Skip to content

Haka akeson yan uwa sukance suna son farin cikin junan su Neehla ce da Neehal suka karaso cikin shigan atamfa dinkin riga da skirt me ratsi fari da ja sunyi matukar kyau kaman yayan larabawa.

Mom yaushe ne za a yanka ma yaya cake don yaune ranar dazamu nunamishi farin cikinmu sosai kuma inaso yana yankawa inyasa miki yasa ma dad nima na taya shi yanzu za ayi tafi sukaga akeyi sosai dukan suka mike suka karasa inda yazid yake suna karasawa ya yanka sai bakin Mom itama tasa mishi ta mishi nuni da Nadiya ya gyada mata kai allamun ok yana yankawa ko kallonta beyi sai sama ta a hanci ranta ya6aci amma bata nunaba itama ta yanka kaman zata kai bakinsa saita sa mishi a a hanci da fuskanshi bakiya daya kowa sanda yayi dariya ganin yadda Nadiya ta6ata masa fuska da cake shima ya mata dad kuwa yayi farin cikin hakan Dan shi yadauka soyayyane besan kuma baso a janda yazid ba Nadiya ce kawai take ta rawa da waka ba me tayata a haka a ka kammala taro ya watse kowa yana farin ciki yazid ma ya manta da Nadiya ta shafa masa cake a fuska.

Daki yashiga domin yin alwala yakara gdy ga wanda yakaishi wannan matsayin da be ta6a tunanin zama ba yana shiga yatsinci kanshi da kallon fuskanshi a madubin dake jikin mirror me zaigani fuskanshine ya 6aci da cake shisai yanzuma yanzuma yatuna lalle yarinyan nan zanyi maganin ki yadda ko ance kisake min makamancin haka bazakiyiba shikadai yasan yadda zai yi mata

Bangaren Zahra kwance take akan tsunman gadonsu tana karatu karatun ma baya shiga ta ajiye littafin tafara waxai taimakamin da kudin da zanbiya nayi register wayek daya bangaren kudin jin yan mahaifiyata gashi inbasamuba zata iya rasa rayuwarta no no Zahra banshirya ganin wannan ranaba ummata zanyi duk yanda yakamata ace ya”ta taimake mahaifiyar zanyi gara ni nashiga kunci danaga mahaifiya ta a cikin wannan yanayi to amma kafin menene mafita?

A ina zansamu kudi? Ko aikatau birni kije Kiyi zaki samu kudi taba kanta amsa a takaice to amma zasu yar da subani kudin aiki na shekara guda kuwa. Gaskiya zanyi tunani akan wannan har samu mafita tashi tayi tafita tsakar gida yayi daidai da shigowan zainab cikin gidan tafiya tana yauki tana tauna cingum sannu da dawowa Anty zainaib ke Zahra dakata aikin menene naje nayi dazaki cemin sannu aa anty Kiyi hkri bansan hakan zai6ata miki raiba kai Zahra kin raina ni harda cewa bakisan zai 6atamin raiba to wlh yau saikinyi danda kinsanin yimin rashin kunya,aa anty nace Kiyi hakuri da hakuri ya mutu sadakan nawa kkban shiru tayi saboda tasan halin zainab yanzu zata mata duka kuma tasata aiki me wahala suna hanata abinci da zuwa islamiya kuma ba me cewa komai to wama zaiyi mgn ko lokacin da mahaifiyar ta take da lfy bata magana intasa baki to wannan ranar Babba zaice ta rainashi yayi ta zagi to bare itakuma loma daya maganar zainab ce yadawo da ita daga duniyar tunanin da tashiga kihuce muje ga yarinya sai shegen girman breast komai ta hada duk abinda na miji ke bukata amma taki tashigo harka ta dangwali arziki ta wallahi sainayi maganin ki ke da uwar ki kuda kwanciyar hankali kunyi hannun riga zonan ta fincikota da karfi kamar zata fadi kasa ta wanke mata fuska da lafiyayyun Mari harguda biyu daga yau na kashe zuwa islamiyan ki da man Boko kan bakuda kudin karasawa to shima na yanke kin min daidai zainab daman ai abinda yakama ceta shine tamana bauta duk abinda suke mata be dametaba saboda idan da sabo ta saba amma abinda yafi daga mata hankali shine islamiya duk runtsi tana jin sanyi ta wannan 6angaren kusani cewa Allah yana tare da me hakuri zanmuku duk yanda kukace amma kuma karku manta akwai yauma tubula sara i ranar da kowa zai girbe abinda da ya shuka na alkairi kona shari.

