Juya wa sukayi suna kallon Dad amma meyasa kk son Aura danka ita cewan abban Zahra zan maka bayani nidae kawai inason dana ya aureta ok bamatsala yanxu kuwa shirya sukayi direct suka huce masallaci aka liman da sauran mutani aka daura aure akan sadaki naira dubu hamsim aka shafa adu,a Dad yaciro kudi masu yawa yaba abba asaya ma mara lfy magani ok Ngd shikan abba gaba takaishi shiba ruwan shi koma ina ne yaje da ita ba bincike ba komai Allah ka shirya.
Sun iso asibiti inda abba ya sheda masu andaura aure sai fatan alkaeri Aisha da Zahra kam kuka sukeyi sbd suna tunanin zasu rabu batasan inda kuma za akai mata Zahra ba
Mama ne dake kwance ta mike tazauna da kyar takamo Zahra tana mata nasiha sosae akan aure yadda zata kula da mijinta da masa biyayya sbd aljarnarki na kafansa takae minti shabiyar tana mata kafin daga bisani ta saketa itama umma Fatima da Umman Aisha nasiha suka mata me ratsa zuciya Umman zainab kuwa banda harara da hausa ba abinda takeyi ayide mugani kwana biyu za a korota ba wanda yakaleta bare yace mata cikanki
Umma Fatima ne tafito haraban asibiti tasame Dad yawwa dama nace kozaka Bari zuwa wani sati a tare ok ba damuwa Ngd amma yarinyan kawai za a kawo nizan mata Kayan daki da sauran duk abinda ake bukata shima mijintan zaizo ya ganta kafin tare ok to address din inda take tabashi kudi yaciro ya mika mata masu yawwa taki kar6a da kyar dai takar6a gdy tayi ta masa sosae da fatan alkaeri ta huce ciki tasami yar uwanta da maganan Zahra zata zauna a hurinta kafin tarewan ta shikenan badamuwa umman Aisha ce tace Aisha zata cigaba da kula dake kamar yadda Zahra take sbd yanxu yakamata ace anfara gyara zahra kuma bazata ringa fitowaba hakadai Suka tattauna
Bayan Dad yakoma gida yasanar da Mom abinda sukayi harda auren dayama yazid taji dadi sosai tanuna farin cikinta anjima zanyi Magna da yazid saimu sanar mishi “ok”cewan Mom
Yanxu komai yakammala zamu iya zuwa da ita gida sbd yanxu Zahra tazama ya”ta sosai ummanta taji dadi ya”ta muje ko cewan Dad yana tafiya juyawa tayi tana kallon mahaifiyarta saita fashe da matsanancin kuka Allah yabaki lfy umma jinjina kai tayi sbd ita kukan ne Ke kokarin cinta Aisha kam tuni hawaye Ya wanke mata fuska umman Aisha a 6angarenta haka yakasance da ummah Fatima Dad ne yajuyo yake cewa nayi alkawarin zan fita da mahaifiyar ki kasar Germany ayi mata jinya gdy muke alhaji ae yiwa kaine ina matukar godiya da jin dadin sama wa dana wanna diya fata na shine Allah yabaki lfy ana hk suka fice sai gida.
