Skip to content
Part 13 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Ta k’are maganar tare da murgud’a baki. Babu shiri ya fashe da dariya, irin wacce sai yabyi watanni ba tare da ya yi irinta ba. Saboda ya fi yawan murmushi mai sauti fiye da dariyar da za a ce ya yi har muryarsa ta tashi. Amma Munawwa ta saka shi yin irinta bai shirya ba, sai da ya yi dariyarsa son ransa kamar ta kashe wayar sannan ya ce,

“Am telling the truth, ki ba ta shawara idan har ta gyara halayenta za ta samu mijin kirki. Idan kuma ta ci gaba a haka to gaskiya akwai matsala, ki yi hak’uri da ni saboda na san kin ji haushi na, tuba nake kaina bisa wuya my angel!”

Munawwa ta yi shiru saboda gaba ki d’aya ya kwance mata notukan kai. Haka suka ci gaba da hira ya saki jiki sai zuba mata hira yake yi mai cike tsantsar so da kauna. Ita ma ba ta ware suka ci gaba da soyewarsu a fakaice. Don ita Munawwa har a lokacin ba ta yarda da cewa son shi take yi ba, saboda ita ganin take yi da nauyi ace tana soyayya da d’an aikin gidansu. Amma kuma ba ta jin nauyin sakin jiki su yi ta soyewarsu.

Bayan sun k’are wayar ne mummy ta turo k’ofar ta shigo ɗakin. Kuma shigowa ta uku ce tana tarar da ita suna wayar, ba tare da ita Munawwarar ta san da zuwanta ba. Saboda shauk’in soyayya da ya kwashe ta, Mummy a ranta ta ji dad’in ganin ‘yarta ta samu wanda take so, saboda yadda ta ga annushuwa a fuskarta ya tabbatar mata da cewa ba k’aramin so take yi masa ba.

Da sauri ta ajiye wayar tana murmushi jin kunya ta ce,

“Yanzu fa nike so na je na ce miki na dawo.”

Mummy ta fad’ad’a fuskarta da murmushi, duk da zuciyarta babu dad’i saboda fushin da Daddy yake yi da ita. Uwa uba ciyon Munara da ya tsaya mata zuciya. Idonta a kan na munawwa ta ce,

“Ai ga ni na zo da kaina na tarar da ana ta waya da surukina, wane ne shi? Kuma a ina yake? Sannan d’an waye a garin nan?”

Munawwa ta sauke k’wayar idanuwanta a k’asa tana cewa,

“Laaa Mummy ba fa wani ba ne Aliyu ne.”

Babu shiri k’irjin Mummy ya buga, a cikin tantama tace,

“Wanne Aliyun?”

Munawwa tana ‘yar dariya ta ce,

“Aliyu dai na gidan nan.”

Mummy ta kalle ta cikin tabbatarwa ta ce,

“Aliyu sabon d’an aikin gidan nan?”

Munawwa ta d’aga kai Mummy ta b’ata fuska a lokaci d’aya ta ce,

“Mene ne tsakaninki da shi to, da kuka d’auki tsawon wannan lokaci kuna waya?”

Munawwa ta daburce gaba d’aya saboda kallon da Mummy ta k’ure ta da shi cikin rawar baki ta ce,

“Mutunci ne kawai amman babu komai fa Mummy”

Mummy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,

“To ki kiyaye, don ba na son abin da zai sa Daddynku ya yi masa korar wulak’anci a gidan nan, kin dai san halin shi ba sai an yi miki dogon bayani ba.”

Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kan fuskar munawwa, wad’anda ta kasa gano ko na mene ne, Mummy ta kalle ta cikin mamakin kukan da ta gani a kan fuskar munawwar. A cikin zuciyarta ta ce,

‘Na shige su, ALLAH ya tsare kada zargina ya zamo gaskiya.’

A fili ta ce,

“Me aka yi miki ne da kike kuka?”

Munawwa ta share hawayenta sannan ta ce,

“Ba komai Mummy.”

Jiki a sanyaye Mummyn ta ce,

“ALLAH ya zab’a miki na alkhairi.”

Munawwa ta ce, “Amiñ” a cikin zuciyarta wanda lab’b’anta ne kawai suka motsa.

Kiran sallahr magarib ita ce ta katse musu hirar, Mummy ta mik’e a tsaye sannan ta ce,

“Yau ba asibitin za ki kwana ba?”

