Skip to content
Part 11 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Iskar lokaci ɗaya ta tsaya tamkar anyi ruwa an ɗauke.

Ganin waɗannan halittu ba ƙaramin dugunzuma hankalinsu Basma yayiba.

Jamcy da Basma tuni suka runƙunƙume juna jikinsu na mazari.

Wata mahaukaciyar dariya suka fashe da ida, wadda ta haddasama dajin. Girgiza.
“Kun ɗauka zaku iya guje mana ne,kunyi kuskure yanzu zaku girbi abinda kuka shuka.”

A suƙwane suka yo kan su Jafar tamkar yunwatattun zakunan da suka shekara basuci abunci ba.

Muggan makaman dake hannuwansu Suka fara kaima su Jafar hari da su.

Kowa kagani wurin takanshi yake yana ƙoƙarin ceton rayuwarshi.

In suka kawoma mutum harida makaman hannunsu ya kauce ya samu wani icce take iccen yake darewa gida biyu, in ƙasa ce makamin yasama sai dai kaga wurin yayi rami.

Basma da Jamcy wani Aljani yayo kansu da mugun nufi , sun riga sun sadakar yau kwanansu ya ƙare jira kaiwai suke ya iso garesu.

Shurun da sukaji ta sanyasu buɗe idanunsu cikin kaɗuwa.

Ganin Jafar sukayi tsaye riƙe da wani abu mai kama sa sanda gefenshi gawawwakin Aljanun nan yayi nasarar kashe wasu.

Cikin kakkausar murya ya fara magana.
“Yanzu ba lokacin tsoro bane, lokacine na tashi muyi fafutukar tseratar da rayukan mu ko mu mutu ko muyi rai, dan haka ku kasance masu ruƙo da addu’a domin ta tasa nayi nasarar kashe wasu daga cikin Aljanun nan dako taruwa mukayi bazamu iya yaƙarsu ba,amma saboda tasirin addu’a gashinan Ubangiji yasa nayi masarar kashesu, dan haka kumiƙe kuceci rayuwarku ko kuma kuyi asararta nan bada jimawaba.”
Yana ƙarashe maganar yayi wurin sauran Maridan bakinshi ɗauke da kabbara.

Kafin Maridan su ankara Jafar yayi masu gagarumar 6annan domin dayayi kabbara yadaka tsalle ya kaima tsakiyar bayan Aljani bugu saidai kaga yayi kururuwa ya zube ƙasa matacce.

Ganin irin illar da Jafar ke masu yasa mukayo kanshi da mugun nufin su raba kanshi da gangar jikinshi.

Addu’a yaci gaba da kwararowa abakinshi yana mai dogaro ga ubangijin shi tare da naiman ɗaukinshi.

Ƙarfin kabbarar da yake ta sanya Aljanun wasunsu yada makamai suna toshe kunnuwansu domin ji suke tamkar ana zuba masu ruwan tafasashshiyayar darma a kunnuwansu, ganin haka su Tk dake boye a mabanbantan wurare yin koyi dashi suna masu ɗaga murya tareda ƙwala kabbara.

Damar da Jafar ya samu ga Aljanun ta sanyashi ƙara ƙaimi wurin ragargazar aljanun, cikin ikon Allah yayi nasarar ƙararda Aljanun wasu kuma suka 6ace.

Iya jigatuwa Jafar ya jigata ga wata yanka da wani Aljani ya shammaceshi yayi mashi a hannu, yana gama faɗan ya yanke jiki ya faɗi.

Tk ganin Jafar ya ƙarar da Aljanun ya sanyashi fitowa suka yo kan Jafar.

Duk iya ƙoƙarin su akan jafar da wani taimako da zasu bashi sunyi, ga hannunshi dake zubda jini, Tk rigarshi ya yaga ya ɗaurema Jafar hannu yayi nasarar tsaida jinin, sunyi duk abubuwan da suka san anayi ma wanda ya suma domin ya tashi amma abin yaci tura domin ba alamun zai tashi.

Sunyi jigum_jigum suna tunanin halinda zasu shiga indai da gaske Jafar mutuwa yayi to bashakka kashinsu ya bushe a tafiyar nan.

Sunan nan zaune jikinsu ya gama mutuwa, zuciyoyinsu sun sadaƙar lallai Jafar bazai tashiba, ga duhun magriba daya farayi wurin ya ɗauki wani irin sanyi mai shiga ƙashi.

Hannunshi dake ɗaure yafara motsawa a hankali yana ƙoƙarin buɗe idanunshi bakinshi ɗauke da addu’a.

Ganin haka yasa su Tk sukayo kanshi zuciyoyinsu cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa.

