Da Bismillah na dan shiga dakin kadan, tare da zubawa tarin ƙur’anan da ke shirye a cikin wata kanta ido, na shiga kirgasu daga inda nake tsaye guda dari ba ɗaya ne cif, na juya kan tulin carbin da ke tare a kan tabarmar kabar da ke shimfide a tsakar dakin, on my estimates sun kai dubu daya.
Na juya can gefe inda aka aje faifan nan me dauke da yashi sai kuma korai guda biyu da aka rufe da wani faifan, bayan nan babu komai a cikin dakin.
Ban san ko minti nawa na kwashe a tsayen ba, kamar yadda ban san me nake tunani ba.
Cike da rashin tsoro na karasa cikin dakin, na dauke faifan da aka rufe ƙwaryar babu komai a ciki, ita ma daya kwaryar babu komai a cikin ta, na mayar da faifan na rufe tare da mikewa tsaye na nufi kofar fita.
Sai bayan na fito daga sashen Hammah ne tsoro ya kama ni, na rika tafiya ina waigen sashen kamar wani ya biyo ni, step ɗaya kacal na taka a kan entrance namu na ji kofar Aunty Adama ta motsa, cikin sauri na juya ina kallon waye zai fito, ganin Aunty Adama ce ya sanya ni juyawa zuwa kofar shiga part din namu.
Yadda na ga ta nufo apartment din namu ya sanya ni fasa rufe kofar har sai da ta shigo sannan ta ce “kira min Aisha”
Tare muka sakko da Auntyn sai dai ni dakina na wuce, amma ban rufe kofa ba ina son jin me ya kawo Aunty Adama.
“Aisha! Tun da aka kawo ki gidannan daga ni har yarana wa ke shiga harkar ki?”
Aunty Adama ta fada cike da gadara.
Da sauri na haye gadona ina lekensu ta window.
“Na san babu wanda yake shiga harkarki, ban kuma sa yarana sun raina ki ba, fada min da sanin ki Abdul’azeez ke min rashin kunya?”
Cikin rashin son hayaniya Aunty ta ce “Wani abu ya faru ne Mamansu Huzaima, ta ya zan aika shi ya miki rashin kunya?”
“To na sani koda sanen ki…”
“Wlh ban sani ba” Aunty ta yi saurin katse ta,
“To ki fada mishi ya fita idona in rufe, ke ce daidai yi na ba shi ba, ke din kuma ba ki isa in yi da ke ba. Don rashin kunya Abdul’azeez zai je har dakina yana min wasu suratan banza a kan kare, me ye kuma ƙuda bare roman Shi? Waye Abdul’azeez bare karen shi? Ina ruwana da wani karenshi can”
“To!” haka na ji Aunty ta fada, yayin da Aunty Adama ta dora a fusace,
“Wallahi idan bai fita ido na ba a kan karen can, zan samo yan iskan layi su kama min karen su murde mishi wuya da ranshi in ga ko me zai iya yi” ta rufe maganar a fusace.
Aunty kuma ta dora da “Wallahi ni ban san komai ba, da idona ma ban ga Azeez ba, ki yi hakuri don Allah zan yi mishi magana.”
“Ba wannan ne kawai abun haushin ba, shigar shi sai da ya dauke min karamar wayata a falo, daga na tashi na shiga kitchen, ki ce mishi ya kawo min Sim din, karamar wayar kuma ta magance mishi talaucin duniya”
Daga haka ta fice, yayin Aunty ta zauna kan kujerar da ke kusa da ita cike da bacin rai.
Kamar in ki fitowa, sai kuma na kasa jure ganinta a yanayin da take ciki, a kasalance na fito zuwa inda take zaune.
Na zauna kan kujerar da ke fuskantarta na ce “Don Allah Aunty ki yi hakuri!”
Ta dago kai tana kallo na, yayin da fuskarta ke nuna min bakin cikin da take ciki.
Cikin muryar da ke nuna bacin rai ta ce “Abdul’azeez zai kashe ni wallahi.”
Da sauri na ce “Haba Aunty ki daina fadin haka don Allah”
“Hammah fa bai jima da fada min ya shiga dakinsa ya daukar masa makudan kudade ba, ni ma ban fahimci ya kwashe min sarkokina ba sai dazu, jiranshi nake ya shigo gidan, kin ji ashe ya shigo, har ya daukar min magana, me wayar 10k za ta yi wa Azeez? Sarkokina daya diba nawa zai siyar dasu sama da miliyan biyu, kudin Hammah kuma Allah ne kadai ya san ko nawa ne, duk wannan bai ishe shi ba, sai ya dauki wayar Adama. Ya kyauta”
Ta karashe maganar kamar za ta yi kuka.