Mommy ..mommy..momm na am Nadiya tunkafin kikaraso kk kirana fadamin meye labari hmm mommy ai wallahi dad ya dauka nida yazid soyayya mukeyi kae babyna naji dadin wannan labari kinga a gefe guda bamuda matsala yanzu mungama da matsalan farko saura na yazid da mahaifiyarsa to mommy ai naga Mom bata da Matsala dana cemata ina taya yazid farin cikin kinga yanda ta nunamin a fuskanta hmm Nadiya bakisan wacece Hajiya Rabi ba a fuska zata nuna tafi kowa sonki amma a cikin zuciyanta akwai nata manufan daban itama Sai mun tashi tsaye mahaifin yazid ma saimun kara tashi akansa in mungama dasu sai mudawo kan yazid ok mommy amma fa me zai hana kawai ki tunkare Daddy da maganan in yadawo daga a merica eh zan mishi maganan kinsan daddy nki bayason rashin adalci zaice saiya amince da bakinsa kafin a yi maganan aurenku yess mommy amma yanzu ta ina zaki fara?? zan nima turai akwai wani malami dazamu je hurinsa shizaima aikin komai kisa aranki kamar kin aure barrister yazid kin gama sai yanda kkyi dashi
I love u mommy shiyasa nake matukar sonki.

Wacce Ce Mommy?

Mommy takasance yar alhaji sani attajirin me kudine mahaifinta duk abinda da takeso shiya ke mata yana matukar son diyar tasa saboda takasance itakadaice diya Mace a hurin tun kafin takai shekara ashirin ya mallaka mata wani babban company yabata motoci guda uku duk abinda takeso shiyake mata ana haka ta wata Rana taje wani restaurant tana zaune ta dora daya akan daya tana dadda na wayana dama ita al adartace..wata mashiyar yarinyace wacce bazata haura ma shekarunta itama indan kaganta kasan wata yar alhjine taja daya daga cikin kujaran da saratu take zaune ta itama ta zauna kusa da ita.

Kee yar waye dazakizo kija kujera kixauna a kusadani to cewan larai ni yar ubankine harke yar waye dazan zauna kusa dake kaja kazama wawiya shasha mai sufar a…. Kafin ta karasa saratu ta kwasheta da wasu zaffafan marika har guda biyu Tasss tasss sanda taga taurari harke kin isa kigaya min magana cikin magana na barki wane u…. Itama taji saukan maruka guda uku ramukon gayya yafi gayya zaffi.

Kae kae cewan saratu wanan Mari da kikamin saikin girbeshi koba yanzu ba wlh kinyi kadan kice zan girbe Marin da namiki ke asuwa Kk loma daya nida kudi zanyi amfani na rama abinda kkmin kuma kisani sai kinyi nadama hmmm ke yarinyace ni bada kudi zanyi amfaniba nida illimin na ke yi muzuba mugani ni larai saina Saki kinyi tsiya saikin zama abin Allah wadarai.

Tofa, nidai nayi shiru.

Haka rayuwa tacigaba dayi musu bawan da yasake ganin dan uwansa tsakanin larai da saratu amma kowa yasan labarin junansu kuma suna bibiya.

