Skip to content
Part 46 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Kamar ba za ta daga kiran ba, sai kuma ta daga.

“Ina kika aje wayarki?”

“Ba ni da caji.” ta amsa shi kamar ba ta son yin magana.

“Aunty ta zo?”

“Ta zo”
Ta kuma amsa shi kai tsaye.

“Fatima kwanciyar hankalina da na ki, ke da na kowa ma, shi ne ki bar min cikina, kina son tursasani yin abin da ba na so, a kan me za ki cire min ciki? Saboda kawai kina karatu? Wlh! Kin ji na rantse miki, ina kokarin cika alkawarin da na daukarwa Alhaji ne na barin ki ki yi karatu, amma kam da na yanke alakarki da wannan makarantar.”

Jin shiru ba ta ce komai ba ya dora” Ba na son komai ya samu cikina, kuma duk abin da kike bukata da ya shafe shi, just let me know, I will do it”

Jin babu alamun za ta yi magana, sai ya yanke kiran, ta bi wayar da kallo, kamar tana jiran Mustapha ya fito ta cikin wayar, mamakin yadda yake mata magana a tsawace take yi, abin da bai taba yi ba, tun daga lokacin da aka fara maganar auran shi kawo yanzu basu zauna lafiya ba, daga wannan sai wannan. Tabe baki ta yi hade jefar da wayar kan katifa, da ta sani tun asali ma ba ta fada mishi akwai cikin ba, da cirewa ta yi bakinta kanin kafarta, da yanzu hankalinta kwance, amma ta yi azarbabin fada mishi Allah Ya kara mata.

Haka ta wuni ɓacin rai, ko karatu ma haka nan ta yi bawai don tana jin dadinshi ba.

Wanshekare ma bayan ta gama gyara dakinta, ta yi break da ragowar kifin jiya, sai ta nufi dakin Umaima, karon farko da za ta, shiga dakin wata, so take ta tambayeta nawa aka biyo ta a fitar da suka yi jiya.

Bugawa biyu ta yi, Umaima ta bude kofar, wani sansanyan ƙamshi ya doki hancinta, daga inda take tsayen tana iya hango tsakiyar dakin Umaiman, mai dauke da katuwar katifa da aka lullebeta da farin bedsheets, sai ƙaramin fridge, da kayan kallo madaidaita, komai dai na dakin madaidaici ne, akwai teburin karatu mai dauke da tulin litattafai, da alama
karatun ma take yi

Sanye take da dogon hijab army Green Mai hannu, ya fito mata da siririyar farar fuskarta, Umaima kyakkyawa ce, wacce hutu ya bayyana sosai a jikinta. A kallo daya kuma za ka shaida hakan, komai nata mai tsada ne, yar gayu, irin dai yadda Fatima take son kasancewa.

Daga wajen suka gaisa kafin Umaima n ta ce “Bismillah mana, ki shiga.”

Cikin muryarta mai tarin nutsuwa ta yi maganar, komai na Umaima akwai nutsuwa babu rawar kai. Karon farko da Fatima ta ji tana son dabi’a irin tata, idan tana abu sai ka rantse yanga ce, amma da alama hakan take.

“Ba sai na shiga ba, dama ina son ba ki kudinki ne na jiya” cewar Fatima daidai tana fitar da hannunta da ke cikin hijab.

Cike da mamaki Umaima ke kallon kudin kafin ta ce “Wane irin kudi kuma?”

Ita ma Fatima sai ta ce “Na jiya mana da muka fita cin abinci”

Rike da haba Umaima ta ce “Haba, manta don Allah, ni ba zan karɓa ba.”

Duk yadda Fatima take magiyar Umaima ta karbi kudin, ba ta karɓa ba, dole ta kyale ta hade da yin godiya.

“Yau ba lecture ne? Umaima ta tambaya a kokarinta na rufe bakin Fatima daga godiyar da take mata.

” Babu, duk mun yi covering, zan fita ne zuwa gidan sisterna,, da muka yi bikinta last week”

“Shi ne ba a gayyace mu ba?”

Murmushi Fatima ta yi kafin ta ce “An gayyace ku yanzu.”

“Really?” Umaima ta tambaya hade da zolaya.

“sosai.” Fatima ta amsa ta.

“To shi kenan, sai zuwa yaushe za ki je?”