Yanzu kam ban san me zan ce ba, saboda duk bayan wancan lissafin akwai wani sabo na jakar kudin da ya ƙara dauka ba da jimawa ba.
“Adama ta yi gaskiya, dama ta ce min sai na yi danasanin haihuwar abin da ke cikina.
Ni dai ban ce komai ba, amma kuma furucin Auntyn ya kama hankalina.
Ta mike tsaye, na ga ta tafi luu za ta fadi, da sauri na mike da zummar rike ta, kafin in riketan har ta dafa kujera, daga nan ma sai ta zauna sosai a kan kujerar. Tana mayar da numfashi, ga wani zufa da ya rufe ta, duk da sanyin A.C da ke falon.
Da sauri na isa fridge na dakko mata ruwa, kadan ta sha, ta nufi dakina da sauri, na bi bayan ta a guje, kan kofar na tsaya ina kallon yadda take amai.
Ni na taimaka mata ta gyare jikin ta, na kamo ta zuwa inda gadona yake ta kwanta.
“Sannu Aunty!” na fada da kasalalliyar saboda zuwa lokacin hankalina a tashe yake, na rasa Aunty ai ban san ya duniya ta za ta kasance ba.
“Ko in kira Ya Azeez mu je asibiti”
Kai ta girgiza alamar a’a, wanda kuma ya yi daidai da tashin ta zuwa toilet ta kuma yin wani aman, abu kamar wasa amanta uku, daga nan kuma sai dai tai ta yunkurin aman ba ta yi. Dalilin da ya sa ta galabaita sosai.
Ba tare da na kara neman shawararta ba na kira Ya Azeez na fada mishi Aunty ba lafiya ya taho mu kai ta asibiti.
Tsakanin ni da shi ban san wa ya fi damuwa ba, ban san yana sonta ba sai a ranar, kamar ya karbe ciwon zuwa jikinshi.
Shi ya sanya mata hijab ya saita mata takalmanta muka rika ta zuwa wajen motarshi
Kai tsaye peace hospital muka nufa, shi ya yi komai har zuwa lokacin da aka bamu gado, bayan mun je mun yi tests na jini da kuma fitsari.
Drip aka sanya mata, na janyo kujera tare da zaunawa kusa da ita, hannun da aka daura mata drip din a cikin hannuna, ba na iya barin kallon ta, yayin da idanunta suke lumshe, wani lokaci kuma ta kan bude su a kaina a hankali.
Kamar 20mins da sanya mata drip din Ya Azeez ya turo kofar hannunshi rike da wata takarda.
Kan kofar ya tsaya shiru, yayin da na kasa fassara yanayin da ke fuskarshi, kallon shi kawai nake yi har zuwa lokacin da ya ce “Zo.” kai karshen maganar ta shi ta yi daidai da ficewarsa daga cikin dakin.
Ban san ya zan fassara faduwar da gabana ke yi ba, amma kamar zai fasa rigata ya fito, wani irin tsoro nake ji, kar dai wata muguwar cutar ce aka gano a jikin Aunty.
Can harabar asibitin na hango shi tsaye, ya goya duk hannayensa a baya ya kalli gabas, da alama ya yi nisa cikin tunani.
Isowata ce ta sanya shi juyowa tare da sauke bayyanannar ajiyar zuciya yana kallo na.
Jin bai ce min komai ba ya sa na ce “Ya Azeez menene yake da mun Auntyn?”
Ya ja dogon tsoki, tare da wurgo min takardar da ke hannunshi yana fadin “Wai ciki ne da ita”
Na fasa daukar takardar da na yi niyya, na waro ido ina kallon shi, ji nake kamar mafarki, Aunty da ciki abin da na dade ina fata, ji nake kamar in taka rawa, amma yadda na ga ran shi a cunkushe ya sa na kama kaina. Har sai da ya kara cewa “zan sanya a cire shi tun da bai jima ba, wane irin ciki kuma fisabilillahi”. Ya karashe maganar cikin jan dogon tsoki.
Ni dai takardar na duka na dauka, ni fara ƙal nake kallon ta, na zabi in yi shiru ne kar ya sauke fushin shi a kaina, ba wuya yay ta ball da ni a wurin nan.
“Haba da Allah! Da wane ido zan kalli abokaina wai Mamata ta haihu.” ya yi maganar cike da bacin rai.
Ni dai uffan ban ce ba, illa kallon rubutun da ke jin takardar da nake yi.
Tsokin da ya ja ne ya sanya ni dago kai ina kallon shi, sai aka yi sa a shi ma ni yake kallo.
