Skip to content
Part 13 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

A soro ya kafe mashinɗinsa kana ya shiga gidan. “Abbas ne?” Aunty ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana karantar yanayin fuskarshi, da dariyar yaƙe ya bata amsa da “Eh ni ne Aunty”, hakan ne ya yi sanadin faɗuwar gaban Aunty, domin duk wanda ya san Abbas, toh zai iya banbance yanayinsa a halin farinciki ko baƙinciki. Jiki a mace ta yi mashi iso a ɗakinta. Kan tilon kujerar dake ɗakin ya zauna, ita kuma ta zauna gefen gado suna fuskantar juna. Cike da girmamawa ya gaishe ta, amsawa ta yi tare da tambayar shi Asma’u da ƴan gidansu, bayan ya tabbatar mata da ƙalau suke ne ɗakin ya yi shiru. 

“Toh ko lafiya?”, Aunty ta tambayi kanta, saboda in dai Abbas ya zo gidan tun a tsakar gida yake fara labari, ko da ita kaɗai ya taras, amma yanzu ya yi jugum kamar mai ciwon baki. 

Kafin ta iya lalubo amsar tambayar da ta yi ma kanta ne ya jefo mata tambaya shi ma “Ina su Nafeesa ne?”, Aunty ta ce “Suna Islamiyya”, ya ce “Ayya, na ji gidan shi fa”, ta ce “Aikuwa ba.”

Sake shiru ya yi, a ƙasan ranshi kuma yana tababar sanar da Aunty abin da ke tafe da shi, saboda gudun ɓacin ran Asma’u, wani sashe na zuciyarshi ne ya ce mashi “Ka san ba zaka faɗi abin da ya kawo ka ba kuma ka zo.?” Wani sashen na daban kuma ya hasko mashi matsalolin da suka dame shi tun daga farkon aurenshi da Asma’u har kawo yanzu, kuma ya nuna mashi girman matsalar da kan iya faruwa idan bai yi gaugawar sanar da manya ba. 

  Ɗago da kansa ya yi tare da duban Aunty da itama bakinta ya ɗinke, so take ta tambaye shi me ke tafe da shi, amma tana gudun yi mashi garaje, “Aunty, dama wani koke ne na zo da shi..”, sai kuma ya yi dakatawar da ta ba Aunty damar sanya shi a hanya, inda ta ce”Koke kuma Abbas?”, ya ce “Eh, wasu ƴan matsaloli ne ke ta faruwa a tsakanina da Asma’u, tun da muka yi aure na ka sa samun kanta yadda ya kamata, ƙarshe da tafiya ta nisaa, sai take ce mani in rabu da ita..”

Cike da fargabar da ta ida mamaye Aunty ta ce “Asma’un dai ke cewa ka rabu da ita Abbas?” kamar zai yi kuka ya ce “Eh”, Aunty ta ce “Tirƙashi” ƙasan ranta kuma tana jin maganar kamar almara, domin basu taɓa ba ransu nagartar Asma’u zata bari ta yi haka ba. Sanin ƙarfe ɗaya ba ya amo shi kaɗai ne ya sa ta tambayar shi “Abbas ko kana yi mata wani abin da bata so ne?”, rantse mata ya yi da Allah bai taɓa ƙirƙirar wani abu dan ya ɓata ran Asma’u ba, idan ma har an ga wani abin da ya ɓata ranta daga wurinshi, toh sai dai ajizanci na ɗan adam kawai. 

Ko bai rantse ba Aunty shaida ce wurin irin kulawar da yake ba Asma’u, saboda duk lokacin da Asma’un ta zo ko su Nafeesa suka je gidanta, toh za su dawo da labari mai daɗi dangane da irin kyautatawa mai ban ƙaye da Abbas ya yi mata, kawai ta tambaye shi ne domin sanin haƙiƙanin mutum sai Allah, mai yiwuwa a gabansu ne yake yi ma Asma’u alkhairi, bayan idonsu kuma sai yadda ya yi da ita. 

Gwauron numfashi Aunty ta sauke , lokaci ɗaya kuma ta biyo bayanshi da faɗin “Toh shikenan Abbas, gobe Insha Allahu zan shigo gidan naku, idan ma ta kama sai mu zo da Baban Nafeesa, sai a san matakin da ya kamata a ɗauka.”

