Skip to content
Part 3 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Me kika yi ne wai?’ Mama ta tambaya dafe da kirji.

“Ban yi komai ba, dazu da kika aike ni gidan Baba Cindo, lokacin da na je Aunty Sadiya na wanka. Shi ne na ga Goga ya fita dakinta yana tura waya a aljihu, bayan ta fito wanka kuma ta ce ba ta ga wayarta ba. Na fada mata abin da na gani da aka kira shi ya ce wai shi bai dauki komai ba, shi ne suka tafi police station. “

“Yauwa to Mama kin ji dalilin kiran.”

Cewar police din yana murmushi.

“To ita kuma me za ta yi a can?”

“Kawai za ta fadi abun da ta sani ne.”

“Kar fa wani abu ya samu yarinyata, bana son ta shiga sabgar wadancan yaran da kowa ya san ba mutumci ne da su ba.”

“Kar ki damu Mama babu abin da zai same ta sha Allah.” Cewar police din me mukamin cpl.

Shiru ya dan ratsa gurin kafin mama ta ce, “shi kenan.”

“Ni fa ba zan iya zuwa har police station a kasa ba gaskiya. Ya yi nisa, idan ba ka zo da mota ba, babu inda za ni, islamiya ma zan tafi.” Cewar Fatima tana kallon police din”

Cike da mamaki Mama da police din suke kallon Fatima, yanayin fuskarta kawai za ka kalla ka tabbatar da abun da ta fada.

“Shi kenan, ni zan ba ki kudin mashin.” Cewar Mama don ta san halinta sarai.

“Ke kuma Mama? Sai ka ce dai wayarki aka sace.”

“To shi kenan, ni zan bayar da kudin” police din ya fada yana murmushi.

“Yanzu na ji bugu an sa sanda, amma fa har da na dawowa za ka ba ni.” Cikin ido take kallonshi lokacin da take maganar.

“Ba ki da damuwa a kan hakan.”

“Yallaboi, amanar yarinyata fa a hannunka.”

Ya yi murmushi, “Mama kina ji da yarinyar nan ta ki, kamar ki ba ni ita.” Ya fada a daidai lokacin da suke fita daga gidan.
“Ko ba za ki auri police ba?” Ya tambayi Fatima lokacin da suka fita waje.

“Sai dai a wata duniyar ba wannan ba.”

“Me ya sa?”

“Ra’ayina ne kawai. Ba ni kudin in tare me mashin.”

Ya ciro 200 ya mika mata, yana kallonta cike da mamakin maganarta da take yin ta kai tsaye.

A ‘yan mintuna da yakasance da ita, ya fahimci yarinya ce me ra’ayi, haka tana da tsaurin ido.

Sauka ta yi a kan mashin din ta shiga wani office, a hankali ta yi sallamar, wanda fatar bakinta ne kawai ta motsa.

D.P.O din ya dago kai yana kare mata kallo, hannunshi rike da biro. A lokacin ita ma kare wa matsaikacin ofishin kallo take, me dauke da benci na zama guda biyu a bangon gabas dana yamma, sai kujeru guda biyu a gaban teburin d.p.o, ba komai sai tarkacen da ba ta san amfaninsu ba, da kuma hotuna manne a jikin bango.

“Kin gama abin da kike yi tun da ba ki iya gaisuwa ba.” D.p.on ya yi magana yana kallonta cikin daure fuska.

Aje kwayar idonta ta yi cikin na shi hade da daure fuskarta tamau

“Shaida na zo yi.”

“Don kin zo shaida, sai ba za ki gaishe mu ba.’

Wannan karon Aunty Sadiya ta kalla, kallon da ke nuna ta gaji da maganar d.p.o.

“Yallaboi mu yi abin da ya tara mu.” Aunty Sadiya ta fada cikin girmamawa

“Kin san wannan?” Ya nuna mata Danliti da ke tsugunne a tsakiyar ofishin.