*****
Suna zuwa mai gadi ya bude musu get suka huce parking space bude mofin moto Dad yayi ya fice itama yabude mata tsoro ne yakamata da ganin irin kyau da tsaruwan da gidan yayi Dad yajuya yaganta sai yace ya”ta mutafi ko dawowa tayi daga duniyar tunanin da ta shiga da to amsa yana tafiya tana binshi a baya a darare tafiya sukeyi har suka isa falow Neehal ce da neehila suke zaune a palow suka ga Dad da Zahra gaishe sa suka farayi barka da rana ya amsa musu cikin kyakyawan murmushi da ya saba musu dad wanna wacece batare da komai ba yabasu amsa ataikaice matar yayanku ne cikin murna duka suka rungumeta suna sake ma juna murmushi mukarasa ciki tusamu ta huta ok Dad itakan Zahra da ido take binsu
*****
Nadiya ce tafito cikin wani shiri saikace ba yar musulma ba tana tafiya tana karya jiki mommy xan huce daga gurin zan bi ta gidan Dad ok adawo lfy babyna
Cikin farin ciki take tafiya har ta iso parking space daya daga cikin motocin ta dauka tashiga key tasa megadi ya wangame mata get da gudu taja gudu takeyi sosae a kan kwalta motoci sai bata hanya sukeyi saboda Sun san moton Nadiya sun san wacece ita wani arniyan motone kiran Dubai yatsaya a daidai hanya matashin saurayine me ji da kansa mahaifinsa shahararen mai arziki iya yansa sun san gartar dashi shiyasa be dauke kowa abakin komai baka isa kanuna mishi yatsaba sai ya kusa karyawa Nadiya takaraso wurin takai 5 minutes be huce ba yana tsaye ranta ne ya fara 6aci tafito a hasale don ganin wani mara san zaman lfy ne tana iso wa ta kwankwasa gilas aka bude mata masifa da zagi tafara yi kafin daga bisani tace ina mai baka shawara da kayi gaggawan bani hanya na huce kafin na dau mumunan mataki fitowa yayi daga cikin moton ya tsaya ok bazaka ban hanya ba kenan cewan Nadiya daga mata kai yayi daga hannayenta tayi tazuba masa lafiyayun maruka guda 2 Tass tass ina mai baka shawaran kayi saurin 6ace min da gani mamakine yakamasa tunda yake babu wanda yata6a Marin sa sai wanna yarinya lallai zai dauka mumunan mataki akanta wanda sai tayi dan da tasanin Marin sa direban sane yamasa. mgn yabata hanya haka akayi ka ceci kanka tana hucewa yama direbansa mgn karinka bin bayanta ok
*****
Bangaren zahra tun da ta zo takasa sake jikinta lunch ne aka hada shirya Dad da Mom suka zauna sai Neehal da neehila a guri daya Zahra ta raku6e a gefe guda tana wasa da yatsunta dad ne yasa akira yazid Neehal ce tace dad neehila taje kafata na buga yanxu ok neehila je fuska ta kwa6a sbd tasan halin yazid shiyasa basa son zuwa da kyar ta yarda taje haurawa stairs tayi tatsaya abakin kofan dakin sallama tafara shiru kawai sai tashiga ciki barka da rana yaya daga mt kai yayi an shirya lunch kai ake jira ok.
Fita tayi tadawo yakai 5 minutes kafin ya sauko yana taka stairs din ďaya bayan ďaya zama yayi cikin daya daga cikin chairs din Zahra dake raku6e taji kamshin Turare amma ta manta inda ta ta6a jii barka dad &Mom ta tsinkayo muryansa still bata ďaga kai takale shiba amma ta ta6ajin wanna murya a wani guri kai bazai kasan ce shibane sbd wancan bashida kirki nan gidan kuma suna da karamcii da kirki muryan dad ne yadawo da ita daga tunanin zucin da takeyi ya”ta kici mana ta daga masa kae alaman ok yazid ne ya ďaga kae dan ganin wata Yarinyace dad kemata mgn yana daga ido…
*****
Daga idanun sa yazuba mata sai yaji wani irin tsananta ya karu a cikin zuciyansa lallai yarinyan nan to me ya kawo ta cikin gidan su koma meye yasa mu daman da zai hukun ta-ta.
Ďaga kai Zahra tayi suka haďa ido wani irin kallo suka watsa ma juna cikin zuciyan ta kuwa tana cewa mugu azzalumi”
Yazid kuwa tambayoyi ne sosai a cikin zuciyan shi idan kuwa aiki tazo yi zaisa a dawo da ita part nasa da zama a dumin ya ladabtar da ita”
“Yazid idan ka kammala zamuyi mgn dakai”
cewan Dad ok yabashi amsa a takaice
*****
Bangaren Nadiya kuwa tafiyar ta takeyi har ta isa gidan su meenat shiga tayi me gadi ya wangale mata get tana yin parking ta shige ciki da mommy n meenat taci karo a pallo gaisheta tayi ta amsa cikin fara a “tana ciki mutuniyar ki ok stairs ta hau ta shiga ďaya daga cikin ďakin dake jere guda biyu a makeken gadon ta taganta tana ganin ta tamike ta rungumeta besty kamar kinsan ke nake jira” hmm cewan Nadiya nima a matse nake wlh ok kulle daki sukayi dama meenat daga ita sai shimi da wando 3 quarter kissing na juna suka fara kaman ma yunwa tan zaki (fita nayi naja musu kofa)
After 2 hours suka fito cikin fara a (Allah ya kyauta ka tsaremu baki ďaya masu yi Allah yasa sudaina)
*****
Bangaren su ummah suna asibiti likitoci suna ta kokari akanta saboda alhaji Muhammad yabada kudi sosai next week za a fita da ita akaita kasar German domin ayi mata jinya.”
