Skip to content
Part 5 of 7 in the Series Barrister by Maryam Ibrahim

Zama sukayi a gujen da ake jiran fitowan marasa lafiya dukkan su sunyi tagumi suna jiran ikon Allah.

Zahra kan sai kuka takeyi kasa kasa. Sai bayan hour biyu wani likita ya fito daga cikin dakin da aka shiga da ita.

Likita cewan ummah Fatima yajuyo ba tare da yace mata kalaba likita me yasa me yar uwata Dan Allah ka gaya mana cewon ta ne yatashi kuma gsky sai anyi mata aeki a meyasa kuka barta takae wannan lokaci baku kawota asibiti ba likita bamu da kudin daza ayi mata aekina shiyasa ok to gsky yanxu yakamata kuna nema don amata aiki be jira amsantaba yahuce zaman dirshan tayi Zahra kuwa ko magana takasa yi sai zuciyarta dayake mata suya Aisha ma kuka takeyi can bayan wasu mintoti Aisha takira ummanta ta sanar da ita halin da umman Zahra take tace itama zata zo ta duba jikinta amma saida safe saboda dare yayi.

*****
Washe gari Dad da safe sukayi breakfast ya shirya zuwa asibiti wato kauyen maduko shima yazid akwae aikin da zaiyi a ta hurin amma be sanar da Dad
Sanda Dad yatafi da minti 45 kafin yazid ya shirya dan zuwa nashi aikin a kauyen maduko be dauki wani lokaciba yafito ya sallame Mom ya huce.

*****
To yanxu ya za ayi kenan gashi likita yace har inba a yi mata aiki ba zata iya rasa ranta cewan Mom ga mahaifinki ma Zahra har yanxu shiru yace ankira tunda yaxo ya ganta so daya yakoma be dawoba nakirashi namishi bayani yace bashida da kudi yama kashe wayansa baki daya kawai sai ta fashe da kuka.

Sunkai awa daya kafin Umma Fatima tace mata ga 200 kije ki hau adai daita 50 sai kisiyo kunu da kosai kikawo musamu koza ta danci abinci kema kici toh umma ta kar6a Aisha tace zataje gida taxo da wani kaya ok diyata mungode ai adawo lfy batare suka tafi da Zahra ba.

Tafiya Zahra takeyi har yanxu bata samu abin hawa kawai sai tacigaba da tafiya tafiya takeyi bata kallon gabanta sai mata horn akeyi amma shiru ta tafi duniyar tunani fita yayi a cikin moton yana ganin yarinya karama yana mata horn taki ta matsa shikuma yana sauri saboda ankirashi kan cewa karya huce 30 minutes yakaraso itakuma wannan tana tafiyan takama kilan yabige kawai saitaji anjawo mata hijab har yana yagewa ya wanke ta da lafiyayyun Mari Tass tass guda biyu ranta ne yayi matukar 6aci duk da ita yarinyace bame son hayaniya amma be kamata ya yaga mata hijab ba gsky bazan bar wanna mutun yahuce ba saina mishi abinda zai 6ata mishi rai daga ganin shi besan mutuncin dan Adam kawai saiya mare ni me nayi masa duka a zuciyanta take magana kee jaga bani hanya na huce inada abinyi ko bakijibane saena kara miki
Eh banjiba ina jiranka kaxo kakarimin dayake kae baka san mutuncin dan Adam ba daga ganinka badaga gidan mutunci ka fitoba yaka mata ka koma asake maka tarbiya daga ganin ma Dan iskane kwartone inba iskanci ba me zaisa ka yagamin hijab kuma Allah ya isa tsakanina dakai Marin da kamin da yagamin hijab da kayi Allah zai sakamin kuma idan kana ganin ka kaiwa ni ne akwai wanda suka fika kudi macuci Dan iska azzalumi yazid kuwa tunda tafara suman tsaye yayi yana kallon yana jinta be cemata komaiba mamaki yakeyi wannan yar yarinyan ce take gayamishi wanna bakaken maganganu to shi besanma ya yagamata hijab ba amma ko ina kwartonci mezanyi da wanna kazaman yarinyan lallai duk randa muka sake haduwa da wanna yarinya saina koya mata hankali saina nunamata na fita iya kwartonci lokacin da yakamata yaje har ya huce saboda wanna yarinya yayi asarar aikin duk abinda yake aiki Akai tsawon kwana uku ya tashi banza haka ya juya ya koma gida da dacin rai sbd ba abinda zai iya aikatawa yau.


