Skip to content
Part 4 of 7 in the Series Barrister by Maryam Ibrahim

Zahra duk inda rayuwa taxo miki ki dauketa a haka ban yarda Kiyi koda canjin yaune da yan uwanki saboda ko ba komai sudin jininki ne Kiyi musu biyayya kafin nan zanmiki nasiha ko bayan raina duk mijin da ya aure Zahra Kiyi masa biyayya kidauki kamar ni fiye ma da haka saboda shine gatanki karki yadda koda canjin yaune Kiyi dashi kisani cewa aljarnarki na kafar sa ya”ta nasanki dabin nagaba dake kicigaba dayi wata rana zaki ji dad.

In sha Allah ummah ta zanyi duk iya kokarina dan ganin nayi yadda kkce fiye ma da haka

Masha Allah. Allah yabaki iko amma Dan Allah ummah kidena cewa zaki mutu da yardan Allah zaki tashi daga wannan ciwon
Fatima kikama mutuncinki saboda shine darajar kowace ya” duk rintsi duk wuya karki bari wani abin duniya ya rude ki kije kibada mutuncinki kowace yar kirki tanaso takai budurcinta gidan mijin ta tunda tafara mata wannan magana gabadaya kunya ya lulubeta

Hmm Zahra kenan akwai ki da kunya wannan magana tsakani na dake ne amma kina jin kunya haka zaki ringa yi idan kinyi aure sake sunkuyar dakae tayi kasa hmm fatima kenan Allah ya baki miji nagari tayi shiru bakice Ameen ba sai tace ameen ko kefa adua na miki ummah na,am Allah yabaki lafiya Ameen
*****
Larai yanxu ina muka nufa zamuje wani kauye ne dake akwai wani malami shi aikin shi kaman yankan wuka yake matsalan biyu na farko kudi na biyu in yabaka magani kar ka tsallake aikin da yace ayi in ba haka to abin zai dawo kan wanda yayi ko kuma duk gurin wanda mukaje ya bamu bazaiyi tasiri akan wanda aka mishi ko za a mishiba mude kawai mubi yanda yace ok to tashi mu huce kinsan gobe daddy n babyna zaidawo in yadawo kinga sai musan yadda zamuyi su amince ayi auren cikin kankanin lokaci ok hakama shawarace ai muje sauka sukayi daga saman stairs din harsuka karaso fallon kas


Tsayawa sukayi saboda mommy tace taman ta kudi komawa tayi ta dauko rafan dubu dubu guda hudu ta saka a jaka suka huce daman cikin jakan akwai wasu kudi masu yawa a ciki fita sukayi xuwa parking space suka shiga daya daga cikin moton dake jere a gurin ciki harda moton larai da direbanta yakawota shi yashiga yajasu zuwa kauyen argungu.

A hanya sukace ya ijiyesu haka akayi suka karasa xuwa da kafa cikin wani buka suka shiga ba abinda ke tashi a gurin banda wari boka munxo ne akan maganan….. Kudakata tunkafin kikaraso aka sanar mana yarinyan ki kikeso ta auri yaron aminin mijinki eh hakane dasauri suka fada mamakine yakama Hajiya saratu saboda ita bata ta6a xuwaba saide tasa larai taje yakaremin6o mata amma wannan karo saita ce sutafi tare shine suka shirya sukazo.

Wasu abubuwa yabasu ya fada musu yanda zasuyi dashi suka kar6a suna gdy suka juye mishi kudi masu yawa wanda nima bansan yawansuba kucire takalmin ku tafi karkusa har saikunyi nisa da nan haka akayi sanda suka yi tafiya me nisa suka sa suka karasa wajen dasuka ijiye direba suka shiga yajasu sai gida

*****
Tunda ya isa suka shiga courtu Dan gabatar da shari a akan wata yarinya da aka mata fyade wani dan alhaji suka basu da karfi sosai suna son sukwota yan su mutuncine shikuma yazid yayi musu alkawarin saiya taimaka musu zai tsaya musu a matsayin lauyan da yake kare hakkin duk wanda aka zalinta anyi shari a sosai in da aka gurfanar da wanda yayi mata fyade anyanke mishi hukuncin zama a gidan yari na shekara 1 da rabi kuma za a buga shi a jarida mahaifinshi ba abin da yake tunani illah 6ata mishi suna da za ayi sbd shi dan siyasane duk yanda zaiyi yayi amma ya gagara haka ya hakura yabar ma Allah komai dan kuka meja wa uwansa zaki.

