Skip to content
Part 2 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Katrina Kaif

Katrina abar ƙauna

Katrina mai daɗin suna

Kyakkywa ce ita Katrina

Kallonki na sanyaya mini raina

Murmushinki na ƙawata raina. 

Ƙwarewarki ta shanye tunanina

Juriyarki ta haye hasashena

Jajircewarki ta ruɗa mafarkaina

Kafiyarki ta sani cikin ƙauna

Wayyo Wayyo Katrina mai kyau abar ƙauna.

Wajen rawa Katrina tana burge kowa

Wajen iya soyayya tana nishaɗantar da kowa

Gashi ta ƙware a dambe da kokawa

Tana da masoya a cikin Indiyawa

Tana da masoya a cikin Larabawa. 

Tana da masoya a cikin Amurkawa

Tana da masoya a cikin Hausawa

Tana da masoya a cikin Japanawa

Tana da masoya a cikin farisawa

Katrina tana da masoya har ma cikin yarbawa.

Kallon idonta kan sani cikin shauƙi

Kalmanta na fa da zaƙi

Murmushinta kan sani shiga yanayi

Kai da ganin sifarta ka godewa Buwayi 

Dariyarta kan sani jin nishaɗi. 

Muryarta a koyaushe tana da daɗi 

Wannan mace gaskiya ta ko’ina ta yi 

Duniya ta sanda ke ake yayi 

Maƙiyanki ko da gardama sun yi 

Da sun gane ki sai su koma wasu bayi. 

Ni ne Masoyinki Jamilu Abdulrahman 

Fatan ƙaunarki ko kaɗan za ki sammin 

Ko da ragowa ce na yarda abar min 

Don Allah murmushinki nake so ki ɗan min

Don Allah dariyar ki nake so ki ɗan min. 

Don Allah tafiyarki nake so ki ɗan min 

Don Allah ɗan farin nan naki ki yi min 

Ko da murguɗa baki ne ma duk ki yi min 

Ko ma duka ne duka na yarda ki yi min 

Koma menene na yarda ki yi min.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 1Ba’indiya 3 >>

8 thoughts on “Ba’indiya 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×