Skip to content
Part 30 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bayan na idar ne, na koma dakin Aunty, kishingide take tana latsa wayarta

Shigowa ta ba ta sanya ta ta daina ba, sallama ta kawai ta amsa ta cigaba da abin da take yi.

Ni kuma na samu wuri na rakube, kamar 5mns da shigowa ta ta ce “kin ci abinci ne?”

Na jinjina kai alamar eh.

Zamanta ta gyara idanunta a kaina, kafin ta ce “Ke dariyata kawai kike sani Maryam, ba ki san damuwa ta ba, kila tunaninki komai na min dadi, saboda ina auran hamshakin mai kudi.
Kodayake kowa ma irin wannan tunanin zai yi, sai dai abin da ba ki sani ba shi ne, ni ban san komai a dadin aure ba, ina dai cin mai kyau, in kwanta a wuri mai kyau, wannan kam Alhamdulillah. Ina godewa Allah. “

Ta ɗan numfasa sannan ta ci gaba” Daga lokacin da na auri Hammah kawo yanzu da nake ba ki wannan labarin, akwai tarin abubuwan da ban san ya a kai suka faru ba, kuma ban san dalilin faruwarsu ba.

Misali sau biyu Hammah jal ya taba kusantata, baya iya kwana a dakina, kamar yadda ban iya kwana a dakin shi.

Sai duk abin da na ce ina so, to yana yi min.

Ɗabi’un Abdul’azeez da ban san dalilin da ya sa yake yin su ba, shi ma kuma Ina jin bai san dalilin ba, zan iya yarda asirin ne kamar yadda Baffa ya fada, saboda dama Mamansu Huzaima ta fada min ba zan yi alfahari da abin da na haifa ba. Amma kuma ban kasa a wurin yi mishi addu’a ba.

Duk lokacin da na yunkura da niyyar barin gidan Hammah sai in tuna ku, ku biyun nan, dama-dama ke, amma Azeez kam kila ya koma tare hanya yana kwace kayan mutane.
Wannan dalilin ya sa na hak’ura, ina jiran lokacin da Allah zai yaye min ko kuma in aurar daku, zuwa lokacin hankalina zai fi kwanciya da barin gidan.

Sai kuma ga ciki, cikin da kullum nake ganin kamar ajalina na dauka, ina tunanin yadda zan haihu, kullum da abun nake kwana nake tashi.

Duk ba wannan ba ma… “

Na yi saurin dago kai ina kallon ta.

“Maryam da wane irin kudi Hammah ya rika ciyar damu. Hankalina a tashe yake. Wa ya sani ma ko saboda kudin haram din da muke ci ne Allah ke ta jarabamu da abubuwa. Kai ni kam ina ganin abu. Maryam don Allah fada min, wane sirri ne na Hammah kika sani?”

Na sauke ajiyar zuciya a hankali kafin na kwashe duk abin da na sani da abin da na gani na fada mata.

Ba ta katse ni ba, har na kai aya, ta shiga jinjina kai, kafin ta ce” kin san me ya faru yanzu? “

Na girgiza kai alamar a’a

Ta kuma muskutawa a karo na ba adadi sannan ta ce” Hammah da kanshi ya ce kudin da ya tara ba dukkansu ne na halak ba, Sai dai bai fadi hanyar da ya bi ya tara ba, ya ce dai yanzu ya tuba ya bar duk abin da yake yi wanda ba daidai ba. Da na matsa mishi ya ce min ke din kin san komai “

Na yi saurin daga hannayena sama ina fadin” Wlh ni ba duk na sani ba, wanda na fada miki shi kadai na sani “

Shiru ya ratsa dakin kafin ta juya hade da daga filon da ta dora hannunta a kai, ta janyo wasu kudi masu yawa, ta mika min.

Na karba ina kallon ta.

Fuskarta ta canja zuwa damuwa, wannan ya sa gabana ya shiga faduwa
har zuwa lokacin da ta ce” Sadakinki ne… “

Wani fitsari na ji yana min zir-zir tun kafin ta kai karshen maganar fatana kar ta ce da Bandi.

“Da Abdul’azez. Hammah ya ce komawarki wancan gidan akwai matsala “

Bayyanannar ajiyar zuciya na sauke, gabana na wani bugu fat-fat.