“Irin 2pm din”

“OK.” Cewar Umaima.

Da haka Fatima ta koma daki, cike da sha’awar Komai na Umaima, akwai bukatar ta zama haka ita ma,, rayuwa a silent akwai dadi. shigarta ke da wuya ta samu ana kiranta.

Ganin Blessing ce sai ta daga da sauri, suka fara gaisawa sannan suka shiga hirar abin da Fatiman ta fi so wato karatu. Har Blessing din ke shaida mata za ta kawo mata ziyara karshen sati kafin a fara exam.

Sosai Fatima ta ji dadin hakan, duk wanda zai goyi bayan karatunta tana son shi, shi ya sa ta fara jin Blessing a ranta.

Ita kanta Blessing din amfani take da damar ta, idan kana son jin dadin zama da mutum to ka gano weak point din Shi, cikin sauki za ka rika sarrafa shi. Tun da ta gano na Fatima ta fara ganin canji, a hankali za ta saye ta gabadaya.

Misalin 2:30pm kuwa suka isa gidan Zainab, sosai gidan ya hadu, don har Umaima sai da ta koka, ta ce wai gidan amarya daban yake.

An tsattsagawa Zainab dukiya kam, komai na girma aka yi mata.

Basu baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, a hanyarsu ta komawa ne Umaima ta ce “Kanwarki ce?

” Eh to, amma da yan watanni na girme ta?

“Kina nufin ba Mamanmu daya ba?” Umaima ta tambaya wannan karon tana kallon Fatima.

“Diyar babbar yayarmu ce”

“Kai amma kuna kama”

Dariya mai sauti Fatima ta yi, yau ne karon farko da aka ce suna kama da Zainab.

“I’m serious fa” Umaima ta karfafa maganarta

“Ke ce ta farkon da kika fara fadin haka.”

“Da gaske?”

“Kwarai” Fatima ta amsa

“Amma ai gaskiya na fada.”

“Ke ce dai kike ganin hakan, amma babu ta inda mu ka yi kama da Zainab.” Fatima ta amsata cikin siririyar dariya.

Yau kam har suka iso gida suna dragging ne, inda Umaima ta dage lallai akwai kama tsakanin Zainab da Fatima, ita kuma Fatima ta ce babu Sam. Wai basu hada komai da Zainab ba, yayarta ce kawai da suke uwa daya uba daya ta haifi Zainab din, bayan nan ba babu wata alaka tsakaninta da Zainab.

Abun da ya ba Umaima dariya kenan, har suka isa gida dariyar take yi.

Yanzu sai Umaima ta zama kawar Fatima, duk da basu faye zama dakin juna ba, amma a kullum zasu hadu a gaisa a taba ƴar hira, akwai bambancin dabi’u sosai tsakanin Umaima da Fatima amma haka nan kowa ke kokarin ganin bai sabawa dan’uwansa ba.

Umaima yar gayu, komin ta tsab-tsab a nutse. Ba ta faye surutu ba, amma kuma suna hira sosai da Fatima.

Fatima yar kai tsaye ni tsaye, komin ta kai tsaye kuma a bude ba rufa-rufa. Wannan ke ba Umaima nishadi har ba ta iya wuni ba tare da ta ga Fatima ba.

Ita kuwa Fatima kokarin Umaima da son karatunta ne ke burge ta, ku san komai ta sani, shi ya sa ita ma take son koyi da ita.

Yau Asabar da misalin karfe 12pm na rana kiran Blessing ya katse baccin Fatima, dama ba ta dade da fara shi ba, kasancewar ta yi karatu da safen, don ranar Laraba zasu fara jarabawa.

Da muryan bacci ta daga kiran amma jin Blessing tana fadin wace unguwa take a Katsina take ta wattsake, cike da mamaki ta ce “Kin zo ne?”

“oh Kin dauka wasa nake yi?”

Fatima ta Mike zaune sosai, har lokacin mamaki take yi, ta dauka da wasa take mata, ashe da gaske take yi.

Wa mai mashin din ta kwatantawa unguwar da gidan, sannan ta fita gate tana jiran isowarsu.

Ba jimawa kuwa mai mashin din ya sauke Blessing.