Zahra kuwa tunda tasa kai ko juyo wa batayiba tafiya take tana mgn zuci shiyasa umma takecemin na kula da mutuncina saboda irin wa enan 6ata gari ita harga Allah ta dauka jan ta zaeyi yasa a moto ya6ata mata rayuwa shiyasa ita kuma mishi haka.

*****
Bangaren Dad kuwa sanda yaje wani asibitin yayi duk taimakon da yasaba kafin yajuyo zauwa wannan asibitin yana cikin zuwa motonshi ya samu matsala karfe cikin moton yayi zafi sai an xuba mishi ruwa gashi kuma motonsa ba ruwa.

Zahra ce take zuwa da Karamin bokitin kunu akanta yarinyata taji ankirata da haka na am baba Dan Allah kitaimakeni da ruwan kanki na watsa acikin motata ayya Baba ba ruwa bane a ciki kunu ne amma Bari na je wancan bohol na dibo maka ok nagode aa Baba kadaina gdy ai yiwa kaine nima bazanso mahaifina ya nima taimako a wani guri akasa masa ba aikaga bazan ji dadi tunda tafara magana yaji takwanta masa a rai irin yarinyan dazata dace Keenan da barrister yazid na inaga zan nimawa dana auren wanna yarinya na yaba da komai nata.

*****

Baba garun cewan Zahra kar6a yayi ya xuba a moton ya”ta Nagode Allah yasaka da alkairi murmushi tayi mishi ina zakije daganan ya jefo mata tambaya zanje asibiti ok muje inkarasa dake aa nagode zan karasa dakaina aiba nisa yayi tashiga ya rage mata hanya taki ya jinji na tarbiyan yarinyan huce yayi itama takara sa tana shiga taga abbanta da turai ina kwana abba lfy ya amsa mata ciki ciki ina kwana umma itama ta amsa can kasan zuciya ke Zahra ina kika tsaya tundazu aka aekeki ina zuwa nan ban gankiba tundaxu kintsaya kina shashan cin da kk saba ko aa abba kayi hakuri na tsaya duba ma umma Kayan dazata sane intayi wanka wayace miki zata sake kwana to yanxuma gida zamuje dan banda kudin dazan biya na jinya ko sisi ok abba ta amsa zuciyanta na mata kuna umma Fatima ta mike take cewa baza mutafi yauba tunda ba kae ka kawomuba kuma bama bukatan kudin ka ae bakai kadai bane kk da hakki a kanta ni yar uwanta baza jura ganin ta hakaba koda zan rasa komai na zanyi wa yar uwa ta jinya kar ka manta kobani ba akwae na Allah Fatima ni kk gaya ma haka na gayamaka cutar da yar uwa da yar da ta haifa da kkyi shekara da shekaru to ya isheka da kae da wanna makiran matan ka kuka zamar da yar ta kamar baiwa to yau komae yazo karshe karya kikeyi Aisha mata tace kuma dole nayi yadda na keso batun ya kuma ba baiwar da muka zamar da ita kae saide ka gaya ma wanda be sani
Umma Dan Allah Kiyi hkri Kubari kinga ummata bazata ji dadiba inta farka da ganku haka ta tsuguna akasa tana bama umma Fatima da abba hakuri tashi takwarata komae ya huce kinga yar Albarka ko cewan Abba yana so ya shashe duk abin da sukeyi Dad yana kallon shi yana jin wani abunda suke cewa wani kuma be jii saboda yana dan nesa da inda suke.