Suka hada ido da Danliti ta tabe baki, hade da lankwashe harshenta cikin baki tana wasa da shi kafin ta ce, “Eh.”

“Lokacin da kika shiga gidan wannan matar kun hadu da shi?”

Ta kuma dora idonta a kan Danliti da ya aje kai a kasa kamar bakuwar tunkiya.

“Mun hadu.”

D.p.o din ya zuba mata ido yana nazarin kalamanta, hade da kallon yadda take abu kamar da isgilanci.

“Samu guri ki zauna.” Ya fada kasancewar tun lokacin da ta shigo a tsaye take.

“Ka ga, ka tambaye ni kawai abin da kake son tambayata, zan amsa ma. Amma ba zan zauna ba, tun da dai ba shi aka kira ni in yi ba.”

“Ke! Ki shiga hankalinki, a police station kike ba gidan Babanki ba.” Ya yi maganar cikin tsawa hade da zaro ido.

“Tohhhh!” Ta fada hade da rike haba tana kallonshi.

“Yo police station lahira ce? Kai ka ji.”

Aunty Sadiya ta yi saurin tashi, hade da dukawa gaban teburin d.p.o. “Yallaboi fita batun yarinyar nan, ba ita kadai ba ce tana jinnu.”

Shiru yana kallon Fatima kafin ya ce,

“Fada mun abin da kika gani ya yi da kuka hadu a gidan?”

“Na ganshi ya fito da waya a hannunshi yana kokarin sanyawa cikin aljihu.”

“Kin tabbatar?”

“To kuma a kan me zan yi karya?”

“Kai gaskiya ne abun da ta fada?” Ya juya kan Danliti, bayan son magana me tsawo na hadasu da Fati.

“Karya take mun, ni ban dauki komai ba.”

Ya juyo da idonshi a kan Fati alamar yana son karin baya ni.

Ta mirgina kai gefe da gefe kafin ta ce.

“Ni fa na fadi abin da na sani, ya rage naku ku gano gaskiya da karya a tsakaninmu. Idan an gama zan tafi.”

Ya yi shiru yana nazarin kalamanta kafin ya ce,

“Sergeant Barkono, zo ka tambayar min yaron nan.”

Fatima ta tabe baki hade da jefar da kanta gefe daya.

Shigowar Sergeant Barkono ya sa Danliti cewa, “Yallaboi yi hakuri zan fadi gaskiya, ba sai an tambaye ni ba, ni ne na dauki wayar, amma ban yi komai da ita ba, tana dakina a cikin takalmi sau ciki, a hada ni da wani in dakko mishi.”

Jin ya fadi haka ya sa Fatima ficewa daga ofishin ba tare da ta jira an ba ta umarnin hakan ba.

Gidan Aunty Bilki ta wuce matar yayanta Bashir.

A can gidan Fatima ba Aunty Bilki labarin abin da ya faru ta yi, wani su yi dariya, wani ko su yi jimami.

Har zuwa lokacin da Bilkin ta kare faten tsakin shinkafa da ya sha aleyahu da yakuwa, ta cikawa Fatima madaidaiciyar Samira.

Fatima na idar da sallahr Magriba ta dauki faten zuwa gida.

Hanyar shiru ba motsin mutane kamar ba yanzu aka yi magriba ba, shi ya sa ba ta son yin dare a gidan Aunty Bilki saboda hanyarsu koda rana babu yalwar mutane.

“Ke karamar ‘yar iska.” A ka fada hade janyo hannun da ba ta rike kwanon faten dake kanta ba.

Ya juyo da ita tana fuskantarshi, Danliti ne, tsoro da firgici suka yi dirar mikiya a kirjinta.

A zahiri kuma fisge hannun ta yi hade da fadin,

“Kai babban dan’iska.”

Ya yi murmushin mugunta,

“Yau za ki tabbatar da ni babban dan’iska ne wallahi, don kuwa sai na aje maku tarihi a gidanku, koda zai kasance shi ne karshen numfashina.”

