Skip to content
Part 23 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Munawwa ta fara kuka tana rok’on shi a kan ita ba ta son shi ya dawo ga Munara, cikin zafin nama ya yi cikinta da duka da k’yar ta samu ta fito d’akin,, ido rufe ta fara saukowa daga saman amman bai daina biyar ta yana dukan ta ba, ta fad’i babu shiri, sannan ta fara gangarowa tana kai k’arshen step ta baje babu alamun numfashi a tattare da ita. 

A d’ari Mummy ta k’araso wurin tare da janyo ta jikinta ta fashe da kuka tana fad’in, “Wayyo ALLAH ya kashe mani ‘ya.”

Munara da ke d’akinta sautin dukan da Daddy ke yi wa Munawwa, yasa jikinta har rawa yake yi ta fito domin kawai ta gani ta yi dariya, ganin Munawwa tana gangarowa daga sama ya sa ta ɗora hannu a ka tare da gwalalo idanu waje, hankalinta ya tashi sosai musamman da ta ga ko motsi ba ta yi ba bayan ta fad’o, da gudu ta k’araso wurin tare da dafe bakinta zuciyarta cike da fargabar kada a ce ta mutu, Daddy kam yana ganin aika-aikar da ya yi jiki babu kuzari ya sulale ya koma d’akinsa, zuciyarshi cike da tsananin tsoro da fargaba don bai san wane hali take ba, amman girman kai ya hana ya je ya gani ko da zai samu natsuwa. 

Mummy kam tana rungume da Munawwa tana kuka gwanin ban tausayi, tare da kiran sunanta tana jijjiga ta, da ta ga ta k’i motsawa ta ajiye ta aguje ta je ta bud’a freezer ta d’auko ruwa a wani k’aton jug mai bala’in sanyi, tana zuwa ta watsa mata ruwan gabad’aya, babu shiri Munawwa ta zabura a firgice tare da fashewa da kuka tana neman inda za ta b’uya, saboda tsammaninta har lokacin Daddyn dukanta yake yI, Mummy ta yi saurin rik’o ta tana kiran sunanta idon Munawwa a rufe tana cewa,

“Don ALLAH ka yi hak’uri Daddy na tuba ba zan sake ba.”

Mummy ta yi saurin had’a ta da jikinta ta rungume, tana bubbuga bayanta tare da shafa kanta alamar lallashi, Munawwa ta ture ta a cikin firgici ta arta da gudu ta shige d’akinsu, kai tsaye ta shige Wadrop d’in kayansu ta b’oye tare da k’udundunewa sai mutsu mutsu take yi, Mummy da Munara suka biyo ta, motsinta da suka ji a cikin Wadrop ya sa suka nufi wurin, tana ganin Mummy ta bud’e murfin ta fasa arniyar k’ara, har sai da suka dafe kunnuwansu duka. Mummy ta fara k’ok’arin fiddo ta tana mak’alewa tare da bugewa Mummy hannu a firgice tana ci gaba da kuwwa. 

Daga Mummy har Munara tsaye suka yi suna ganin Ikon ALLAH, saboda abin ya so ya shalle tunaninsu, don saboda gabad’aya Munawwa ta fita hankalinta, sai abubuwa take yi irin na tab’in ƙwaƙwalwa gabad’aya jikinsu ya yi sanyi, Mummy kam duk da tirjiyarta sai da ta yi dubarar fito da ita ta rungume ta jikinta tana kuka, domin zuciyarta tana ta kai komo a kan Munawwa ba ta cikin hayyacinta, sai ga shi ta tabbatar mata da zarginta, don kuwa fisgewa ta yi daga jikin Mummy ta shiga janyo kayanta da na Munara tana sakawa a jikinta wani kan wani. Babu shiri Mummy ta fashe da kuka cikin tashin hankali ta ce da Munara ta tsare ta kada ta bar ta ta fita, za ta je ta fad’o wa Daddynsu abin da ke faruwa, Munara ta bi Munawwa da kallo Mummy ta fita jikinta yana rawa kamar ta fad’i ta nufi d’akin Daddy, a firgice ta fad’a d’akin ko sallama babu ta ce da shi, “Kazo a kai Munawwara asibiti ba ta da lafiya.”

