Skip to content

Barrister 3

Bayan Wasu Lokaci

Larai taji labarin auren saratu kuma kudiri anniyan zaman aminiyanta wacce zata amince da ita.

Taje tasameta tabata hakuri akan abin da yafaru a tsakaninsu da farko ta nuna baxata hakura ba saida larai ta rinka yimata magiya ta hakura.

Suka zumun har tana bata shawara tana daukawa itama saratu tana bata
Ahaka rayuwa tacigaba har suka zama aminan juna bayan shekara daya da rabi saratu ce ta zauna ta tashi takasa zama huri guda saboda yanda takeji likitocine mata guda su ke mata sannu Hajiya karki damu insha Allah zaki sauka lafiya bayan awanni 2 ta haife yarinyan ta Mace me kama da ita ya Allah duk wacce takeda ciki Allah kasauketa lfy
saratuce take kwance asaman gadon asibiti akan wani kayataccen gado gefe guda kuma gadon ya rane akasa mata babynta a ciki.

Assalamu alaikum cewan Hajiya Rabi da danta suka shigo saboda alhaji yakirasu a waya yasanar musu cewa Hajiya saratu ta sauka lafiya gasu a asibiti nanda nan tasanar ma mijinta yace aeni yafara gayamin matarsa ta haihu ok to Bari nasa a hada abinci a tafi dashi asibitin ok to bamatsala yakamata a tafi da abinci.

Ciki ciki ta amsa mata da wa alaiki salaam ta karaso da kulolin abincin dake cikin wani kayataccen basket na xuba abinci abincine kala kala masu saukin sarrafawa aciki tazauna a kujeran dake kallon gadon da take kwance tafara mata sannu ya jiki ??
a hankali take amsa mata dasauke

Allah yakara lafiya Ameen

Alhaji Muhammad da Ahmad suka shigo atare basu fi minti goma da shigowa ba dangin saratu dana alhaji Ahmad suka zo anci a sibiti ciki kuwa harda aminiyan ta larai kowa yaxo ganin yarinyan da mahafiyanta

Bayan kwana 7 anyi suna lafiya Yarinya taci suna Nadiya

To saide muce Allah ya raya

Tunda Hajiya saratu ta haifi Nadiya tace ita yarinya daya ta isheta taje akamata alluran dena haihuwa

Nadiya nada shekara 7 a lokacin kuma yazid yanada shekara goma shabiyar ya fara zama saurayi yarone miskili bashida sonyin surutu gashi da izzah kuma de kunsani basai nakarasaba

Yazid yana da shekara 23 mahaifinshi yakai Dubai yakarasa karatunsa na likita

Cigaban Labari

Kai yarinyan nan kinsamu bakin mayar min da amsa kamata tayi ta muntsike mata baki har sanda yayi jinni.

Kije ki kwashe kayana ki wanke min cikin sanyin murya tace to nima ganawa ki hada dashi dana Hafsat ki wanke kaya dayawa tafito dashi itama zainab tafito danata kayan yayi yawa amma ba tausayi ba imani Haka suka bata tashi tayi ta kwashe wanki taje can nesa tafara wankewa duk abinda suke mata ummanta tana kwance a zaure tana jinsu kwalla ne ke gangaro mata tana tunanin rayuwar Zahra yazata kasance nan gaba inbata raye wani irin garari rayuwarta xaikasance a ciki koda yake akwai Allah wata rana rayuwar ta zai inganta ita kadai take maganan zuci.

Mama meyasa kike bama anti Zahra aikin wahala keda zainab hafsat kenan har yanxu baki da wayo yar ubace fa ko itama intasa mu dama haka xata miki keda zainab aa ni nasan ba haka halin anti Zahra yake ba intasamu abu burinta kowa ma yasamu rannan ma haka tabani naira 50 wai itama kyauta aka bata nace tabari tace na Kar6a in taci ita kadai ma zai kare gsky kune kawai bakwa gani amma ni nasan halin tana gama fadan Haka ta huce xuwa inda Zahra take dauraya maman ta na kiranta amma ina ko kallonta batayi harta isa can inda Zahra take wanki ta tsuguna anti Zahra tajuyo ta kalleta Dan Allah Kiyi….no Hafsat karkice komai nasani wata rana sai labari eh haka anti Zahra amma yakamata kema ki ringa kwata ma kanki yanci zalinci da ake miki a gidan nan yayi yawa Hafsat kinmanta da cewa wahala bata kisa.

Eh haka ne yawwa Bari na tayaki aa kibari baruwana ae wallahi saina tayaki haka tasa hanu suna atare tasss taji saukan wasu lafiyayyun maruka guda biyu nasaki aiki shine zaki sa ya”ta zo tayi baki isaba wlh aa Mama nice da kaina nasa hannu ba ita bace tace nasa hannu na tayata ai wannan zalincine Hafsat nice kk cewa zalinci lallai ma kuwa amma bakida kishin kanki.

Bangaren yazid kwance yake a kan bed yana tatta6a laptop nashi saboda anturo mishi da wani aikine dazaiyi.

*****

Zahra kin gama wankin ne ko haryanxu baki karasaba cewan zainab Kiyi hkri anti zainab na kusa kammalawa kai to nabaki minti 5 kikarasa kizo kimin girki Don nasayo kaza kezaki gyara ki wanke kisoya min kuma.. Saitayi shiru tohh anty in sha Allah yanxu zanxo na miki kin cece kanki.

Sanda takai tsahon mintuna 15 kafin takarasa Tasha masifa da zagi da zainab akan me zanbaki mintuna 5 kikai minti 15 ok saboda kinrainani ko aa anty bahakabane toya yayane cewan Zahra kinsan kayan yanada yawa shiyasa nima banso yakai haka batare da na kammala ba.