“Wallahi karya kake, ko uban da ya haifeka bai isa ba kai.”

“Zan rufe bakinki, rufewa ta har abada.” Ya katseta

“Ai wallahi kai dai ba ka isa ka rufe mun baki ba.”

“Ke har kin isa ki bayar da shaida a kaina don ubanki, yar iska, yau sai na yaga mutumcinki fata-fata, sai iyayenki sun yi hawayen jini a kaina.”

“Na je na bayar da shaidar, ga ka nan dan iska barawo, ni ce na ce ka yi satar. Kuma iyayenka ne za su yi kukan jini ba na wa ba.”

Ya kai hannu hade da cin kwalarta, ya fisgota zuwa gabanshi, ta yadda take jin tsamin jikinshi sosai.

Ya fitar da karamar wuka hade da aje ta dab da fuskarta.

“Ki bi umarnina kawai ko ki kwana a lahira.”

“Idan kuma kika yi mun ihu, saina sanya tsinin wukar nan na caccake miki idanuwa ta yadda koda an kawo miki dauki ba za ki amfanu ba a gaba.

A yanzu kam tsorata sosai, musamman yadda ta ga ba wani a kusa da zai kawo mata dauki.

Kallonta yake cikin magaribar da jajayen idanuwanshi.

Yana jiyo yadda kirjinta ke bugawa, saboda yadda hannu yake a kan kirjinta.

Jujjuya kanshi gefe da gefe ya yi, alamar ko tana da abun cewa.

Shiru ba ta nuna alamar xa ta yi magana ba, haka ba ta dauke idonta a
kanshi ba.

“Biyo ni” ya fada a lokacin da yake kokarin tafiya

Dagewa ta yi duk kuwa da jan ta da yake.

Ganin ya fara gwada mata karfi ne ya sa ta kifa mishi kwanon samirar dake kanta.

Ya yi saurin sakinta hade da yada wukar da ke hannunshi, saboda yadda zafin ya ratsa fatarshi yana shiga cikin tsokarshi.

Mama zaune a kan sallaya tana lazumi sallamar Jamil ce ta fito da ita tsakar gida inda yake tsaye yana tambayarta inda ta aje mishi cajarshi.

Shigowar Fati a guje ne ya sanya mama yin shiru, illa dai ta mika mishi cajar da ke hannunta.

“lafiya? mama ta tambaya.

Maimakon ta amsa tambayar shigewa ta yi tsakiyarsu hade da sakin kuka me sauti.

Ba komai ne ke sanya Fati kuka ba dalilin da ya sa hankalin Mama tashi kenan.

“Ke kalle ni ki fada mun me ye ya faru, dazu har station din na aika a duba mun ke aka ce an sallame ki.

“Danliti ya tare ni a hanyata ta dawowa, ya ce wai sai ya keta mun rigar mutumci, kuma har ya nuna mun wuka wai zai yankani idan na yi mishi ihu.” Cewa Fati tana share hawaye.

Mama ta dire sallallami hade da tafa hannayenta,

“Wai don kawai kin bayar da shaida a kanshi? Ni fa shi ya sa sam ban so zuwa bayar da shaidar nan ba.”

“Kin tabbatar bai miki komai ba?” Jamil ya tambayeta cikin wata irin murya da ta kasance bakuwa a gareta.

Jijjiga kai ta yi alamar Eh lokaci daya kuma tana share hawaye

“A ina kika bar shi yanzu?”

“Can kofar gidan manager bayan na watsa mishi faten da Aunty Bilki ta ba ni.”

A fusace Jamil ya bar gidan.

Mama da hannunta ke kan haba tun dazu, tunani take idan da Danliti ya aikata wani mugun abu akan Fatima fa, ita dai koda kashe shi za’a yi ba za ta gamsu ba. Ta godewa Allah da bai ba shi sa’a ya aikata wani mugun abu a kan Fati ba.