Yadda ta yi shiru, ya tabbatar min ba za ta kara magana, dalilin da ya sa na ake kudin, na fita daga dakin jiki ba kwari

*****
MAIDUGURI

9:00am

Aunty Adama ce da Gana suke takawa a kasa zuwa bakin hanya inda zasu samu abun hawa, tun da ta zo jiya suke hirar abu daya har yau kuma hirar ba ta kare ba

Yanzu ma Aunty Adama ce take cewa “Wannan karon interlock zan balle, in binne kwalbar nan in kuma sanya Malam ya turo min baƙaƙen aljanu su rika yi min gadin ta, kamar dai yadda suka rika yi min gadin duwatsun nan.

Gana ta zaro ido tare da fadin” Kin manta wuyar da aka sha kafin a samu masu gadin, yanzu a ina za ki kara samun abin da kika basu suka yi miki gadin? “

“Inda aka samu wancan mana. “Aunty Adama ta karbe.

“Ke ya fi a ba ki wanda za ki iya binnewa a ko ina, kamar yadda na fada miki jiya, ba dole sai a cikin gidan ba.”

” Gana kina mance hatsabibancin Aisha, magani ma tana tare da shi bai yi aiki ba, ina ga ta yi nesa da shi. “

“Kuma fa.” Gana ta amsa a sanyaye

“Sannan a wannan karon kamar yadda na fada miki, dole sai an sanya tsanar Aisha a zuciyar Hammah. Daga karshe ya sake ta. “

Gana ba ta ce komai ba, Aunty Adama ta dora da” Shi kuwa wannan gantalallen ɗan nata, so nake ya kara gantalallewa”

Wannan karon ma Gana ba ta ce komai ba.

Aunty Adama ta kuma dorawa da fadin “Shi kuwa mijin Huzaima, farraqu zan sanya a yi mishi da ko wace mace.”

“Ai ba mijinta kadai ba, su dukkansu.” Cewar Gana tana kallon ta

“Wlh fa, gara kawai a yi musu gabadaya, tun ba mijin Karima ba. Idan ma kin samu labarin mutuwarshi to mace ce ta kashe shi. Ni tsorona ma kar ya dakko musu cuta”

“Shi ne damuwar” Gana ta fada lokaci daya kuma tana daga wa mai Napep hannu.

Shigarsu Napep din ne ya sanya su yin shiru, har suka isa inda zasu je basu kara magana ba.

A waya suka kira Malam, ya ce su shiga.

Bayan gaisuwa Gana ce ta fara ba shi labarin abin da ya faru sannan ta dora da “So nake a cusawa Bukar kaunata, ya ji babu wacce yake son gani a duniyar nan sai ni, ya ji babu wacce take sai ni. So nake ya rika dukawa a kan gwiwarsa yana hawaye yana neman afuwa ta.”

Dariyar Adama ce ta katse ta, ta shiga kyakyatawa kafin ta ce “Ke ƙawata sauki dai.”

“Babu wannan zancen Adama, ya shanye min kuruciyata yanzu ya ce ya sake ni, har da yi min korar kare, kuma ki ce wai zan raga mishi wlh karya ne”

A fusace Gana ke maganar kamar Alhaji Bukar ne a gabanta yake neman afuwar tata.

Adama ta yi siririyar dariya, Gana kuma ta ci gaba

“Ita ko matar Bilya, so nake dare daya ya sake ta, sannan a saka mata kaunarshi, tai ta wahala kuma kar kowa ya aure ta”

Adama ta kuma tintsirewa da dariya jin yadda kawarta ke ta kulla mugunta

Malam ma ya murmusa kadan, kafin ya ce “abinda kike so kenan?”

“Idan wannan ya faru, to za a tafi shiri na gaba”

“Ke fa?” ya juya kan Adama

Zamanta ta gyara kafin ta ce “bayan maganar ruhin kwalba da mu ka yi, ina son kuma Hammah ya tsani Aisha ya ji ba ya son ganinta. Su kuma mazajen yarancan zuciya nake so a kashe mu, a rufe idonsu da kallon ko wace mace. Su kuma yaran nawa sai abin da suka ce”

Ya shiga jinjina kai lokaci daya yana miko matsa katuwar kwalbar da aka cunkushe cikinta da layoyi.

Ta karbi kwalbar tare da fadin “Ina son a kara hadani da masu gadi”

“wannan karon ba za ki iya ba.”

