Sai da Junior ya yi wata hudu sannan na samu ya barni na tafi Malumfashi.A lokacin kuma har ya iya zama. Sannan ne aka sa bikin Husna da Sagir ɗinta watanni bakwai masu zuwa, dan wata biyar ne ya rage mata ta kammala karatunta.
Sanda Junior ya cika shekara ya yi daidai da tura Ahmad America za su yi bincike kan wasu cututtuka. Ba kaɗan yaso tafiya da ni ba nima haka, sai dai ba halin yin tafiyar ta mu tare, ga bikin Husna da ke zuwa Momi ma cewa tayi idan muka tafi duka shi ba shi. . .