Rufe min baki kije Kiyi aikin Dana saki ok hucewa tayi taje inda ta ijiyemata Kazan ta dauka.

Dama kafin tagama wanki ta gaya mata inda zata dauka Kazan gyarwa tayi ta wanke shi tasss ta dora akan huta tazuba Maggi gishiri curry citta albsa etc ta hada a ciki ta dauki wajen mintuna 45 kafin ta karasa soya Kazan saboda murhun itace ne.

****
Ya na cikin aikinsa a laptop ya ga wayan sa na ruri ya dauka dagawa yayi asalamu alaeikum daga daya daya 6angaren aka amsa da cewa wa alaika sallam amm nakammala hada maka coffee n din amma yayi sanyi yanxu na hada wanine nakawo maka ne.

Ok shigo dashi befi minti biyar ba kukun yakaraso da coffee a hannun shi barka da dare ya daga masa hannu ya ijiye ya juya.

Yakai mintuna uku kafin ya rufe laptop din ya dauka coffee ya fara sha dama shi al adarsace Kafin ya kwanta sai yasha coffee shiyasa indai yana gari to kullun sai ankawo mashi.
Washegari da karfe 7:30 ya shirya cikin kayanshi na barrister toci saboda yau akwai wani Shari a dazasu gabar a court yayi matukar kyau cikin shigan kayan.

Hawa daya stairs din yayi xuwan dakin da Mom take asalam Mom barka da safiya cewan yazid wa alaika salaam son barkan kade cikin farin ciki ta amsa saboda shigan sa taga yayi masa kyau ba kaman ko yausheba saboda yakara girma da kyau son kayi kyau yawwa daddy n ka yace nagayamaka yanason magana dakai ok Mom innadawo zamuyi magana yanxu inason naje court ne ok Allah yabada sa a Neehal ce da Neehla suka shigo shigo cikin dakin Mom a guje suna kaman zasuyi fada Mom kigaya ma Neehal ta dena… tsaya tayi da abinda zatace ganin yazid a tsaye juyawa zatayi da gudu ta koma inda tafito taku daya yayi ya cafkota ina zakije zoki karasa magananki dama Neehila tariga ta shigo har ta isa inda Mom ke shiyasa batayi yinkurin guduba sorry ya yazid Mom Mom takama kame kame saboda tasan halin yayan nasu yanada sauki tawani gefen amma tawani gefen bashida dadi shiyasa duk abinda sukeyi indai sunga yazid to zasu daina kee zonan cikin daga murya wani iskanci ne kuke ma mutani a gida yaya kayi hkri baza mu sake ba karyo kukeyi yau sakun gayamin kuka suka farayi ganin haka Mom tace kuyi shiru son meyasa kk ma kannin ka haka Mom basajine kibari nashiga jikinsu da belt ko zasuyi hankali jin haka suka kara sa kuka nace kuyi shiru baxe muku komaiba ba gani a kusa dakuba to Mom munyi shiru yawwa twins na son suci darajata ok Mom amma inkuka sake kunsan sauran in sha Allah yaya a tare suka hada baki kum sake fada ba kuma sake saina 6alla yarinya good morning yaya morning.

Good morning mom morning ya fada atare sukayi dariya mujenku dining muyi breakfast atare suka suka isa anjere komai na breakfast akai sunkae minti 15 kafin yazid ya mike Mom na huce a dawo lafiya son Allah yakai ka lafiya ya tsaremin kae da sharrin abin hallitta Ameen Mom I proud of you thank you ya huce.

Baby na na am mommy ina zuwa naga kinsha makeup kinyi kyau mommy zanje gidan Mom ne gurin yazid ok a dawo lafiya to Mom yau mommy nki larai zataxo zamufita muje wani guri da ita ok mommy yaushe zata xo yanxu haka ma tana hanya ko zaki xauna ku gaisa saiki huce to mommy bamatsala na kwana biyu ma banganta amma tunda tana hanya zanjirata mu gaisa salamu alaikum atare suka jiyo ganin Hajiya larai mommy tacika da farin ciki wa alaiki salaam yanzu muke magananki da baby Nadiya good morning mommy cewan Nadiya morning daughter ykk lafiya naganki kaman kina shirin fitane ma eh wlh mommy gidansu barrister yazid zanje to yayi kyau mommy na huce ok doughter adawo lfy.

Haka ta kammala takae mata daki ko kashi bata bataba ta cinye sai maganan banxa da ta gaya mata gaskiya Zahra baki iya girkiba kikara koya dawani ne a fuska zai watsa miki Kiyi hkri zan gyara karma ki gyara 6ace min da gani tashi tayi sum sum ta huce zuwa inda ummanta take (wannan shine ga Mari ga tsinka jaka Allah kamana me kyau injini.)

Sannu umma ya jikin naki Zahra ta ke zance miki sannu da gajiya aa umma ae inda sabo nasaba kefa bakida lafiya dun da haka Zahra.

Zahra “ba abinda zance miki saida nace kika ra hakuri da turai da zainab nima mahaifiyarki lokacin danake da lafiya kullun da kalan makirci da bakaken maganganun dateke jifana dashi.

Zahra inaji ajikina bazan iya tashi daga wannan ciwo ba shine ajalina amma inaso nabaki wani labari a game da rayuwarki da na gidan nan sbd ko bayan bana raye kisan kalan zaman dazakiyi dasu.

“Aisha ummah kwana biyu banga Zahra ba lafiya kuwa?”
‘To nima abinda Zan tambayeki Keenan bana ganinta ko kuma haduwa a makarantane aa um.”

Bookmark
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Barrister 2Barrister 4 >>

Drop a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.