Daddy ya bi ta da kallo sororo, ya kasa magana. Sai da Mummy ta k’ara maimaita masa cikin d’aga murya ta ce, “Munawwara ba ta da lafiya! A kai ta asibiti yanzu a shawo kan matsalar tun kafin abin ya yi tsauri!”

Daddy ya ja key ba tare da ya ce da ita k’anzil ba ya fito ta biyo bayansa da sauri, sai ga Munara tana kokawa da ita a kan ba za ta fita ba, da ta ji haushi ta gartsa mata cizo a hannu, babu shiri ta sake ta ta zunduma da gudu za ta fita, cikin tsawa Mummy ta d’aga murya ta ce, 

“Kada ka bar ta ta fita ba ta cikin hayyacinta” 

Caraf Daddy ya ri’ko ta sai fisge-fisge take yi a kan sai an bar ta ta fita,Mummy ta je ta sako hijabinta jikinta yana rawa ta fito, ta tarar da Munawwa ta k’ara firgicewa sai kici-kicin fisgewa take yi a hannun Daddy tana runtuma kuwa, tana zuwa ta ri’ko hannunta tana tirjiya suka fito daga cikin gidan, kai-tsaye motar Daddy suka nufa da k’yar suka saka ta da taimakon Baba Isah, sannan Daddy ya fisgi motar da k’arfi suka nufi wata private hospital, yanayin da suka gan ta ya sa aka yi saurin karb’ar ta aka shiga da ita emergency room, sai kurma kuwa take yi ko’ina ana jin sautin muryarta tana bai wa Daddy hak’uri a kan ba za ta sake ba. 

Mummy ta kai zaune babu shiri ta fashe da wani sabon kuka, Daddy ma jikinsa ya yi sanyi k’alau saboda zuciyarsa ta tabbatar masa da fad’uwar da ta yi ce sanadi. 

****

Basarake yana barin k’ofar gidan ya haye acab’a ya nufi hotel, zuciyarsa cike da tunani ya shiga d’akin da ya sauka inda Nuradden yake zaune yana jiran shi, shigowar shi ke da wuya Nuradden ya ba shi hannu suka yi musabaha cikin barkwanci ya ce, “Ya dai saurayin budurwata?”

Basarake ya yi d’an murmushin yak’e tare da ya kai hannunsa ga clips d’in da ke wuyan rigar Nuradden ya cire, sannan ya yi wani munafukin murmushi ya d’auko computer tare da ciro wani abu jikin clip d’in ya saka a jikin computer’. Nuradden yana biye da shi da kallo saboda mamakin Basarake da ya cika masa zuciya, saboda ganin plan d’in da ya had’a masa wanda shi kansa bai san da shi ba, jiki a sanyaye ya zo ya zauna gefen Basaraken idonsa a kan fuskar computer, sai ga d’akin bak’in su Munara an hasko ɗan lokaci kafin ta shigo d’akin ta zauna, tiryan-tiryan hoton abin da ya wakana ya yi ta haskawa tare da duk maganganun da suka tattauna, har zuwa k’ofar gida inda yake tsaye da Munawwara da barazanar da Nuradden ya yi masa, har zuwan hotel d’in da d’akin da suke ciki yanzu, sai dai shi Nuradden ba a ganin fuskarsa sai muryarsa kawai da ke fita, sannan dukansu suka sauke ajiyar zuciya, Nuradden ya kalle shi yana dariyar yak’e mai cike da jin haushin abin da Basaraken ya yi masa, waton dai abin nufi kamar bai yarda da shi ba, ransa a jagule ya ce, “Trust to me my man, alkawali na d’auka ko wani ba zan tab’a bari ya cutar da kai ba balle ni, amman idan ka san zuciyarka tana kokwanto a kaina ka cire ne kawai ka ci gaba da fighting d’in kai d’aya.” 

Basarake ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya furzar da iska mai zafi a bakinsa sannan ya ce, 

“For give me my man, na yi hakan ne kawai don ba na son a fad’a mini na fi son na ji kuma na gani da idona, believed me i trust to you kai ma ka sani.”

Ya k’are maganar tare da bubbuga kafad’arsa, Nuradden ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “What’s our next target?”

Basarake ya rufe computer ya nutsa cikin zurfin tunani sannan ya ce, “Ta ce na turo iyayena, kuma ni ba na son na sako su Abba a cikin lamarin har sai na tabbatar da ta cinye sauran exam’s d’in.”