Munawwa ta ce,

“Eh Daddy ya ce na dawo gobe, saboda da safe za a sallamo ta.”

Mummy murya a sark’e ta ce,

“Abincinsu fa ya za a yi da shi? Ga shi ba yaro gare mu ba. Amma bari na kira Yusuf ya zo ya kai musu don ba na son ki koma ya yi fad’a, tunda har shi ya ce ki dawo gida.”

Sosai Munawwa ta ji dad’i don har ta fara hango kanta Daddy yana ball da ita a cikin asibitin. Mummy tana tafiya ta ce,

“Kira shi ya san da zancen, da ya k’are SALLAH sai ya zo ya kai musu.”

Sannan ta fice d’akin, Munawwa ta jawo wayarta ta danna masa kira, ringing d’aya biyu ya d’auka bayan sun d’an gaisa kai tsaye ta sanar da shi sak’on Mummy. Ya ce daman yanzu da sun k’are SALLAH asibitin zai je ya kai su Mama, waton mahaifiyar shi da abokiyar zamanta.

Yusuf d’a ne a wurinn yayan Daddy Alhaji Musa, wanda suke uwa d’aya uba d’aya da Daddyn, yana da mata biyu da ‘ya’ya sunfi goma a gidan shi. Tsakanin mata da maza, wasu sunyi aure, sannan still har yanzu akwai matasan samarin da ‘yanmata a gidansa.

Yana k’are sallah’r ya kwaso iyayen shi da ‘yanmatan gidan su biyu ya zo da su, sai da suka gaisa da Mummy tare da yi mata ya jikin Munara sannan suka nufi asibitin.
Munawwa ko bayan sun k’are cin abinci da Mummy ta k’ule d’akinsu, wanda take jin kewar Munara saboda ita kad’ai za ta kwana a kan gadon nasu. Bayan ta yi komai na aladarta kafin ta kwanta sannan ta jawo wayarta ta shiga chatting. Kwatsam sai ga number’r da aka ta turo mata saƙonni masu dad’i, an yi mata magana da ita. photon dpn da ke kan lambar; wani matashi ne mai jini a jika, kyakkyawa ne shi, kuma mai fad’in fuska. kalar shi chocolate color ya sha k’ananun kaya. Pic d’in ya had’u, ko kayan da ke jikin shi za su tabbabar da cewa naira ta zauna a jiki, sai da ta k’arewa pic d’in kallo sannan ta bud’e saƙon.

‘Hello’

Ta mayar da amsa da

“Hy”

Sannan ya k’ara rubuta

‘Munawwara ko?’

Ta rubuta

“Eh, amman plss ina ka san ni? Kuma ina ka san sunana? waye ya ba ka lambata?.”

Ya turo emoji mai d’auke da murmushi kamar haka 😅 sannan ya ce,

‘Duka ni kad’ai wad’annan tambayoyi? To ki kwantar da hankalinki ni masoyinki ne na gaskiya. Na dad’e ina d’awainiya da sonki sai ga shi yanzu na yanke shawarar na fallasa kaina, saboda haka very soon zan bayyana kaina har cikin gidanku da fatar za ki tarbi bak’onki da hannu bibbiyu.’

Munawwa ta yatsine fuska sannan ta mayar masa da reply kamar haka

“ALLAH ya nuna muna lokacin lafiya.”

Ya ce, ‘Amin, na gode sosai. Amma ba ki tambayi sunana ba har yanzu, ko ba kya buk’atar sani ne?’

Ta turo emoji kamar haka 🤩 sannan ta ce,

“Sorry mene ne sunan?”

Ya ce, ‘No problem my favorite, kina magana da muhammadu Nuraddeen!’

Munawwa ta zunb’uro baki sannan ta ce

“Thanks! Nice name”

Sannan ya ce,

‘My gift fou you; zai zo unexpected! Amma don ALLAH kada ki ce ba za ki karb’a ba.’

Ta sauke ajiyar zuciya kamar tana ganin shi sannan ta yi masa reply kamar haka,

“Da ka bar shi kawai, don ni ba na son karb’ar abu a hannun wanda ban sani ba.

Saboda haka idan har da gaske kake yi; to ka zo gidanmu first kafin ka yi mini kyautar komai. Saboda yanzu idan ma ka ba ni abu ta ya zan bayyana wa iyayena kai? Alhali ni kaina ba sanin ka na yi ba, to me kake so na ce musu su yarda da ni?”

