

Yau kai ke shanawa,

Zakaranka ya riƙa 

Yau ga waƙa yana rerawa.

Murnar birthday muke maka 

Domin yau ce ranar ka,

jajircewa har yau babu 

Wanda ko ya kamo ka.

Mun yi murna muna ƙara 

domin muna ƙaunarka,

Aikinka ai na musamman ne

Shi yasa muke daɗa bibiyarka.

Maƙiya sun sha haushi 

Kai kuma kullum sai tashi

Kai ne iska da bata

Biɗar fuffuke domin tashi.

Maƙiyinka fa kowaye 

sai mu ce a kamo shi,

Mu danne ɗan nema 

Mu shafe ido nai da toshshi!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 13

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.