Sanin gobe Asma’u zata je unguwa a goben ne ya ce “Gobe Asma’un zata fita ai, ta ce kuna da suna a familinku na can gida.” 

“Suna dai kuma?”, wani sabon mamaki kwance a fuskarta ta tambaye shi, domin a familyn mahaifinsu ba wadda ta haihu, ya ce “Eh”, shiru ta yi na wucin gadi, daga bisani ta ce “Ok, ka ce mata ta jira ni, sai mu je sunan a tare”, ta ƙi ƙaryata Asma’u ne domin bata son darajarta ta ƙara raguwa a idonsa, domin duk macen da miji ya fara kaiwa ƙara, toh ta sani kaso mai yawan gaske na darajarta ya ragu a wurinsa, kai kawai ya ɗan ɗaga “Ok, zan fad’a mata.”

  Shirun da ya sake yi ne ya ba Aunty damar ƙara nazartar shi, sosai ta fahimci tsagwaron ƙuncin da ke ranshi, dan tunda ya kafe ƙasa da idanu bai sake ko motsi ba, uwa uba ga wata irin rama da ya yi. Cikin sigar lallashi ta fara nuna mashi ba abin da ke cikin aure sai haƙuri, duk abin da Asma’u ke yi mashi sai ya kasance mai juriya, tare da ɗaukar matakin da ya dace kafin ta dena. Da ace Aunty ta san irin haƙurin da yake da Asma’u, da bata jadadda mashi ba, toh amma hakan ma tunatarwa ce, kuma bata amfanar kowa sai mumini. 

Godiya ya yi mata, sannan ya miƙe da shirin tafiya. Tayin abinci ta yi mashi, amma ya ce ya ƙoshi, duk da gurnanin yunwar da cikinsa ke yi. 

Har soro ta raka shi tare da ƙara tausasar mashi da zuciya, sosai ya ji daɗin haka, domin alama ce dake nuna ba zasu bari Asma’u ta yi yadda ta ga dama ba, duk da rayuwar ta kasance naka sai naka ne. Bankwana suka yi, sannan ya tafi ya bar Aunty da jimami. 

Abbas bai koma unguwarsu ba sai bayan isha’i. Gidansu ya biya kamar yadda ya saba ya karɓi tuwo sannan ya wuce gida. Tsakar gida Asma’u take kwance kan tabarma tana shan iska, amma ko da jin tsayawar mashin ɗinshi sai ta tashi a gaggauce ta koma bedroom, ba tare da damuwa da azababben zafin da ke ciki ba, kasantuwar ba wutar nepa. 

Aje tuwon ya yi a kan tabarmar kana ya shiga ɗakin, da fitilar waya ya haska fuskarta da ta fara jiƙewa da zufa “Yanzu me kike tsinta a cikin wannan zafin Asma’u?, shiru ta yi kamar ba da ita yake ba, sake cewa ya yi “Magana nake fa”, a tsiwace ta ɗago “Toh me ye naka a ciki?”, ya ce “Akwai kam, saboda bana son ki illatar mani da ajiyata dake cikinki.”, a hasale ta ce “Ajiyar banza gare ka, ka fitar da rai ma daga wannan banzan cikin dake jikina, dan na rantse ba zan haife shi ba.” Duk wata kalma marar daɗin dake fitowa a bakinta, in dai a kanshi ne, toh baya jin zafi, amma idan a kan Ɗan cikinta ne ji yake ransa na ɓaci, domin miyagun kalmominta zasu iya cutar mashi da ɗa ko ɗiya, tunda ita ce uwa ga abin da ke cikin, cikin ɗaurewar fuska ya ce “Habawa yarinya, na rantse naki wasa ne dangane da cikin nan, duk da a jikinki ya ke, idan kina aibata shi toh za ki ga fushina.”

“Hmmm!” kaɗai ta ce, dan fushinsa rufe mata baki yake. Sake ce mata ya yi ta fito ɗakin, amma ta ƙi, aikuwa ya ce “Toh matsalarki ce.”

Ficewa ya yi daga ɗakin ya ci tuwonsa, dan ya fahimci idan ya biye ma damuwar Asma’u toh mutuwa zai yi. 

Ita kam kamar zata sulale a ɗakin, duk irin firfitar da ta riƙa yi da hijabi, amma bata samu iskan da zai gamsar da ita ba, Abbas na shigowa ɗaukar filow ya ganta zaune a ƙasa sai tsuma take, raɓawa ya yi gefenta ya ɗauki filon, lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗn “Wanda bai ji bari ba, zai ji wohoho!.”