Kamashi Tk yayi ya ida miƙewa zaune.

Sannu suke ta keta kwararo mashi yana binsu da yawwa.

Sai da Jafar ya ida dawowa cikin hankalinshi sannan ya umarcesu dasu tashi suci gaba da tafiya, domin zama bai gansu ba.

Tafiya suke ga duhu daya yayi tsayawa sukayi sukai taimama suka gabatar da sallolin da aka biyo su.

Ƙara nausawa sukayi cikin jejin duk da yunwar da ta addabesu ga matsanancin sanyin da ake zubawa hakan bai hanasu cigaba da tafiyaba.

Yada zango sukayi saboda baccin daya rinjayi idanuwansu.

Wurine mai yalwar ciyayi ko ina ka wurga idonka lullube yake da ciyawa tamkar cikin yanayin damuna.

Kwantawa sujayi Jafar ya umarci kowanensu da yayi addu’ar kwanciya bacci kafin ya kwanta.

Bayan kwanciyarsu Jafar ya warware hannunshi domin ganin yadda raunin ya koma.

Abunda ya tada mashi hankali kuma ya bashi mamaki bai wuce ganin yayi wani irin rami tamkar an yanke fatar wurin, addu’o’i yacigaba da kwararowa yana tofama raunin domin yasan babu abinda ya gagari Allah.

Kowa yayi bacci wurin in banda Jafar da sai da yatofe jikinshi da addu’a ya kuma tofe inda suke kwance ya kakka6e inda zai kwanta ya kwanta bakinshi ɗauke da Basmala.

Wurin yayi tsi! Bakajin motsin komi sai munsharin da Tk ke yi kamar wani bujimin sa.

A hankali wata irin iska mai kaɗawa cikin natsuwa ta gauraye wurin, ciyawar dake ƙasan wurin a hankali ta fara kaɗawa rana motsawa, Bayyana sukayi cikin muguwar suffar mai tsananin ban tsoro.

Rashin sani yafi dare duhu, domin dasu Jafar sun san inda suk kawo kawunansu da tuni tun bar wurin.

Tsaye suke jikinsu baida maraba da jikin Fatalwa, gasu wasu irin dogaye fuskarnan tasu ba kyangani idanunsu guda ukku jere reras basuda hanci sai wani irin bakuna tanan suke shaƙar iska, fuskar su cike take da gashinda yayi nasarar lullu6e ilahirin fuskar,ga jikinsu sanye da wasu fararen kaya da jini yayi nasarar mai dasu jajaye.

Cikin tsananin 6acin rai macen takawo hannu da nufin ta ɗauko Jafar ta tsotse jininshi, sai dai mi, hannun na ida isa inda Jafar ke kwance taji wani irin zafi Kamar ta sanya hannunta cikin Wuta, bashiri tayo baya tana mai yarfa hannunta da fatar wurin ta dare jini Ya fara zuba.

Ganin abinda ya samu matar ya Sanya mijin zura hannuwanshi biyu da nufin ya tattaro su Jafar su duka ya hallakasu.

Abinda yaji yasanyashi ja da baya ga hannuwanshi dasuka fara ƙonewa.

Yaja matarshi suna mamakin abinda ya yi masu shamaki da kashe waɗan nan halittu, bacewa sukayi zuciyoyinsu cike da ƙudirin ɗaukar fansa.

Kamar cikim bacci Jafar yaji hayaniya amma yana buɗe idonshi yaga babu kowa.

Addu’a ya ƙarayi tare da komawa ya kwanta.

Sanyin asubar daya ratsasu shine yayi nasarar farkawarsu daga bacci,buɗe raunin hannunshi Jafar yayi, abun msmaki raunin nan ya warke tamkar bai ta6ajin ciwoba wurin, taimama sukayi suka kabbara sallah bayan sun gama suka zauna suna tunanin inda zasu samu abinda zasu sama bakinsu.

Gari na ida yin haske suka tafi naiman abinda zasuci.

Ƙoramace mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kana hango yadda kifaye ke wasansu saboda ruwan ba zurfi.

Shawara suka yanke sukama kifayen su gasa su ci.

Jafar da Tk su suka shi suka samu wasu dogayen tsinkunan icce suka riƙa chako kifayen dashi.

Basma da Jamcy suna daga wajen ruwan suna kallonsu, Basma jitayi kamar ankira sunanta waigawa tayi tareda hango wasu kyawawan kifaye sunata iyo nesa kaɗan da inda su Jafar suke kama kifayen.