Take ya tamke fuska tare da nuna ni da yatsa cikin kakkausar murya ya ce “Wallahi zan ci ubanki, yar iska kawai, ai na san murna kike yi, shegiya munafuka shi ya sa kika yi shiru.”
Na aje kaina kasa kamar munafukar ina sauraron shi “babu wata haihuwa da za a yi a wannan gidan, wannan cikin sai an cire shi.”
Ni dai ko kaina ban dago ba, bare in ce wani abu.
Kudi ya wurgo min, “ga shi nan idan ta farka ku je scanning, kuma kika fada mata za a cire cikin wallahi…”
Na yi saurin ja baya ganin yana matso ni “Na rantse miki da Allah ke ma sai na zubar da ke. Shegiya munafuka “
Abin da na fahimta a kaina kawai yake son huce haushinshi, ni ban ga abun damuwa ba don Aunty ta yi ciki, abun da muke ta addu’a ba dare ba rana.
Dogon tsokin shi ya katse min tunanina “Ciki fa!” cikin wata irin murya ta bacin rai ya yi maganar.
“Kar ma yaron nan ko yarinyar nan ya bari ya zo duniya, saboda na yi ta cin ubanshi ne ba ƙaƙƙautawa”. Ya karashe maganar tashi da nufar inda ya parker motarshi.
Wannan ya sa ni ma na nufi hanyar da za ta mayar da ni cikin asibitin cike da farin cikin da ban yi ba dazu.
Tafiya nake ina waige har na shiga corridorn da zai sada ni da dakin Aunty, na kara bude takardar sai na rufe ta cike da murna, sannan na shiga rawa a wurin, kafin na kwasa da gudu na yi dakin da Aunty take kwance.
Na tsira mata ido bayan na shiga dakin, kafin na kama hannunta na yi kissing a hankali don kar ta tashi, sai kuma na juya na yi sujudur shukur, kafin na mike na rika tsalle a dakin ni kadai kamar mahaukaciya, yau ji nake kamar an biya min hajji, Aunty da ciki, wayyyo Allahna dadi. Allah ya nuna min ranar da Aunty za ta haihu, Allah kuma ya sauke ta lafiya.
Haka nai ta murnata cikin daki ni kadai har zuwa lokacin da Aunty ta farka.
Na taimakata ta mike zaune”Sannu Aunty! “
“Yauwa Maryam” ta fada a hankali
” Na gode, Allah Ya yi miki albarka “
” Amin” na amsa ina kallon ta cike da tausayawa, kafin in ce “kina son wani abu ne?”
Shiru ta dan yi kafin ta ce “A’a! Na fi son mu tafi gida, ki je ki nemo min wata nurse mu yi magana”
“Sun ce idan kin farka aje scanning”
“Ban so, just go and call one nurse for me please, ba na son yawan magana”
Haka na tafi neman nurse, ko 20mins bamu kara ba a hospital din mu ka tafi gida.
Muna isa Hammawa ya ce ai Hammah ya tafi nemanmu, Aunty ce ta ce za ta kira shi a waya idan mun shiga, sai dai me ya Ya Azeez har ya yi aikin nashi, ya kwance TV plasman falo, ya kuma daukewa Aunty waya.
Ban taba jin takaicin satar Ya Azeez irin yau ba, a rana daya babu wanda bai yi wa sata ba a gidan. Kuma halin da mahaifiyarsa take ciki bai hana shi kara mata bacin rai ba.
Kokarin kwantarwa da Aunty hankali nake ta yi, yayin da na yi amfani da wayata na kira Hammah na shaida mishi mun dawo.
Ba jimawa sai ga shi ya dawo, shigowarshi dakin Auntyn ne ya sanya ni ficewa zuwa dakina, kamar 30mns da shigarshi dakin na ji muryarshi yana kwada min kira.
Da sauri na fito inda mu ka yi kicibis a falo, Aunty na bin shi a baya a hankali.
“Zamu fita da Auntynki, ki kula da gidan sosai saboda Azeez.”
Na jinjina kai idanuna a kan Aunty cike da tausayinta.
Bayan fitarsu ne shiga kitchen na hadowa dog abinci Shi da Monkey.
Bayan na basu na dawo daki, a lokacin na lura da ɗan akwatun da nake aje sarkokina a kan mirror.
Da hanzari na karasa wurin tare da bude shi, abin da zuciyata ke fada min shi na riska, Ya Azeez ya kwashe min duk sarkokina da zobuna na.
“Kai Subhnallah!” na fada hade da zama a gefen gado jagwaf.