Asma’u ta kanta take, ƙuncin zuciya da na ɗakin ba su bari ta iya ce mashi komai ba har ya fice. “Allah ka sa wuta ta dawo”, ta fad’a murya can ciki, zamewa ta yi ƙasan ledar tana ta tsaki. Wurin shad’aya ne ijabar addu’arta ta sauko, wuta mai ‘karfin ce aka maido, godiya ta yi ma Allah cikin sauti mai cike da tausayin kanta, taƙarƙarawa ta yi ta mike tare da kashe fitilar ɗ’akin, hasken wayarta ne ya yi mata jagora zuwa kan gado. A tsammaninta Abbas zai dawo ɗakin ya kwanta, amma har bacci ya ɗauke ta bai shigo ba. 

Washe gari ko kalaci Abbas bai yi ba ya yi shirin fita, falo ya iske ta kwance kan abin sallah, ƙiƙam ya yi a kanta, kamar yadda itama take yi mashi “Toh ki shirya, Aunty zata biyo ku tafi sunan tare”, ras! Gaban Asma’u ya fad’i, domin asirinta ne zai tonu, zumbur ta tashi zaune, ta bud’e baki zata yi magana ne ya fito d’akin, “Lallai akwai wani abu a ƙasa”, ta fad’a a ranta, ji ta yi kamar ta biyo shi ta tambaye shi yadda aka yi har Aunty ta san zata je unguwa, amma rawanin tsiyar dake d’aure a kanta ya hana ta, tana ji har ya fidda mashind’insa ya tafi. 

Tuni dama baccin da ke idonta ya fice, tashi ta yi ta d’auko wayarta a bedroom, number Auntyn ta yi dialing, sai dai bata shiga ba. Ta yi trying ya fi a ‘kirga, ba tare da bu’katarta ta biya ba.

Aje wayar ta yi, lokaci d’aya kuma ta tambayi kanta “Ko dai Abbas ya fahimci shirina?”, da yake ba tsoron ta kife take ba ta yi magana cikin sautin da wanda ke tsakar gida ma zai iya ji “Idan ya sani ma sai me.” Fitowa ta yi tsakar gidan ta fara gyara, duk da ba wata dauɗa gare shi ba, saboda jiya sai da Abbas ya maida shi kamar haƙori, saƙe-saƙen zuci kuwa ba kalar wanda ba ta yi, domin jikinta ya dad’e da bata zuwan Aunty ba zai yi mata kyau ba, musamman idan ta tuna ‘karyar sunan da ta shirga ma Abbas.

Wurin ƙarfe goma ne Aunty ta zo gidan, tun a tsakar gida Asma’u ta kama kanta, domin a daburce ta yi mata sannu da zuwa. Aunty na lura da haka ta ƙara shan mur tun a tsakar gidan itama.

Gaisawa suka yi bayan sun shiga d’aki, sannan Asma’u ta miƙe “Bari a kawo maki abinci”, dakatar da ita Aunty ta yi “A’a, ba zama zan yi ba, dawo ki zauna”, zama Asma’u ta yi tana ƴar dariyar yaƙe. 

Tambayarta ta yi “Ina Abbas d’in?”, Asma’u ta ce “Ya fita”, Aunty ta ce “Ok, mun yi waya da shi ai, na zata ko ya dawo”, shiru Asma’u ta yi, bata ankare ba ta ji Aunty ta ce “Halan ba ki da lafiya”, cikin sanyin jiki ta tambayi Aunty itama “Me kika gani Aunty?”, ta ce “Wai na ga kin rame”, yadda Aunty ta ‘karashe maganar cikin taushin murya ne ya karya zuciyar Asma’u, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a kumatunta, cike da damuwa Aunty d’an russuno daga kan kujerar da take, “Ke, meke faruwa ne?”, kasa magana Asmas’u ta yi sai kuka, Aunty da tausayin ‘kanwarta ya cika mata zuciya ta ce “Tambayarki na ke, me ye ma had’inki da Abbas da ya kai ƙararki jiya?”