Wata Rana da alhaji Ahmad dabazai ta6a mantawa ba ranar da ta kasance shine kaddararsa na auren saratu yammane ga hadari yana ta faman haduwa gashi gari yafara yin baki ga tayan motonsa ta lalace kuma ba me gyara a kusa da gurin ya rasa yadda zaiyi can gyafe yazauna yayi tagumi yafara tunanin mafita ta yadda zai bar garin a yau tashi yayi yafara tafiya don niman mafita ko Allah zaisa yayi dace da wani me gyara horn akafara mishi ba kakawtawa ya tsaya matashiyar yarinya yagani wacce ashekaru bazata haura 21 years tafito tafara masifa ku kenan kuna tafiya inkunga moto sai kutsaya in ya bige ace yayi jinya shashashu kawae dalla bani hanya na huce tunda tafara masifa bata kalle wanene ba har tagama shima 6angarenshi tunda tafara yatsira mata tayi matukar yimasa kyau shidama yanason mata wacce zata tsaya ta kwatama kanta hanki wacce baza a zalince shi ko ita tabari ba zata dau mataki.

Amm naceba dan Allah zansa mu number wayan tunda naganki naji nasamu matar da zan Aura.

Juya Wanda zatayi wa zata gani hammshakin dan kasuwan nan tagani matashi me tashen kudi hammdala tafarayi amma saboda karta nuna wani sai ta basar aa bawan Allah wani irin maganane kuma kace nabaka number na mezakayi dashi inaso ne murinka gaisawa sanda taja mishi aji sosai ta bashi tundaga wannan rana suke gaisawa akai akai ahaka suka fara soyayya dashi.

Harmagana yaje gaban Manya da farko da yaje da magana gurin mahaifiyarsa bata yarda saboda tasan halin saratu da irin rashin tarbiyan yarinyan amma da yanuna lalle shi ita yakeso ta bashi tabishi da Allah yasanya albarka akayi maganan aurensu ba asa wani lokaci me tsayi saboda dukansu kowa ya matsu sati 6 aka tsayar wato wata daya da sati biyu.

Bayan sati biyar biki akeyi sosai kowani 6angare suke ta shiryaye alhaji Ahmad ya sanar da saratu ce wa abokinshi koma amininshi alhaji Muhammad zaizo daga kasar Dubai yace dashi za ayi komai ok dama kaga bansan babban abokin mijina naba amma inyazo zansanshi tabbas zaki sanshi harda matanshima da yaron daya ok Allah yakawo su lafiya.

Yanzu me kk bukata na hidiman bikin mu?

Gaskiya babu saboda abbana yamin komai saede hidiman dinner da sauran party ok bakida matsalan baby na ok mijina I love you too.

I love u more.

Bayan kwana hudu alhaji Muhammad ne da matarsa hajiya rabbi sun iso Nigeria lafiya a ranar dasuka iso sukaje gidan su saratu amaryan amininsa Ahmad tayi musu tarba me kyau tunda taga alhaji Muhammad taji tanasonsa amma lokaci yakuremata kumashi babban sojane yafi mijinta da mahaifinta ga yaronsu kyakyawa fari tass dashi yarona menene sunanka cewan saratu BARRISTER yazid wow nice name kace kae barrister ne hakan yayi yarona da gsk Mom yess dukansu sukayi Dariya.

Suna zaune suna ta6a hira kadan kadan. Aka jera musu gaban su da kayan motsa baki da su snacks sadwet pizza da kayan fruit sunci amma ba sosaiba.

Ahaka suka kammala sai wajen yamma sosai suka huce gidansu dasuka sauka
Alhaji Muhammad shi mutun ne son wasa da raha.

Komin taulaci mutun indai ka girmeshi zai baka girmanka shiyasa yake da jama a abin hannunshi be dameshi ba yanada yawan kyauta kuma yanason yaga yayi adalci duk da shi sojane shiyasa yakeso yazid yazama barrister shiyasa yake kiranshi da BARRISTER Yazid harya saba duk inda sukaje da mahaifinsa in aka tambayeshi menene sunanka yaro saiyace BARRISTER yazid abin yana burge mutani sosae gashi yarone kwakwata shekaransa 6 ne amma ko a makarnta shiyake zuwa na daya. Anyi biki lafiya ansha shagali sosai ankai amarya dakinta saide muce Allah yabada zaman lafiya.

Bookmark
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.7 / 5. Rating: 3

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Barrister 1Barrister 3 >>

1 thought on “Barrister 2”

Drop a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.