Skip to content
Part 3 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Shah Rukh Khan

Da fari na sa Rabbana da yai kowa 

Shi yai albasa da wake yai maiwa 

Tsira, aminci gun sahibi son kowa 

Wannan da saƙonsa ya je ga kowa

Wada darajarsa ta shafe ta kowa 

Wanda ba ya ƙyashin ya ba kowa 

Wanda ruhinsa ya shafe na kowa

 Baitin da na tsara, fatan ya amsu ga kowa. 

Ka yi murna da shagalinka gwanina

Ka more jin daɗin duniyarka sarkina 

Ka ɗaure ɗamarar ka zam kawai gwanina 

Ka tunkari aikinka babu batun wani kwana 

Ka kece raininka don ka fi ƙarfin a raina 

Ko an ƙi ko an so dai kana gaban arna 

Ko ba a sonka yau dai kana gaban ɓauna 

Shah Rukh gwanina, ka rabu da tunanuka, ka sanya Allah a cikin rai da addu’a.

In banda ƙaunar gaskiya da bata ƙarewa 

Ya za na bika da son nan da ba ya ragewa 

Ya za na gina gida wanda bashi rushewa 

Ya za na tara kalaman da basu ƙarewa 

Ya za na dasa itacen da bashi bushewa 

Ya za na shimfiɗa wundin da ba shi yagewa 

Ya za na ɗaura majanyin da bashi suncewa 

Shah Rukh gwanina da zaka ɗan ji uzurina, da ka canja akala kafin a gicciye kwana. 

In banda burin zuciya da ke mankantarwa 

Shah Rukh gwanina ya zarce duk gwanin kowa 

Aikin gwanina ya zarce na gwanin kowa 

Gami da baiwa duk ta wuce ta gwanin kowa 

Sauti, kalamai duk sun wuce na gwanin kowa 

Daidai da muryar sa fa ta fi hasashen kowa 

Hatta fahimtarsa ta fi ta gwanin kowa 

Shah Rukh gwanina da zaka ɗan ji uzurina, wallahi da anyi ruwa da tsakiyar rani. 

Kalma dubu na aje tanadi na waƙena 

Gami da sauti dubbai daban-daban guna

Don tanadi da tsumin fitowa a watarana 

Sannan in kaucewa tunanuka da ke bina 

In ɓadda sawayena ga masu nemana 

Sun ɗauki rayuwa mai tabbata gidan kwana

Gida ga mai burin rayuwa cikin ƙuna

Shah Rukh gwanina Allahu ya kiyaye ka. 

Mutum guda jiran biliyan Shah Rukh gwani gwarzo 

Ɗaya tamkar miliyan Shah Rukh ka zamo kadarko 

Sha-kundum kake ƙwarewarka ta zarce ko’ina 

Bango kake a jikinka Bollywood ta jingina 

Gaba dai mijin Gauri baban Aryan da Suhana 

Mai Raees da Fan da Main Hoon Na 

Taka sannu matakalar ɗan Johar da Aditya 

Shah Rukh gwanina, girmanka ya mamaye ko’ina. 

Na zama bawan ƙauna da bata ƙarewa 

Ina haƙa ya na mai rijiya da babu ruwa

Ina ta tihu zuciya tana ta fa nutsewa

Ina ta bautar ƙaunarka kuma ba ƙiwa

Ina biyewa muryarka ina ta wayewa

Giya ta so ta sanya ina ta yin shewa

Hatta tunani da sani da ke a ƙwaƙwalwa

Shah Rukh gwanina da ka fahimci uzurina, da ka yi ɗauki da ruwan kashe ƙuna.

Ubangijina ka taimaki Shah Rukh da taimakonka 

Ubangijina ka agaji Shah Rukh da agajinka 

Ubangijina ka tallafi Shah Rukh da tallafinka 

Ubangijina ka tsare shi da tsarewarka. 

Ubangijina sa hannunka mu ke nema.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 2Ba’indiya 4 >>

6 thoughts on “Ba’indiya 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×