A hankalii Asma’u ta lumshe idanu, har zarafin kai ta ƙara yake da shi, lallai tsugunne bata ƙare mashi ba, cike da ƙarfin hali ta ce “Aunty sam bana jin dad’in zama da shi”, Aunty ta ce “Kamar ya bakya jin dad’in zama dashi; ya rage ki da wani abu ne?”, kasa bata amsa Asma’u ta yi.

Tambayoyi Aunty ta cigaba da jefo mata wad’anda suka danganci rashin abinci ko magani ko ha’kkin aure, Asma’u idan har zata iya bata amsa, to ba ta wuce duk bata da matsalar wad’annan ba, dan haka sai dai ta yi ƙasa da kanta, Aunty ta ce “Butulci za ki yi ma Ubangiji ko, yanzu duk ni’imar da Allah ya yi maki amma kike neman saki ko.?”

A nan ma dai da ace Aunty ta san damuwar Asma’u ƙila da bata kware mata baya ba. Haƙiƙa soyayyar Nas ta yi mata mugun kamun da ba zata iya kallon samun Abbas a matsayin arzkin da zata yi godiya a kanshi ba. 

Wasu zafafan hawaye masu kaurin gaske ne suka sake gangaro ma Asma’u ga kumci, take kuma Aunty ta ji tausayinta ya sake dawo mata, danne shi ta yi ta cigaba da fad’in “Ki rufa mana asiri dan Allah, ki barmu mu ji da maraici da kuma talaucin dake damun mu Asma’u.” Fad’a sosai ta yi mata, dan duk da ba da Abbas aka yi zaman ba, amma ta fahimci bata da gaskiya, Asma’u kuwa kamar ranta zai fita saboda kuka. Abbas na dawowaya tsinkayi muryar Aunty a tsakar gida na fad’in “Wallahi idan kika rabu da Abbas, toh bana zaton za ki samu nargatcce kamar shi”, wani irin dad’i ne ya ratsa shi, domin irin wannan razanarwar ka iya tasirin da Asma’u zata dena gudun shi.

Cikin d’akin ya shiga tare da zama kusa da Asma’un suna fuskantar Aunty. Had’e su Aunty ta yi ta fad’a musu gaskiya tare da nuna masu aure bautar Ubangiji ne, muddin mutum na son samun lada a dalilinsa, toh sai ya cire son zuciyarshi, ya kuma kyautata ma abokin rayuwarshi.

Abbas ya ji dad’in wannan fad’a da Aunty ta yi masu, godiya sosai ya yi mata, sannan ya fito d’akin. Hakan ne ya ba Aunty damar tambayar Asma’u “Ina kike son zuwa ne da har kika yi ‘karyar ana suna?”, Asma’u bata son Aunty ta zarge ta, dan haka ta ce “Aunty gidan ne ba dad’i”, Aunty ta ce “Toh ki dena irin wannan ‘karyar, domin idan ya gano ki, zai fara zargin kina zuwa wurin da ba shi kika tambaya ba.”

Wannan nasiha Asma’u ta d’auke ta, amma fa da zummar a gidan Nas zata yi aiki da da ita, kamar yadda duk wani sirrin zaman aure ta adana shi, sai a gidan Nas zai yi tasiri.

Da Aunty ta ga Asma’u ta yi ladab, sai ta fara shirin tafiya. Abbas ya so ta biya gidansu, amma ta ce tunda zuwan ba na lafiya bane ba zata je, ya kuma kar’bi uzurinta, domin shi ma bai son gidansu a san rikicin da ke tsakaninsa da Asma’u. Har bakin titi ya rakata ta hau napepe, yana dawowa gida ya taras da Asma’u ta kife kai a kan kujera tana ta kuka.

Dafa kafad’arta ya yi “Asma’u”, cikin ransa yana jin kamar ya yi kukan shi ma, domin bai san yau she zai rabu da ‘kuncin Asma’u ba. Zummuwa ta yo mashi tana fad’in “Rabu da ni baƙin mugu, ka je ka kai ƙarata, a tsammanika zan janye ƙudirina na ƙinka”, ba arziki Abbas ya ja baya yana fad’in “SubhanaLllah”, dan mugun kallon da take mashi sai da ya kaɗa mashi hantar ciki, cikin sanyin murya ya ce “Asma’u yaushe zaki fahimce ni ne?”, mi’kewa ta yi tana kuka ta ce “Ba rana, kuma idan baka rabu da ni ba sai na zama ajalinka”, tana rufe baki ta cukumi wuyanshi tana fad’in “Ni ce ajalinka na fad’a maka idan baka rabu da ni ba”, tare da ‘kara ma’kure shi da iya ƙarfinta, cikin tsananin firgici Abbas ya shiga ɓanɓarar hannunta a wuyansa, domin ko shakka babu yanayinta ya tabbatar da zata iya aikata abin da take faɗa.