Nuradden ya kai masa duka yana dariya ya ce,

“B aka da kyau mutumina, yarinyar nan fa da gaske take son ka don ALLAH ka tausaya mata haka nan plss.”

Basarake ya tashi tsam ya fara tafiya hannuwansa a baya ya fara zirga-zirgar neman mafita, sannan ya ce, “Na san tana so na amman akwai amfanin cikasa plans d’in, don lokacin da duk gaskiya ta bayyana ‘yar uwarta ba za ta ga na ci amanarta ba, domin na tabbata ita ko jarabawa d’aya ba za ta ci marking ko d’aya ba balle ta cinye duka, saboda haka zan yi amfani da damata na damalmala mata tunaninta da na mahaifinta. Saboda na san lokaci zai zo, wanda ita da shi duka za su durk’usa gwiwa bibbiyu suna neman alfarma a wurina, ni kuma a lokacin na riga da na yi masu nisa dukansu.”

Ya k’are maganar cikin zafin rai, wanda har b’acin ran ya bayyana a kan fuskarsa, Nuradden ya ta so ya dafa shi cikin sigar lallashi ya ce, “Easy easy abokina, yana da kyau ka ci gaba da jajircewa amman don ALLAH ka sassauta.”

Basarake yana k’ok’arin yin magana Malam Isah ya kira shi, har ta tsinke bai d’auka ba don ko dubawa ma bai yi ba balle ya gano wa yake kiran, aka sake kira na biyu Nuradden ya je ya d’auko cikin ‘yar dariya ya ce, “Baba Isah ne fa.”

Da zafin nama ya karb’a tare da sakawa kunnensa, amman ya kasa cewa komai saboda zuciyarsa da yake ji babu dad’i, Baba Isah kai-tsaye ya zo da maganarsa yana cewa, “‘Yar gidanka ce aka fito da ita babu lafiya sun nufi asibiti, don kamar ma shafar aljannu ne ko tab’in hankal…”

Da k’arfi Basarake ya ce “What!!!!!!!” Babu shiri ya kai zaune tare da maimaita INNALILLAHI wa’inna ilaihirrajiun a cikin zuciyarsa, Nuradden ya karb’i wayar yana tambayar Baba Isah abin da ke faruwa, ya maimaita masa duk abin da ya faru, jiki babu kuzari ya kashe wayar, sannan ya koma lallashin Basarake da ya rud’e sai kiran lambobin Munawwa yake yi da layinsa mai sunan Nuradden , suna ta ringing ba’l a d’auka saboda wayar tana d’akin Mummy kan gado, sannan a silent take balle Munara ta jiyo k’ararta ta d’auka.

Nuradden ya ce da shi llya sake kiran lambar Malam Isah ya tambaye shi a wane asibiti aka kai ta, ya kira Baban ya ce shi ma bai sani ba, amman bari ya fad’o masa lamber maigida ya tambaye shi ya ji. Cikin farinciki Aliyu ya ce yawwa baba dubo lamber sai na sake kira, da sauri Baban ya fita ƙofar gidan, ya yi sa’a wani matashin saurayin unguwar zai wuce, kasancewar akwai sanayya a tsakaninsu ya kira shi ya ce da shi, idan an kira wayar ya lissafo lamber da ke jikin bangon d’akinsa, sai ga shi minti uku a tsakani Aliyu ya kira yaron yana fad’a masa, yana lodawa a d’ayar wayar har ya k’are sannan Baba isah ya karb’a suka yi sallama, ya yi wa yaron godiya da sa masa albarka. 

Jikin Basarake yana tsuma da gumin da ya dinga tsiyayo masa ko’ina saboda tashin hankali, ya danna kiran Daddy sannan ya mik’a wa Nuradden aka yi sa’a tana shiga ya d’auka, duk da bai san mai lambar ba, Nuradden cikin murya mai cike da kasaita ya fara yi wa Daddy sallama, bayan sun gaisa ya sanar da shi wane ne, jikin daddy ya fara kyarma saboda girman da yake bai wa Nuradden a matsayin d’an hamshak’in mai kud’i, Nuradden ya wayance kamar bai san abin da yake faruwa ba ya ce, 

“Na yi ta kiran lambar Munawwara ba ta d’auka ba, shi ne na ce bari na kira ka na ji ko lafiya.”