Mahaifin yarinyan sunyi gdy sosai da barrister yazid ba abinda zamuce maka sai gdy

*****
Zahra lokacin dana aure mahaifinki ya tsana nin sona na tare a gidan ko wata biyu banyi ba matar shi tasani a gaba dayake mahaifinku ba me zama bane a gida shiyasa yana fita tayi tazagina nikuma bana kula saitace wato na manna mata hauka Keenan bana ce mata komai amma saboda makirci irin nata yana dawowa zata je takaran ta mishi karya da gaskiya tun baya kamawa harya fara kamawa abin kullun gaba gaba yake inta gaya mishi baze tsaya yayi bincikeba saiya hauni da masifa nikuma nayi tabashi hkri ana haka lokacin tana da yarinyan ta daya wato zainab tanada shekara 4 nasamu cikin ki a wannan lokacine mahaifinki ya dage dabani kulawa duk wani makirci dazata gaya mishi ya dena daukawa. Abin ya bata haushi sosae kwatsam wata rana yadawo gida sai naganshi bayadda nasaba ganin shiba.

“Malam yana ganka haka lafiya kuwa?”

Kawai saya faramin sababi banan yake shigaba banan yake fita ba masifa kamar zai dakeni saina barshi nashiga daki sbd banason ko canjin yau nayi dashi.

Bayan wasu kwanaki tsakani da mahaifin ki da turai kullun sai hantara a haka har cikina ya girma yakae wata ta tara da wasu kwanaki na haifeki wata rana yayi kamar bashi ba rana suna kikaci sunan kanwata Fatima haka rayuwa tacigaba tunda na haife ki bansake ko yin 6are ba turai tasake haifan yarinyan ta na mace shikenan turai tashiga tafita dan ganin ta rabani da malam amma hakan yaki yiwu wa saita samishi tsanata daga baya ta turamin ciwon kafa amma ni banyi imani da hakan ba nasan komai yasa meni daga Allah ne.

*****

Zahra ke kadai Allah yabani nasani kina da tarbiya to ko bayan Raina ki rake maraicinki turai makirrar mata ce Allah ya miki albarka Ameen ummata kina gani yanxu babanku zai shigo gida kaman bashiba anjima inyafara bamai tare kisamu kirabu da mahaifinki lafiya in sha Allah ummah zanyi duk yan da kkce amma kidena cewa zaki tafi kibarni bani da kowa saike se abba kuma be damu damuba sai yar uwanki umma fatima kuma basa shiri da Abba karkidamu Zahra ko ba na nan akwai Allah a lokacin damuke rayuwa da dangina cikin jin dadi da kaunar juna amma kwatsam wata rana na rasa gaba daya nida yar uwa ta fatima ce muka tsira da kyar bagashi mun rayuba hakane kawai se hawaye ba kakatauwa.

*****
Yazid be dawo gida ba sai waje jen karfe 1:00 na rana yana yin parking ya huce cikin fallo Neehal ce da Neehila suke zaune suna kallo sai neehila ta dauka remote ta chanja tasha wai ita bazasu su kalla india ba saboda suna iskanci wani program ne akasa a wannan tashan kuma suna kiss da saurayinta shiya sa Neehila tace baza su kalla ba ita kuma Neehal tanaso kwace remote tayi ta mayar itama ta fizge fada suka fara yi sai Neehila tace yaya na dawowa saina gaya mishi yanxu kije kigaya mishi inbaki fada ba nikuma sai na dau mataki akanki duk abin da sukeyi yana jinsu kuma yana kallonsu saboda basusan shigowansa.  Wani suket ya cire y afara ya tako inda suke basu san dashiba kawai se suka ganshi a gabansu kuka duka suka fara Dan Allah yaya kayi hakuri bazamu sake ba dazuma haka kukace wai meke damunku babu duka suka fada atare mussamman ke Neehal fada ya musu sosae kuma yabasu punishment nikuwa nace kaman wani soja tsallen kwado yasasu ya zauna akan super kushine yana kallonsu har sunyi gumi Neehila ce yace tabari tazauna ita kuma Neehal taci gaba.

