Kwana biyun Mustafa, Ummi da Inna ne ke ta jigila da Fatiman.
Ta ce wannan take so, idan an yi kuma da ta ci kadan sai ta ce ta koshi, wani kuma ko cin ma ba ta yi, a bangare daya kuma ba ta iya shan ruwa.
Da zarar ta sha sai amai, sai dai a zuba july juice a ciki, ko a siyo mata dangin minerals.
Har zuwa lokacin kuwa Fatima ba ta san ciki ne da ita, don babu wanda ya fada mata, har kuwa Mustafan.
Tsawon sati Mustafa na a gida, ciwon Fatima ba sauki, daga wannan. . .