“Me ya sa? Idan har za su yi min gadin kwalbar nan zuwa haihuwar Aisha da girman abin da ta haifa aiko zan iya” ta yi saurin tarar numfashinshi

“Ko ba ki binne ta ba, idan har suna tare da ita, babu mahalukin da ya isa ya ganta, bare kuma ya iya taba ta”
Ya karfafa mata gwiwa

“Aiko zan iya” ta fada cike da kwarin gwiwa.

“Da farko za a samu sabuwar gawa a daura mata wannan bakin kyallen da zan ba ki, to idan har gawa ba za ta bude ido ta yi gani irin namu ba, babu wanda ya isa shi ma ya ga kwalbar nan”

Duk suka yi shiru kafin Gana ta ce “Ai samun gawar shi ne matsalar”

“Wa kuke so a kauda muku? Wannan karamin aiki ne. ” Malam ya tambaya kanshi tsaye yana kallon Adama

Kafin ta yi magana Gana ta ce “Wlh ban da ina son daukar fansa da an kashe min Bukar ko matar Bilya”

Cike da mamaki Adama take kallon Aunty, yayin da kasan zuciyarta take saka wani abu daban.
“Yarinyar nan Maryam nake son a kauda.” Aunty Adama ta amsa kai tsaye

Gana ta kalle ta da sauri.

“To amfanin me take yi min, ba ta daga min ba ta aje min, kuma babu wanda ya dogara da ita” cewar Aunty Adama cikin sauri.

“Kuma fa” Gana ta fada a sanyaye.

“Ita Maryam din ta yi?” Malam ya kara tambaya

Aunty Adama ta shiga girgiza kai a hankali tare da fadin “A kyale Maryam din nan, na canje ta da Hammawa maigadi”

“Wannan din ya yi miki?” ya kuma tambayarta

“Eh wannan kam ya yi. Amma a jira sai na koma gida.”

“Yaushe za ki tafi gidan?”

“Gobe da assussuba zan tafi”

“To shi kenan, idan kin isa sai mu kara tattaunawa”

“To shi kenan.” ta yi maganar hade da fito da kudi masu yawa ta aje mishi.

Bayan sun fito ne Gana ta ce “Me ya sa za ki canja da wanda bai taba yi miki komai ba, mutuwar Hammawa ai ba za ta daki Aisha kamar ta Maryam ba” cike da bacin rai Gana ta yi maganar.

“Kwantas kawata! Abin da ya sa na canja Maryam shi ne. Ba za a bar ni in rabi gawarta ba, har in ida nufina. Shi kuwa Hammawa Allah ne gatanshi mune gatanshi ba shi da kowa sai mu, don haka ni ce nan zan nemo masu suturtashi, in zuba musu kudi in yi yadda nake so da gawar shi”

Gana ta shiga jijjiga kai hade da yaba basirar kawarta kafin ta ce “Lallai kin yi tunani mai kyau.”

“ki bari kawai, Sai dai goben idan na isa.”

Wunin ranar hirarsu duk a kan yadda zasu aiwatar da aikinsu ne. Suna kara karfafawa juna gwiwa, da irin yadda zasu ja zarensu bayan sun aiwatar da komai.

Asubar fari kuwa Aunty Adama ta dakko hanyar zuwa yola.

*****

GEMBU

10:00 am

Tun daga lokacin da mu ka yi magana da Aunty zuciyata ba ta kara samun sukunin zama shiru ba tunani ba.

Ga tambayoyi fal a bakina ban san wa zan yi ma wa ba.

Me ya sa Hammah ya ce komawata gidan akwai matsala?

Ta wace hanya Hammah ya tara dukiyarshi?

Ya Azeez ya san da maganar auranmu?

Na rasa farin ciki zan yi da auran ko akasin haka?

Burina dai shi ne auran Ya Azeez amma na fi son a yi auran da amincewarshi.

“Ko ya zai kalli abun oho?” na yi maganar a hankali jiki a mace.

Daga cikin dakin da nake na ji Aunty ta fito tana kwala sallallami, yadda ta rikice haka ni ma na fito a rikice, ta sauke wayar idanunta a kaina ta ce “Kin ji wai Mamansu Huzaima ta rasu.”

<< Da Magana 29Da Magana 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×