*****
Abba dashi da su umman Zainab sun dawo gida bakin ciki ka kamar ya kasheta
Malam kenan ina kudin sadakin yarinyan?? nan yana nan!to kaje kasayo mana kaji da shinkafa da kwai muma yau muci daďi ita kuma yarinyan Allah yasa gidan yakan kai zaikaita kaga shikenan munrabu da k’aya” hakane uwarta kuma Allah yasa ta mutu da ciwo a gurin a cikin zuciyansa bejin daďin maganganunta amma kuma bazai iya musa mata komai ba saboda a yanxu duk abin da tace shine.
*****
Bayan sun kammala yin lunch Dad yace ma su Neehila da Neehal sukai Zahra dakin dake kusa dana Yazid ta watsa ruwa tasauko subata kaya da komai na bukata!toh suka amsa a tare haurawa sukayi suka shiga kamar yadda Dad ya umarce su hk sukayi har privacy suka kaita suka nuna mata komai da yadda zatayi amfani dashi Zahra kuwa tun da suka shiga komai suka nuna mata toh take cewa wanda bata gane yadda ake amfani dashi ta tambaye su mamakin irin kayan alaton dakin tayi komai na dakin rainbow color ne
fita sukayi suka barta ta kimtsa suka dawo pallow suna kallo watsa ruwa tayi _tayi wanka sosai ita kanta jin wani irin ni’ima take ji a jikinta isowa tayi dressing mirror ta shafa cream taďauko wani gown da suka ijiye mata tasa ta ta kalle kanta a jikin mirror tayi matukar kyau ďaukan hijab nata tayi ta mayar jikinta saukowa tayi zuwa pallow inda su Neehal suke itama ta zauna Dad ya ce in kin karasa mu samesa a dakin Mom ok muje
“Neehila ce ta ce aa malama ya kinyi wanka kika sake mayar da wanna hijab ki cire mana”
“Aa muje hk kawai”ok cewan Neehal “nima na so mata mgn gashi kinyi kyau sosai cirewa Neehila tayi tabata gyale ta rufa.
Wow Kîñga yanda kikayi kyau suna hk har suka shiga ciki bakinsu ďauke da sallama Mom da Dad ne suka amsa Yazid Chan kasan makoshi shima ya amsa.
“Yawwa da farko na taraku ne anan domin na faďa muku wanna yarinya wacece to batare da 6ata lokaci ba itace matar Yazid.”
Dasauri Yazid ya ďago idonsa “Dad ban fahimta ba wani yazid a ciki “
Barrister Yazid ďana dana haifa”
Dam-dam kirjinsa ke bugawa idanunsa sun janza kalla cikin mituna kaďan ya sauya.
Ruďewa ne da firgici suka kama Zahra bata ta6a tunanin shine mijin da aka aura mata ba,
Hawaye suka cika mata idanu acikin zuciyar tana tunanin wani irin zama ne zasuyi da shi
6angaren yazid sake_sake yakeyi a zuciyar wani irin hukunci zaiyi mata ya huce
“‘”Ya ta wanna shine mijinki fatan zaku zauna lfy” juyowa yayi kan Yazid.
“Son ga matar dana aura maka fatan zaka rik’e ta amana Allah y baku zaman lfy da zuri’a ďayaba.”
Mom ne ta amsa da Ameen”
Adu,a suka masu sosai da nisaha me kama zuciya
“Abuna karshe da nake faďa maka shine nabaka ďaya daga cikin Gidana aciki zaku zauna nasa ayi gyara-gyare saboda bazaku huce kwana uku a Gidan nan ba zaku tare a chan”
“Dad nagode Allah yakara maka budi ya ďauka kaka Ngd sosae “
Zahra kam tsoro da kunya ya hanata cewa komai
Mom ne ta jata jikin ta tana shafa bayanta kamar yadda take ma su Neehal da Neehila
“Gobe zaka dauka Zahra ka kaita shopping taza 6a kayan sawa da abubuwan buk’ata zaka tayata za6a kaima duk abinda ya dace saboda na sa a haďa mata lefe a Dubai to sai nan da 5 day’s zasu taho dashi zaka min transfer na kudin Kayan 2m” cewan Mom
Yazid da ranshi yagama 6aci ya amsa da to
Tashi yayi zai huce zuwa room nashi ya dauka key ya fita.
