Skip to content
Part 9 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Ganin anjanye Mandiya yasan ya su Jafar tsananin ruɗuwa suka ƙara himma wurin yin iyo.

Da ƙyar suka samu suka ƙaraso ga6ar ruwan.

Kowa ka kalla fuskarshi cikin firgice take da tsananin tashin hankali.

Basma tunda suka fito take zazzaga uban aman ruwa, saboda ruwan da ta shaƙa.

Aman da takeyi kamar zata amayo ƴan hanjinta.

Jamcy kuka kawai take tana tashiga ukku lokacin mutuwarta yayi, da ta sani da bata fito ganin kwaf ba.
Tk bai hanata yin kukan ba dominshima a halinda suke ciki inda zaiyi kukan zai fijin sauƙin abinda Yakeji cikin zuciyarshi.

Sun ɗan jima awurin suna jimamin abinda ya faru da Mandiya.

Ɗunguma sukayi sukabar wurin suna tafiya da ƙyar jikinsu babu kuzari.

Jamcy faɗuwa tayi ta tare da fashewa da kuka.
“Wayyo masoyi, Mutuwa zaniyi bani iya tafiya, ga yunwa nikeji, dan Allah koɗan naman kifi kayo iyo cikin ruwan nan ka gasa mani inci , ni bazan iya cigaba da tafiyaba.”
Taci gaba da kukanta.

Galala suka yi suna kallonta.

Basma kallon bakida hankali tayi mata cikin 6acin rai ta fara zazzaga bala’i.
“Ke yanzu in baccin kin maidamu marasa hankali da tunani irinki, gidan ubanwa zamu samu maki irin waɗan nan kayan?, ko kitashi mutafi ko muyi gaba mubarki nan wurin.”

Zagita aikoma Basma dashi cikin masifa dake cinta ta miƙe tayo kan Basma.
“Ke harkin gaya mani wannan maganar?, kinsan ko wacece Jamcy bala’i, nayayimi kankazar_kazarki kaga tunkiya uwar tan6ele ke in banda gantali miya fiddoki kika baro mijinki kika fito yawon gantali.”

Tatss! Kakeji Basma ta ɗauke Jamcy da kyakykyawan mari, chakumar juna sukayi sukai faɗi kowa tana naushin ƴar uwarta, an rasa mai raba faɗan sunyi tsaitsaye sunkasa koda furta kalmar kudaina faɗan.

Ƙyalesu sukayi suka samu wuri suka zauna suka zuba masu ido.

Sun bugu sunjigata.

Jamcy da taji bugu fuskarta ta chanza kamanni samu tayi ta kubce daga hannun Basma takoma gefe tana maida numfashi ta fara magana da ƙyar.

“Muguwa azzaluma, wannan ai zaluncine ace ana faɗa bazaki bari a huta ba sannan muci gaba dan zalunci ,muguwa mai suffar agwagwa Allah ya isana ban yafe maki ba.”

“Nikike kira mai suffar agwagwa?, kiƙara maimaita abinda kika faɗa yanzu in take maki kai in maimaita maki bugun da yafi wannan 6allagaza mai zubin muciya.”

Basma ta ƙarashe maganar tana huttai.

“Idan kun gama faɗan kutashi mucigaba da tafiya, nikam kunkusa daina ganina dan tsaf zani rabu daku in raba tafiya daku.”

Jafar ya ƙarashe maganar ranshi a 6ace.

Harararshi Jamcy tayi tana gunguni.

“Kai kuma maloho kayi sakaka kana kallo wannan matar tayi mani wannan bugun, wallahi zaka gane in muka koma gida.”

Tk banza yayi ya kyaleta kamar baijita ba, domin shi yanzu abinda ke damunshi taya zai tseratar da rayuwar da daga wannan Baƙar tafiyar.

Sunyi tafiya mai ɗan nisa suka samu bishiyar ruman suka tsiga suka sha suka zauna suna hutawa.

Motsin da sukaji alamun takun sawun mutum ya nufo inda suke yasanya su ɗago kawunansu.

A firgice suka miƙe tsaye suna kallo cikin matuƙar mamaki atare suka furta Rabson!.

Tsaye yake yana kallonsu yana murmushi.

“Nine zuwa nayi domin intafi daku wurin sauran abokan tafiyarmu, tunda kuka bace mana muke yawon naimanku sai yanzu Allah yasa na ganku.”

Cikin zaƙuwa Basma tayo wurinshi, “yauwa Mutumina Rabson ina su Salma da su Biba.”

Jin an ambaci sunan Biba yasa Jafar matsowa domin yaji inda aka baro mashi abar ƙaunarshi.

“Suna chan suna jiranku, kuyi sauri mu ƙarasa wurinsu.”

Ɗunguma sukayi suka mara mashi baya.

Sunyi tafiya maitsananin nisa har suka fara gajiya da sunce Rabson har yanzu bamu iso ba sai yace masu ku ƙara haƙuri munkusa ƙarsawa.

Wani wuri suka iso mai matuƙar duhuwa ga yawan bishiyoyi ganyayen jikinsu duk sun zubo ƙasa, ta cikin duhuwar suk riƙa ratsawa har suka iso wani bangare daya matuƙar basu mamaki.

Gani sukayi Rabson ya tsaya yaƙi gaba yaƙi baya.

“Rabson mun iso ko?.” Basma ta faɗa tana ƙoƙarin shan gabanshi, dariyar daya tuntsire da i ta ce tasanyasu ja da baya bashiri.