Idanu jajur ya dube ta bayan ya samu sa’ar ‘kwace kanshi, magana yake son yi, amma tari da zafin maƙara sun hana shi, sai da ya yi da gaske kana ya iya cewa “Na gode Asma’u”, kai ya sa zai fita daga d’akin, cewa ta yi “Adungi zuwa rafi! Wata rana gawarka ce zata fita ba kai ba”, dakatawa ya yi a bakin ƙofa ya dube ta “Tunda rayuwata a hannunki take ba”, ta ce “A hannuna take mana, tunda tsoron rasa ta ya hana ka rabuwa da ni”, gaba ya yi ba tare da ya sake tanka mata ba, aikuwa taraka shi da fad’in “Allah ya haɗa ka da bala’i da musiba idan ka fita, Allah ya sa ƙatuwar mota ta bige ka ka mutu in huta da jaraba”, daga chan soro ya ce “Bakinki ya sari dutsen kwatarkwashi.” 

Durƙushewa Asma’u ta yi akan guiyawunta ta dasa sabon kuka, tun kuwa tana yin mai sauti har tai ga ta koma na zuci, daga ƙarshe ta baje a tsakar falon tana ta ajiyar zuciya. 

Abbas ma zaure ya tsaya ya ci kukanshi kamar ƙaramin yaro. Shi kam a wannan gaɓar dai zai iya cire Asma’u a rai, toh da ya cire ko dan ya samu salamar zuci, toh ba zai iya ba, dan haka ya ɗauri ɗamarar jure duk wata uƙuba tata, madamar daga ƙarshe zata so shi.

Kamar yadda Asma’u ta gaza samun nutsuwa a ranta bayan ta gama kukan, haka shi ma Abbas ya gaza, wurin aiki ya nufa, amma ya gaza yin komai, Abdul kuma ya lura da yanayinsa, amma sai ya share shi, dan bai son jin abinda shi ma zai ɓata mashi rai. Hankalinsa na gida. Azuhur na yi ya ɗauko mashinɗinsa, sai da ya biya wani gidan abinci ya siwo sannan ya dawo gidan. 

Kwance ya same ta falo a kan abin sallah tana ta ajiyar zuciya, ɗan russunawa ya yi “Asma’u, tashi ki ci abinci”, zaune ta tashi, idanunta cike da ƙwallah ta ce “Na ce maka ina buƙata ne, ka ɗauke abincinka tun kafin na juye maka shi a jiki”, da wani irin kuka mai taɓa zuciya ta ƙarashe maganar. 

Har cikin ransa ya ji wannan kukan, tausayinta ne ya kama shi, dafa kafaɗunta ya zo yi amma ta kwaɓe mashi hannu. 

Gwauron numfashi ya sauke “Asma’u me kike so?”, cikin ƙaraji ta ce “Saki”, ya ce “Toh ki bari ki haihu tukunna”, fizgo shi ta yi “Wallahi baka isa ba, kuma wannan shegen cikin zubar da shi zan yi”, a wannan karon bai bata amsa ba ya fice daga gidan. 

Da ba dan Asma’u na da burin auren Nas ba, da ta yi fatan mutuwa a yanzu ko dan ta huta da baƙincikin da ke ranta. 

Haka ta wuni, kuma ta kwana ba ci bare sha, aikuwa da Asuba ta fito sallah jiri ya kwashe ta, kafin ta kai ƙasa kuma hankalinta ya fice a jikina, dan haka ba zata iya tantance duniya take ko lahira ba, Abbas na dawowa Masallaci ya ganta sume a ƙasa, cikin tsananin tashin hankali ya yo kanta bakinsa na faɗin “Asma’uuuu..!” 

*****

Dan Allah ku dinga yi mani like da comment hakan ne zai ba bakandamiya damar biyana. Idan kuma baku da account a bakandamiyar ku yi ƙoƙari ku buɗe, zaku amfana da wasu ƙarin litattafan da fasihan marubuta suka wallafq. 

<< Cikin Baure 12Cikin Baure 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×