Zuciyarta kwadaituwa tayi data matsa taganema idanunta waɗannan kifaye, duƙawar da zatayi domin ta kamo kifin Taji an fizgi wuyanta anyi Cikin ruwan da ita, ƙarar faɗuwar ta tajawo hankakinsu Jafar suka nufo inda take aguje, abinda suka gani ne yasanya numfashinsu yakusa ɗaukewa na wucin gadi, Mandiya suka gani kamanninta sun koma na horror, ƙarar dasukaji Basma ta ƙwala ce ta dawo dasu cikin hankalinsu, Mandiya suka gani ta kasama Basma haƙora awuya jini yafara malala, wata wahalallar ƙara Basma ta Ƙwala………………….

______________________________
Gudun ceton rai su Rabson suke tamkar zasu tashi sama ga waɗannan halittu Dasun Juya sai suka sun kusa cimmasu.

Abinda basu saniba halittun nan kamar fara haka suke Tashi sama.

Basu ankaraba sai gani sukayi halittun nan sun dira gabansu, ja sukayi suka tsaya kafin su ankara halittunnan sun lullu6esu tamkar yadda fara ke lullu6e ganye.

Biba gani tayi halittun nan da ƙarfi taɗaga murya tana ƙwararo addu’a tana kai masu naushi da hannuwanta, duk wadda ta kaima bugu saida kaga tafaɗi ƙasa ƙasusuwanta sun karairaye.

Rabson dayaga biyu sunyo kanshi gudu yafara kafin ya ankara sun wawuro ƙafafunshi, ganin sun buɗe baki sunyo kanshi ya fara ihu yana karanto duk addu’ar da tazo bakinshi
“Innalillahi, la’ilaha illallahu, inna ansarnahu, amanarrasulu, wayyo kaka ɗan bunsurulle, wayyo Salma masoyiya ku kawo mani ɗauki.”
Haka yaita ihu, ganin babu mai cetonshi yafara gano mutuwa ido buɗe yasa ya dage iyakar ƙarfinshi yana kaima halittun harbi da ƙafafunshi.

Kulu da Nas wuri ɗaya suka haɗe Nas ganin halittun sun nufoshi Ya koma bayan Kulu yana.
“Kulu ki taimaka mani wayyoh Allah innalillahi nashiga ukku, Kulu kin cuceni da kikasa mukayi wannan Baƙar tafiyar.”
Yaƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikon Kulu.

Ganin addu’ar da Biba tayi Allah ya kawo mata mafita, ta ɗaga murya tana mai umarta su Rabso dasuyi koyi da ita.

Sunjigatu sun matuƙar jin jiki kafin suyi nasarar gamawa da halittun.

Fuskar kowa tasha karta duk sawune jiki in banda Biba.

Bayan sun sun dawo cikin hankalinsu Rabson yayi ƙarfin halin miƙewa.
“Kun lura kuwa har yanzu muna cikin kogon nan? Kamata yayi mubar kogon nan nidai bazan tsaya in mutu a banza ba.”
Ya ida maganar yana dudduba inda Salma ta shige.

Chan ya hangota ta tayi ɗai ɗaya a ƙasa tana maida numfashi.
“Hhh, Salma masoyiya kece kika zama haka?, kinga yadda kikayi buɗu_buɗu, wayyo masoyiya miya karceki a fuska taimaka kitashi muƙarasa fita.”
Ya ƙarashe maganar yana yimata dariyar mugunta.

“Allah ya isa inka ƙara kirana Masoyiyarka, mugu mai suffar mutanen 6oye.”
Taƙarashe maganar tana ƙoƙarin miƙewa.

Baikulata ba dariyarshi yacigaba dayi.

Kulu kallon Nas tayi tare da jan dogon tsoki.
“An daiji kunya, kabani mamaki lusarin banza kawai wanda mace ma tafishi jarunta.”
Ta kuma jan wani tsokin.

“Am..uhm..kingane Kululu wallahi kawai kinsan ni ina tsoron ƙwarangwal, amma kin gane kibari a karo nagaba zani baki mamaki, haba my sweet Kululunah.”
Ya ƙarashe maganar da daɗin baki.

“Allah dai yasa da gaske kake.”
Tafaɗa tana yamutsa fuska domin yau Nas ya matuƙar bata haushi.

Sun yi yawo cikin kogon harsun gaji basu samu hanya ba.

Har sun haƙura da fita daga kogon sai suka hango wata ƴar hanya ƙarama wadda mutum ɗaya zai iyabi ya wuce, haka suka riƙa fita da ɗai ɗaya.

Ganin sun fita kogon wani irin farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu.

Abinda idanuwansu suka hango masu ne yasasu ja da baya cikin matsanancin tashin hankali da kuma tsoro…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Tafiya 10Bakar Tafiya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×