Shiru ya yi na minti biyu kamar bazai ce komai ba, sai can ta ga yana typing ta kur’e kallonta a kan screen d’in wayar saboda ta k’agu ta ji amsar da zai ba ta. Sai ga shi ya saki ya shigo d’irrrrr! Idonta a kan saƙon babu shiri ta yi wata guntuwar dariya sannan ta yi mere, saboda abin da ta ga ya rubuto ya ba ta matuk’ar dariya wai,

‘Mijinki ne nan da sati biyu masu zuwa idan Allah ya kai mu.’

Munawwa ta fara typing tana dariya ta mayar masa da amsa kamar haka,

“A auren wasa irin na d’iyar ‘yar tsana ko?

Ya turo da emoji mai nuna alamun fushi kamar haka 😔 sannan ya ce,

‘Shekaruna ba su kai matsayin da zan aure ki ba ne halan?’

Munawwa ta turo d’an dariya kamar haka 😅sannan ta ce,

“Sorry ba abin da nike nufi kenan ba, kawai dai na ga daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zak’i? Daga had’uwar yau kawai shi kenan sai zancen aure nan da sati biyu? Sai kace wacce aka ce maka an gaji da zamanta gidansu, ana neman hanyar da za’a rabu da ita? Ai ko da ka zo gidan namu kamar yadda kace; to ba haka kawai daga zuwan farko za a ce da kai ka je ka shiryo ka zo an ba ka ni nan da sati biyu aure ba. Cab! Aure sai kac e irin na wasar yara?”

Ta k’are maganar tareda sako d’an dariya kamar haka😆.

Aikuwa yana k’are karantawa y ayi saurin typo ta shi maganar kamar haka,

‘Ai abin rabo ne ni, na san ni mai sa’a ne, domin ban fito ba sai da na shirya. Na sha tabara na sha yasin.’

Munawwa ta k’yalk’yale da dariya sannan ta ce,

“Sannu gagarabadau!” Tare da sako 😊haka.

Sannan ya ce,

‘Seriously zan zo satin nan, amma kafin na zo sai gift d’ina ya riga ni zuwa.’

Munawwa ta yi saurin typer masa, “No kada ka yi tunanin zan karb’a, koma mene ne matuk’ar ba kai ka fara zuwa first ba, don ban san me zance da su Mummy ba, so ka jira kawai idan kazo sun ganka d’in shikenan.”

Ya ce,

‘Sorry my heart beat, ba na k’asar shi ya sa, amman da na dawo i promise to you zan zo gidanku mu gaisa da Daddy.’

Munawwa ta ce “Hmmm na ji, amma fa ina kan bakana.”

Ya yi murmushi sannan ya ce,

‘Pic’s d’inki plss koda guda goma ne zanyi manage PLSS and plss my golden girl.’

Tare da turo wannan👏🏻har guda uku, jikin Munawwa ya yi sanyi ta shiga gallery ta d’auko pic’s d’inta uku ta tura masa, suna shiga ta yi saurin kashe datar, tare da ajiye wayar ganin k’arfe 1:24am. Hakan ya sa ta tashi tsam ta shige toilet, minti biyu a tsakani sai gata ta fito tare da d’oro arwallah. Kai tsaye ta shinfid’a carpet d’in SALLAH sannan ta saka hijabi ta fara jero nafilfili, sai da ta yi raka’a takwas sannan ta zauna tana ta kai kukanta wuri UBANGJI ALLAH a kan ya biya mata buk’atocinta, kuma ya kawo mata mafita a cikin lamurranta. Ta ayi wa ‘yar uwarta addu’a sosai akan ALLAH ya ba ta dangana a kan wannan mayaudarin HAIDAR d’in da ta nacewa, sannan ta yi wa Daddynsu Addu’a akan ALLAH ya fahimtar da shi gaskiya ya gyara tsarin gidan shi a kan hanya madaidaiciya.

Sannan ta k’udundune anan saman carpet d’in saboda baccin da ya ci idonta, amma duk da haka daga kwancen sai da ta zura hannunta ta janyo wayarta ta duba saboda k’arar shigowar saƙon da ta ji, aikuwa tana dubawa ta ga haka.