Tsawon lokaci babu wanda ya yi magana, da alama kowa da abun da yake tunawa.

Shigowar Aunty Hauwa ne ya sa su mayar da hankali a kanta, bayan sun amsa sallamar da ta yi a sanyaye.

“Mama me ya sa kika bar Jamil ya fita gidan nan?”

“Me ya faru?” mama ta tambaya jiki a mace.

“Ita Fatiman ma ubanwa ya kaita wani bayar da shaida can, ke ba namiji ba. Kuma kin san halin yaran nan sarai.”
Aunty Hauwa ta fada hade da kallon Fatima da tun dazu take tsaye.

“Ki fada mun me ke faruwa, ba dai yankar Jamil din suka yi ba ko?” Mama ta yi tambayar jiki a mace.

Aunty Hauwa ta sauke ajiyar zuciya “Ina gida aka fada mun wai ga Jamil can suna fada da Danliti har ya sumar da shi. Shi ne mutanen Danliti abokanshi suka rufar wa Jamil har ma sun yanke shi da wuka, shi…”

“Me?” Mama ta yi saurin katse ta. Ba ta jira amsarta ba, ta nufi hanyar fita waje.

Da sauri Aunty Hauwa ta rikota.

“Ina za ki je?”

“Zama kike son in yi yarona na cikin hatsari, suna ina yanzu?”

“Haba Mama, mun daidaita komai, suna Police statio dukkansu, har da Bashir ma, Bashir din shi ma kamar an yanke shi.”

“Subhanallah” Mama ta fada jikinta ya kara mutuwa sosai.

Mamaki ne ya kama Fatima ganin yadda Jamil ya yi fada a kanta har ma aka yanke shi, wannan fa kamar misalin ya sayar da ranshi ne a kanta. Abun da ba ta taba tunani ba a irin zaman da suke yi da shi.

Yaya Bashir ma Sam baya shiga sabgarta, sai ta yi sheka kwandalarshi ba ta shigo hannunta ba. Haka sukan shafe watanni ba tare da sun yi wata magana me tsawo ba bayan gaisuwa. Ita wani lokacin ma mantawa take da shi cikin ‘yan’uwanta. Ashe kuma a hakan yana sonta, baya son abin da zai taba ta, har yana bayar da ranshi fansa akanta. Lallai kowa ya rasa dan’uwa ya yi kuka.

Hawaye masu dumi suka gangaro mata, haka ta ji kaunar’ yan’uwan nata yana shiga ko wane sassa na jikinta.

Sallamar da aka yi ne ya sanyasu mayar da hankulansu akan masu shigowa. Da sauri Mama ta tares u, Jamil ta fara rikewa tana tambayar,

“Ya ya jikin naka? Me ya sa ku kai haka ne?”

“No Kar ki damu Mama, ba ciwo ba ne sosai.” Ya fada yana kokarin zama akan tabarmar da Aunty Hauwa ta shinfida.

Bashir kuwa a kan dutse ya zauna, a hannu suka sare shi Jamil kuma a goshi.

“Kar ku damu fa, mun yi abun da ya dace ne, haka kowa ya kamata ya yi a kan ahlinshi.”

Bashir ya fada yana duban su mama da suke tsaye kamar sun kada surika.

“To yanzu ina yaran suke?”cewar Mama jiki a mace.

“Duk suna station.” Cewar Jamil.

“Mtswwww!” Fati ta ja dogon tsaki, tun shigowarsu sai yanzu ne ta samu kuzarin Magana.”

Dukkansu hankalinsu ya dawo kanta. Amma shiru ba ta yi magana ba.

“Shi ya sa ake son maza su rika shan maganin tauri, ba wai namiji ya zauna jiki kamar kabewa ba.”

Bayan fitar maganar ne ta gane ashe a zahiri ta yi ba a zuciyarta ba.

<< Daga Karshe 2Daga Karshe 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×