Daddy jikinsa yana tsima ya ce, “Eh WALLAHI ba ta da lafiya muna asibitin Daula an shiga da ita emergency.”

Nuradden ya ce, “Subhanallah! Ga ni nan zuwa yanzu tun da ALLAH ya sa ban bar garin ba.”

Cikin jin dad’i Daddy ya ce, “OK ALLAH ya taimake ka, sai kazo.”

Sannan suka yi sallama Mummy ko kallon shi ba ta yi ba balle ta tambayi wane ne, saboda haushin shi da take ji tun da suka zo asibitin ba ta ce da shi k’anzil ba, sai fatar samun sauk’in ‘yarta take yi don ta sha alwashin da ta ji sauk’i dole ne ta nuna masa b’acin ranta a kan cin zarafin da yake yi masu ita da Munawwa, sannan ta nuna masa aibin bambancin da yake nunawa tsakanin ‘ya’yansa. 

Babu b’ata lokaci suka k’araso asibitin don shi Basaraken ya rud’e sosai ko fuskar da yake sakawa bai saka ba haka ya fito suka garzayo asibitin, zuwansu ya yi daidai da fitowa da Munawwa daga emergency room d’in, aka gangaro ta ankan d’an k’aramin gadon d’aukar majinyata, sambal tamkar wata matacciya saboda allurar bacci da aka yi mata, da gudu Mummy ta bi gadon sai hasbunallahu wani’imal wakil take fad’a a cikin zuciyarta, saboda firgicin da take a ciki tana fatar zuciyarta ta sami salama, Daddy kam bai bi su ba saboda ganin su Nuradden da ya yi ya tsaya suna gaisawa, fuskar Basarake da ya gani yasa ya k’ara rud’ewa saboda ya shaida fuskar kasancewar shi ma’abocin kallon news tare da karatun jaridu, fuskarsa ba b’oyayyiya ba ce a wurinsa duk da bai tab’a ganin shi a zahiri ba, jikinsa yana rawa ya mik’a masa hannu suka gaisa tare da kallon Nuradden bakinsa yana motsi ya ce , “Ka ce ba kai kad’ai ka zo garin namu ba! Ashe har da babban bak’o kuke tare? Lalle yau na yi farin gani tun da…. “

Da sauri Basarake ya katse shi zuciyarsa cike da jin haushin shi ya ce, 

“Ina mara lafiyar ne?”

Sai a lokacin ne Daddy ya tuno da abin da ya kawo su, cikin jin kunyar kansa ya ce, “Ku zo mu je ranka ya dad’e yanzu aka shigar da ita wani d’aki.”

Suka bi shi baya sai surutu yake zuba musu wanda ba ya da tushe balle makama, saboda tsananin rud’ewar da ya yi sanadin yin ido biyu da yaro da kud’i, kuma abokin manya, waton ALIYU HAIDAR BASARAKE. 

Koda suka shiga d’akin kukan Mummy ne ya tarbe su, jiki babu kuzari suka k’arasa jikin gadon saboda tsananin tausayin da ta ba su, Basarake ya kur’e kallonsa a kan fuskar Munawwa yana jin soyayyarta tana k’ara fisgar shi, tare da tausayin halin da take ciki babu shiri ya dafe goshi, saboda muguwar sarawar da kansa ya yi. Nuradden ne kawai ya saki jiki yana yi mata addu’ar samun sauk’i, Daddy ya jawo kujerun robar da ke d’akin guda biyu ya ce su zauna, Nuradden ya zauna amman Basarake kikam ya yi ya kasa zama saboda bai ma san abin da Daddyn ya fad’a ba, sai da ya sake cewa,

“Ranka ya dad’e ka zauna ga kujera nan.”

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya zauna idonsa akan fuskar Munara, sai ga Dr ya zo da wata farar takarda a hannunsa yana kai gaisuwa wurin su sannan ya ce da Daddy akwai maganar da za su yi akan matsalar Munawwa, idan ba damuwa ya biyo shi office su tattauna, da sauri Daddy ya ce, “Ai nan duka ba bare fad’a kawai. Ni Mahaifinta ne ga Mahaifiyarta, sannan wannan shi ne Mijin da za ta aura.” Ya ƙare maganar yana nuna…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 22Bakon Yanayi 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×