‘Shi ne kika gudu kika bar;ni ko? Bayan kin san dole ne na magantu, amma babu komai a hakan ma nabgode gudnyt sweet dreams, my sunshine baby.’

Munawwa ta kashe wayar duka sannan ta janyo filo ta d’ora kanta, zuciyarta sai sak’e sak’e take yi domin ta kasa tantance matsayin shi a zuciyarta, domin ita dai ta fi jin natsuwa da ALIYU duk da dai har lokacin ta k’i yardar wa zuciyarta tsananin soyayyarbshi da ta mamaye zuciyarta tun tana tunani har bacci b’arawo ya yi awon gaba da ita.

*****

A B’angaren Basarake kuwa, mai sabon suna Muhammadu Nuradden,wanda sunan abokin shi ne na k’ud da k’ud ya yi amfani dabshi, har pic d’in ma na shi ne ya saka a kan dp don kawai ya ji dad’in shigar da ita komar basajarsa. Ganin pictures d’in da ta turo masa ya sa ya k’ara dulmiya a cikin kogin k’aunarta, saboda tsananin kyaun da ta yi a photunan duk da kowane pic ba wanda ta bayyana tsiraici, guda d’aya ma sai da tayi rolling d’in gyalen ya zagaye ‘yar faffad’ar fuskarta, sauran biyun kuma ta aza d’an karamin gyalen kawai ta sako lebunan gyalen a gaban doguwar rigar da take sanye a jikinta.

Sai dai ta yi kyau matuk’a fuskarta ta fito rad’am a jikin photon, ya kurewa photon kallo babu bambanci da picture’s d’in munara da ke wayarbshi, idan ban da yanayin shigarsu da rashin ji da Munara ta ninka Munawwa da shi ko a cikin picture’s d’in. Domin ita har wad’anda daga ita sai kayan bacci duk tura masa take yi babu ruwanta, babu shiri ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya nace wa kallon hotunan dole sai ya gano abinda ya bambanta su amma ya kasa. Saboda Munara da Munawwara identical twins ne komai nasu iri d’aya ne banbancinsu kawai ta b’angaren shiga da halayyarsu, wadda ko a minti biyu za ka iya banbance su saboda Munara mutunci ya yi mata k’aranci, yayin da Munawwara kirki idan yana yawa sai ace nata ya yi yawa.

Basarake haka ya kwana da begen masoyiyarshi. Munawwa, yayin da ya goge kaf photunan Munara akan wayoyin shi. Saboda ya fi son ya san Munawwa d’in ce kawai a cikin galleryn shi, don ba ya son duk wani abu da ya dangance ta kamar yadda ya goge komai nata a zuciyar shi.

*****
Daddy kuwa yana can asibiti da babyn shi sai aikin lallashinta yake yi, dak’yar ya samu ta d’an kwantar da hankalinta saboda alkawullan da ya ta d’aukar mata, shi ya sa ta nutsu domin ita ma ta matsu a sallamebta tabji dad’in nemo HAIDAR d’inta duk inda yake.

Shiyasa abincin da Yusuf ya kawo musu ta saki jiki ta ci, shibma daddyn ganin ta natsu taci abincin shibma ya sauko daga fushin da ya yi na k’in cin abincin Mummy. Ya ci na shi sosai sannan ya dinga bai wa babyn shi labarai masu saka zuciyarta a nishadi, har bacci ya yi awon gaba da ita sannan hankalin shi ya kwanta.

*****

Tun da sassafe Munawwa da Mummy suna kitchen suna aiki had’a abun breakfast nasu da na kaiwa asibiti, koda 7:30am tayi duk sun kammala komai sannan Munawwa ta je ta sullo wankanta, tare da yin simple make up, ta saka wata doguwar rigar kanti wadda ta ji aikin stone a gabanta, sannan ta d’an aza k’aramin gyale a kanta ta nad’o shi.

A falo ta fito suna karyawa ita da Mummy sai ga Yusuf ya yi sallama ya shigo, bayan sun gaisa ko zama bai yi ba ya nemi a ba shi abincin ‘yan asibitin ya kai masu, saboda yana sauri ya wuce School. Ita ma kanta Munawwa saurin da take yi kenan saboda makarantar take so ta wuce, don kwananta biyu ba ta je ba gabshi jiya wata k’awarta ta…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 12Bakon Yanayi 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×