Hanyan da zaibi ya cikaro da Nadiya dake tsaye fuska sharkaf da hawaye.
“Yazid ka cuceni aure kaje kayi karasa wace zaka aura ma sai yar talaka da me tafini kyau ko arziki.”
Tunda tafara mgn yake sauraranta har takai aya
“Nadiya kinsan cewa bana sonki na tsaneki bazan iya auranki ba haka itama wancan Dad ya aura min ita batare da sanina ba,ni babu wata ya” dana keso a duniya aura ma bashi a cikin lissafina dan hk ina mai baki shawarar kifita a hanya na ita ma wace aka auramin ba daďewa zanyi da ita ba zan sallameta ta tafi ” juyawa yayi da nufin haurawa sama ya tsinkayo muryan Nadiya
“hmm wlh Yazid k’arya kakeyi kana sonta da baka sonta da ana gaya maka zaka sallameta kasani cewa kota halin k’ak’a saika rabu da ita ka aureni baka da wata mata a duniya face ni “
“ok”
cewan Yazid yakara sa haurawa saboda wani irin ciwo kansa ke masa, yana shiga room nashi ya faďa a fafaďan kadonsa ya lumshe ido.
6angaren Nadiya shiga tayi part ďin Mom dan taga wata irin kucaka yarinyane ya auro ;shiga tayi da sallama kamar mutuniyar kirki gaba ďayan su suka amsa wa alaiki salaam zama tayi kusa da Dad tafara gaishesu,
“Daughter kina lfy?”
“Lfy qlau Dad “
“ya mutanin gidan “
“suna lfy suna gaishe ku”
“Masha Allah muna amsawa “
har suna haďa baki da Mom
“Dad wanna wata bakuwa ce ta kwanta a jikin Mom “matar yayan kine Yazid ayya “dama yayi aureni Dad shine ba labari ko invite.”
“A’a ba haka bane auren bazata ne sai ranar tarewa za ayi invite da komai su tare a sabon gida “Nadiya ji tayi kamar an chaka. mata mashi a zuciya Allah sarki Allah y kaimu
“Ameen “
Zahra kuwa duk abin da sukeyi bata sani dan har tayi bacci.
Nadiya taso taga fuskar ta amma bata samu daman gani har tagaji ta mik’e Dad zan huce sai anjima ” mujima dayawa
Dad ma fita yayi zuwa wani guri moton Nadiya na fita shima yafita.
Mom ne ta tashi Zahra taje ďakin ta ta kwanta mikewa tayi saboda jikinta da yayi tsami na bacci tana tafiya har ta haura sama tsayawa tayi tafara tunani wani daki ne a ciki kawai sai ta shiga daya daga cikin ďaku nan ta kwanta a kasan capet wani baci ne ya tafi da ita………
*****
Sai wajen karfe 3:40 Yazid ya farka daga barci shiga privacy yayi alwala ya gabatar kafin ya fito Dan zuwa masallaci
Fita yayi falo dai dan in da take kwance be lura da ita ya taka mata yatsu
cikin barci taji wani raďaďi a hanun ta kara tasa sosai wanda be san lokacin da yaja baya ba sai de duk ihun da takeyi wanda ke waje bazai jita ba
“Dan Allah Kayi hkri karka ta6a ni ban san kai bane”
cikin razana da ganinsa akanta takeyin sababi Yazid kuwa mamaki ne yaka masa me yakawo ďakinsa har tayi barci! Me aka mata take wanna haukan
“lallai yaka mata na dauki mataki akan wanna yarinyan” cewan Yazid
Sake taka yatsun hanayenta yayi sosai har hanun sunyi ja tarasa yadda zatayi
Wani razanan nan kara yadaka mata idan kika sake tare saina karya Yatsun hanun baki daya
Yajuya yafita ya barta a gurin saboda kar jam i ya huceshi
*****
Bangaren su umman Zahra jinya ake yimata jikin ta na k’ara sauk’i yau saura 3 day’s a fita da ita tunda aka tafi da Zahra Aisha sai tazama wani iri kullun adu a take yi mata Allah y sa tana cikin koshin lfy,
Umman ta ma tana taya su uni a asibiti suna zaune ita da ummah Fatima suna hira sai aka kirata a waya ďaga wa tayi tasa a kunenta cikin murya me ban tausayi tayi salaam.
