Sosai Fatima ta samu sauki, kawai dai ba ta koma gidanta ba ne, sai ta yi arba'in.
Ita kanta ta ji dadin hukuncin Mama, saboda gidan ba kowa daga ita sai Ummi, Ummi ma da dare ne kawai suka fi zama tare.
Amma a nan kam ku san kullum gidan cike yake, wannan ya shiga wannan ta fita, hakan yana debe mata kewa, hade da rage mata wasu tunanin, musamman a kan mutuwar Alhaji, da take ganin kamar ita kawai aka yi wa mutuwar.
Dama-dama yanzu Ya Jamil wata irin kulawa yake ba ta ta musamman, da ace. . .