Ango Da Amarya
Bayan fitar su hussy, su zakkiya suka fito da Amarya falo dan yi musu abin da ya tara su kamar yadda sameer ya buƙata, sa'ed ya buɗe taro da addu'a yayi nasiha, sameer ma ya ɗora da nashi, ƙawayen Amarya nata amsawa, a ƙarshe shadow ya rufe da addu'a baza kace shine mai tsokanar ango ba, an shiga fagen serious tongue, Har ƴa basu haƙuri da su zauna da juna da gaskia da Amana.
Aka shafa addu'a, sameer y ba ƙawayen Amarya kuɗin d ƴa hanasu ciniki a farko dan baya son. . .