Kama hannun Zahra abbanta yayi zomu huce ina zaka je da ita ya”tace baki isa ki hanani iko da ita zainab da shigowanta Keenan yayi dai dai da Kama hannun Zahra da Abba yayi ta tsaya Aisha karasowanta kenan ita da ummanta kama hannun Zahra umma Fatima tayi tana cewa babu inda zakaje da ita dan haka inaso kasani ga kafata gana Zahra bakaeba Dan haka kasake mata hannu karya kkyi nice mahaifinta Dan haka nizanyi iko da ita
***
Mommy yanxu wanna ya zanyi dashi cewan Nadiya wanka zakiyi dashi kifesa turaren ajinki inkinje inda zaku hadu da yazid yakansace kina fesa shine zai shake Kamshi kafin wanni kuma karkibar kowa yaga lokacin dazaki fesa to zaran kin sa yaji Kamshi bazai ta6a iya yin komae sai abinda kikace kuma bawata ya” dazai Aura a duniya in ba keba kinriga kin mallakeshi ok mommy zanyi duk yanda kikace indai zan mallake yazid ne to shikenan.

Kudi mommy ta dibo masu yawa tabata ga wanna babyna kisa mae thank you mommy yawwa mommy gobe akwae birthday na amina dazamuyi ok to bamatsala kudi kamar nawa kike da bukata mommy only 2m ya isa ok bakida wani problem daddy sannu da dawowa cewan Nadiya da ta kalleshi yana karasowa saboda bata san da zuwan barkanki baby na naji kuna tattaunawa akan wani magana kirjin mommy yayi rass rass wani Magna daddy n Nadiya cewan mommy da wani irin sauri naji kuna cewa gobe birthday na Amina ok cewan mommy hartaji sanyi ta dauka yaji maganan dasukayi ne Nadiya haka ta 6angarenta eh daddy na mantane bangaya maka ba am sorry okay baby na karkidamu nima zanbaki 1m kuyi hidima thanks daddy Allah yakara arziki
*****
Yazid kwance akan daya daga cikin super na dakin yana tunanin maganganun da yarinyan nan taga ya mishi Dan iska kwarto azzalumi maganganun dasuke ta mishi yawo Keenan akae shi babu yarinyan da yata6a koda ta6ama hannunta da niyan iskan ci ko wani abu kuma babu wacce ta ta6a tsayawa tagaya mishi magana irin wanna yarinyan amma duk randa muka sake haduwa da ita saita gane cewa nita zaga saina mata abunda bazata sake zagin kowani bane sake sake yake tayi kala kala a zuciyarshi
*****
Neehal ce da mom zaune a fallow suna firan su mom naga yaya yadawo kaman ranshi a 6ace nima haka nagani cewan niheela da yanxu shigowanta ok ina zuwa Bari na dubashi ina xuwa ok Mom wata yar aikice takaraso zata kae mishi coffee saitaga Mom na haurawa kan stairs ta tsaya tabata hanya ta huce dama shi yazid indai yana gida to yanashan coffee shiyasa ya” aikin gidan suma suka saba to yanxuma shiyace a kawo masa
*****
Kasake mata hannu Dan nayi alkawarin bazan barta katafi da ita ba Kiyi hkri FATEMA shidin mahaifintane amma kaima malam Kabarta kaga mahaifiyarta ba lafiya zata tayata wasu ayyukan kuma zata so ta farka taga ya”nta kusa da ita cewan Umman Aisha.

Nidama auran da ya”ta zanyi sadaka duk wanda ya min kuma a yanxu zanje koma waye zan Aura mata Aisha ce da Zahra suka kama kuka dukansu duk da basu gama sanin menene aureba amma sunsan inka tafi to shikenan kabar gidan iyayenka saidai kazo kana gaishesu shima ba ko yausheba Dan Allah Abba kayi hakuri karka rabani da ummanta wlh bazan iya tafiya inbar taba.

Wani irin dadi Zainab da turai suka ji jincewa za a bada sadaka da Zahra da duk wanda yaga dama Dad ne yakaraso jin maganan da sukeyi beji dadiba kaman wanna yarinyan ace za a mata auren dole nizan Aura ma dana ita inka amince.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Barrister 4Barrister 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×