Sanda takai so biyu yace ta tashi in nasake ganin ku kuna kallon irin wanna Film din saina karya ku shiyasa ke Neehal nabarki kk cigaba saboda kene saikuma yayi shiru yabarsu ya haura sama watsa ruwa yayi. ya yi alwala ya fito ya yahuce masallaci daya da minti arba in yadawo madara yasha ya huce dining yasamu su Mom da daddy n da kaninsa suna jiransa dan gabatar da lunch son kadawo lafiya.

Sannu da gida Mom daddy barka da rana.

Barka sannunka da samin yara pushiment son banaso Mom a barsu kenan suna fada kullun aa amma ae da zanesu kayi shikenan Mom yi hakuri kaine da hakuri shikenan abar maganan cewan Dad abinci suka Fara ci kala kala wanda masu aiki suka girka shi yazid yana ci ne kawai amma beson cin abinci yan aeki

*****
Nadiya tunda tabar gida tace wa mommy nta zata je gidan su yazid ba hurin ta huce ba gurin wata kawarta meenat taje suna ta holewarsu akan insun gama saita huce gidansu yazid in gskya besty kina hutawarki cewan meenat dukansu suka tu6e tsirara aihuwar uwarsu sunata kwakulan juna rufe musu kofa nayi nadawo waje na zauna sunkai awa 2 kafin suka rabu da juna suka meenat ma takasance wata yar alajine tun suna yara suke kawance har yanxu

*****
Ummah zanje gidansu su Zahra na duba ta kinsan ummanta ba lafiya ko jikintane ya tashi aa bana raba dayan biyu ko wancan bakar makiran ne tahanata fita ko jikin ummanta to ummah hakane bari naje to adawo lfy tashi tayi tahuce gaba daya jikinta yayi sanyi haka kawai
*****
Sallama? Wa alaiki salaam tareda da juyawa danganin wacce laa ummah kene nice Takwara ta sannu da zuwa sannunki yajinki ummantaki da sau..bata gama bata amsaba taga ummanta tana tari ba kakautawa a daidai lokacin Aisha ta shigo ummah ummah kar6a ruwa kisha kawai saisuga ta sume dasauri ummah Fatima ta suka kamata suka fita waje niman me a daidaita yakaisu asibiti —– suna fita sukayi sa a subiyu suka shiga ita da ummah Zahra da Aisha suka tare wani adaidaita suka shiga Aisha ce tabiya kudin naira 100 dakyar ma ya kar6a suka huce suna isa a kashiga da ita ciki dan bata taimakon gaggawa.

*****
Nadiya ce tashigo bakinta dauke da sallama kaman mutuniyar kwarai amsawa sukayi barka da rana da dad ya amsa Mom ma haka karaso kixauna karasawa tayi tazauna kusa da yazid a haka suka kammala yazid ne yafara tashi sai Dad da twins son inkagama anjima akwai maganan danake muyi dakai ok Dad bamatsala
Nadiya bata bar gidan ba sai wajan karfe 5:00 ta huce sunyi hira da Mom sama sama inda Mom ke tambayanta ta girma yaushe zatayi aure take cemata sai lokacin da yazid ya shirya Mom tagane son yazid takeyi amma ba sosai kuma ita gsky bazata iya hada jinin ta da saratu ba saboda bata da kirki ga izzah ga nuna tafi Kowa haka itama Nadiya halin uwanta ta gada ita a tsarin Mom tanaso yaronta ya auri yar gidan mutunci me tarbiya wacce tasan yakamata komin yaya take inde tanada halin me kyau zatayi maraba da ita.

Karfe 7:00

Yazid yake zaune shida Dad suna magana—– yazid Ka girma ka mallake hankalin kanka yakamata ace yanxu kanada iyali kobaka sone naga jikane aa dad bahaka bane kawai de kasan aure lokacine ni gsky ba aure a tsari na saboda banga yarinyan datamin na aura ba Nadiya fa aa dad nibazan auretaba son kasan tanasonka eh Dad amma duk da haka ni bazan aureta kaima kasan wacece ita bata kirki to shikenan zan nima maka wacce ta dace na Aura maka.

Aa dad ba yanzuba shikenan Allah yakaimu lokaci a haka suka karasa magana inda yake ce mishi gobe zaije wani kauye duba marasa lafiya da suke asibiti ya taimaka musu da marasa karfi dama haka yakeyi duk karshen yana xuwa ok Dad adawo lafiya
Good night safe journey
Nima nace good night

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Barrister 3Barrister 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×