Suffarshi tariƙa rikiɗewa tana kasuwa kashi_kashi yana komawa wasu irin maridan Aljanu hannuwansu ɗauke da muggan makamai tamkar waɗanda zasuje yaƙi.
Ga wata iriyar guguwa da ta turniƙe wurin…

Ida haɗewa tsutsar tayi wuri ɗaya tana wata irin dariya mai haddasama kunnuwan bil adam ɗaukewar jin su na wucin gadi.

Rabson da Salma haɗe suke suna kuka suna sambatu domin yau sun fidda rai da rayuwarsu, Salma wani zazzafan fitsarine ya wanke mata ƙafafu batareda tasani ba.

Tsutsar dariyar datake ta tsagaita tafara magana cikin amon sauti tafara magana.
“Yaku waɗannan halittu masu tsananin taurin kai yau kwananku yazo ƙarshe kushirya baƙuntar lahira.”

Jin wannan jawabi ba ƙaramin tada hankalinsu Kulu da Nas tuni jikin Nas ya fara rawa tsabar tashin hankali.

Tamkar maciji haka tsutsar tasulalo tayo kan Kulu da Nas.

Ihu suke suna naiman agajin abokan tafiyar su, amma ina suma ta kansu suke.

Tsalle tayi tadira jikin Kulu, ƙara Kulu ta fasa tana”Nawan kataimaka mani kacire mani ita, kayi sauri wayyo nashiga ukku Nas kodai bakajin minike faɗa ne?.”

Nas cikin muryar da ta gama karaya yafara magana tsoro ya gama baibayeshi.
“Aa Kulu na barki har abada kiyafe mani Allah yatsayar da mutuwarki ke kaɗai kinga tafiyata kiyafe mani, in ana doyayyah alahira muyi a chan.”
Ya ruga aguje yayi bayansu Rabson da suke ƙoƙarin guduwa bankesu yayi ya ƙwara kan Salma dana Rabson yayi gaba.

Basuji zafin abinda Nas yayi masuba suka bi bayanshi.

Biba kowace addu’a tazo bakinta furta ta take tana naiman kariyar ubangijinta.

Kulu tariga ta yanke rai da tsira ta sadaƙar yau mutuwa zatayi.

Ganin halinda Kulu take cikigasu Nas sun gudu, wani ƙarfin hali taji yazo mata lokaci ɗaya ta furta, “LA’ILAHA ILLAH ANTASUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIM, ya Allah ka kawo mana ɗauki, kafitar damu daga wannan bala’in ya Allah mundogara gareka ya Allah kakawo mana mafita.”

Tashi tayi tanufi inda Kulu take ga wannan tsutsa ta kanannaɗe ilahirin jikinta, wani ƙarfe tagani mai suffar wuƙa, ɗaukarshi tayi ta nufi inda Kulu take, shammatar tsutsar tayi ta luma mata wannan ƙarfen ajiki bakinta ɗauke da addu’a take ta saki Kulu ta ƙwala wata irin ƙara, take wurin ya6ule wani ruwa green mai kauri ya riƙa fita tamkar anbuɗe famfo, nan tagama bullayi ta mutu.

Kamo hannun Kulu Biba tayi tana mata sannu, tashi tayi jikinta duk ya baci saboda faɗuwar da tayi, lura Kulu tayi daga ita sai Biba da ƙyar tabuɗe baki tana tambayar ina sauran abokan tafiyarsu.

“Yanzu dai ki miƙe musamu mafita daga nan.”

Biba ta kamo hannunta.

Wata kunya ce takama Kulu da ta tuna da rashin kunyar da ta yima Biba ɗazu amma yanzu gata itake taimakonta.

Lallai duniya kakiyayi wulaƙanta mutum bakasan ranar da zai maka wata rana ba, ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane duk yadda ka ganshi.

Abinda idanuwanta suka hasko mata ya kusa datse numfashinta na wucin gaɗi, jikinta kyarma ya ɗauka tamkar mazari, hannunta yana kyarma ta ɗagoshi tana nunama Biba abinda idanuwanta suka hasko mata.

Ruwan jikin wannan tsotsane ya dunƙule ya rarraba kashi_kashi yana wata irin kumbura tamkar zai tashi sama, a hankali yake miƙewa tamkar yadda hayaƙi keyin sama yana miƙewa,wasu irin halittu masu suffar ƙwarangwal saidai su basukai tsayin ƙwarangwalba gasu da ƙaton kai yatsun hannuwansu kwara ukku rak!,idanuwansu jajur tamkar garwashin wuta jikinsu irin na ƙwarangwal sak.

Misalta halindasu Biba suka shiga bai misaltuwa, ga halittun sun fara miƙewa,Biba hannun Kulu ta kamo suka bi bayansu Rabson aguje.

Sunyi rasarar riskarsu Rabson, “ya kunkashe tsutsar?”

Salma ta tambaya tana maida kallonta ga Biba.

“Ta mutu amma kuduba bayanmu wani sabon bala’in ke tunkaro mu.”ta ƙarashe maganar tana maida numfashi da ƙyar.

Hayaniyar da sukajiyo tasasu juyawa ganin abinda ke faruwa, halittun ne sun nufo inda suke bakunansu buɗe.

Ganin haka yasasu bin wata wangamemiyar ƙofa dasuka gani tabi tacikin kogon.

Bawan Allah Rabson yana gudu wani dutse ya taɗe shi ya faɗi kasa warwas, da rarrafe yasamu yana bin bayansu Alkah yabashi sa’a yayun ƙura yamiƙe tare dayi bayansu, ga waɗannan halittu biye dasu bakunansu buɗe.

<< Bakar Tafiya 8Bakar Tafiya 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.