“Assalamu alaikum”
ta ďaya 6angaren aka amsa da
“wa alaiki salam”
muryan Dad ta tsinkayo
“barka da yamma alhaji”
“barkanki dai “ya jikin mara lfy”da sauk’i” Alhamdulilah”
Likita ya gaya muku cewa saura kwana uku zaku tafi ko”
Eh ya faďa mana mungode sosai Allah yasa maka da Gidan aljanna”
Sosai yaji dađin a du o’in ta
“Yawwa jibi za ayi tarewan yaran nan zan turo miki address na Gidan sai kuzo kuma ku gayyaci yan uwa da abokan arziki”
Allah y kaimu jibin in sha Allah zan gaya musu suzo “
“ok”
yakashe wayan
zama tayi ta sanar da su umman Aisha duk yadda sukayi da alhaji murna da farin ciki a gun Aisha kamar ace yau ne zata je taga inda Zahra nta take zama dukan su dai farin ciki sukeyi Aisha ce tace zata sanar da k’awayen su na makaranta da abokan arziki fita tayi daga cikin asibitin tace ma ummanta zataje ta dawo
Allah y tsare suka yi mata
*****
Bangaren Nadiya da wani irin gudu taja moton ta sai gida duk inda tayi moton nan yana biye da ita har ta shiga me gadi ya wangale mata get a parking space ta ijiye da sauri sauri ta huce cikin tana isa tafaďa a jikin mommy nta tasake wani marayan kuka me tsuma zuciya
“Babyna me ya faru kike kuka waya ta6amin ke wani marasan zaman lfy ne”cewan mommynta.
“komai ya faru mommy” faďan min to Kiyi shiru kinsan babu wanda ya isa ta6a min Baby na ko shi waye ya zauna lfy
“Mommy naje Gidan su BARRISTER Yazid “
“Meya faru dashi Baby na”
“Aure yayi “
“what “
*****
Bangaren Aryan kuwa fita yayi ya tambaye me gadi nan Gidan su Nadiya ya basa amsa a takaice da Eh kudi yabasa dan yabasa lbrin wacece ita haka ya koshe labarin ta tass ya bashi da irin rashin kirkinta gdy ya masa yashige moton sa driver yajasa sai Gida
(nikuwa nace a sauka lfy)
*****
Yazid kuwa yana idar da sallah be dawo gida ba sai lokacin dinner kowa ya haďu a dining area har da Zahra basu fi 30 minutes ba kowa ya kammala Zahra ce tafara tashi ta ma su Mom da Dad sai da safe
“Asuba ta gari yarinyan ta”cewan Mom da murmushi a fuskar ta ta haura stairs Neehal ce tabiyo ta da kayan barci masu kyau da taushi riga da wando kar6a tayi suka ma juna saida safe
yanzu ma ďakin yazid tashiga ta kwanta bata canza kayan ba sbd bazata iya sa wanna kaya ta kwanta ba duk da ba wani me muni bane amma hk ta ijiye ta kwanta a capet
Yazid yana shigowa ya hangeta a kasa ta kwanta da du kunkune waje ďaya tsaki ya ja a ranshi yana cewa har da ďaki ma ďaya aka haďa mu lallai wanna Yarinya nayi alkawari saboda azaba da kanki zaki bar Gidan nan
Karasawa yayi inda take ya tsunguna daidai inda ďazu yatakata ya gani har gurin yayi ja ya kunbura taka wajan yayi da sauri ta farka da sunan Allah abakin ta tashi tayi ta zauna ta ganshi a kanta Dan Allah Kayi hkri bazan sake ba shiru yayi yana tunani kafin yace yanzu ba lokacin barci bane tashi zakiyi muje kimin ďauraya hanu
Fatan alkhairi
Ina sha.awan hakan