Yau kam shigar yan Maidugurin ta yi, farar tas din lifaya ta nade jikinta, sosai Blessing kyakkyawa ce, musamman yanzu da take dauke da dan matashin cikinta, kamar dai Fatima Blessing ba ta faye yin heavy makeup ba, amma hakan bai hana kyawunta fita ba, tun da ta sauka take washewa Fatima baki, yayin da Fatima ke ta kokarin danne abin da take ji, Allah Ya sani ta tsani ganin Blessing kokarin dannewa kawai take yi, babu macen da Blessing za ta kasance kishiya a, gare ta, ba tare da ta rika razanata ba.
Mace cikakka haka ta ko wane bangare.

Dole ta kirkiro dariya ta manna a fuskarta, lokaci daya kuma ta nufi Blessing din.

Ga mamakinta sai Blessing din ta rungume ta, ita ma sai ta taya beranta bari suka rungume juna.

Lokaci daya kuma ta amshi kayan hannunta suka nufi ciki, lokaci daya kamshinta mai dadi ya cika dakin, abin da ya ba Fatima mamaki hade da tambayar kanta, ko wane irin turare Blessing ke amfani da shi oho.

Sam ba ta ji dadi ba, da ya kasance yau ba Umaima a gidan amma haka nan tai ta kokarin ganin ba ta bar wata kofa a bude ba. Yayin da Blessing ma ta tattara hankalinta kaf kan yadda Fatima ke tafiyar da rayuwar ta.

Kowa dai karantar kowa yake.

Ko sau daya Blessing ba ta yi maganar Mustapha ba, kamar yadda Fatima ma ba ta yi ba, sai karfe hudu suka shirya zuwa gidan Aunty Lami, amma sai da suka fara zuwa gidan Zainab.

Sosai Aunty Lami ta yi mamakin ganin Blessing, amma sai ta boye mamakinta, ta tari Blessing din da sha tara ta arziki.

Ita kanta Blessing din sai da ta kara jin dangin Fatima sun burgeta, basu baro gidan ba sai karfe takwas na dare, direban Aunty Hauwar ya kawo su.

Mustapha ya iya takunsa, ko sau daya bai kira ko wacce a cikinsu ba, kamar yadda su ma basu kira shi ba, tun da dai ya ji Blessing ta sauka lafiya kuma sun hadu da Fatima sai ya fita batunsu.

Misalin karfe goma na dare Blessing ta yi shirin bacci yayin da Fatima ta janyo handout din ta.

Ba ta kwanta ba sai wajen biyu na dare bayan ta sallah ta rufe da shafa’i da wutri.

Da safe Blessing ce ta hada musu abun kari, soyayyar doya souces, suka ci tare gwanin sha’awa don sosai Blessing ta saki jikinta.

Sai misalin karfe goma na safe ta fara shirin tafiya.

Lokacin da Blessing ta shiga wanka ne sakon Mustapha ya shigo wayar Fatima.

“Ga kudi nan, ki yi mata tsaraba”

Yake kuma alert din 10k ya shigo mata.

Ta zuba ma wayar ido, kafin wani murmushin da ba ta san dalilinshi ba ya kucce mata, a zahiri kuma ta ce “Ban yi.”

Ta dora da “Wato a wanki kifi da ruwanshi ko, ba zan yi ba, ai makaranta ta same ni, tsarabar da Zainab da Aunty Lami ta yi mata sun isa, ni fa ba yar iska ba ce yar neman suna da wurin zama mtswww!” ta rufe maganar zucin da jan tsoki a zahiri, a daidai lokacin Blessing ta fito wanka.

Fatima ta bi lafiyayyar fatarta da kallo a fakaice, lumui kamar tuwon mai tsabta, gashin kan nan baki sidik sai sheki yake alamun yana samun kulawa, ta tuna nata wanda sai ta shekara ma ba ta ga saloon ba, tana dai yin kitso a kai-a kai. Kafafun nan kamar ba ta taka kasa lukui abin ta.

“Anya!!” maganar ta kucce mata ba tare da ta yi niyya ba.

Blessing ta yi saurin dago kai hade da tambayar “Momyn Ziyad are you alright?”

“Yas I’m” ta amsa mata a hankali tare da gyada kanta, tana kallon ta har ta gama shirinta cikin doguwar Bakar riga mai kyau, ta nade kanta, take ta fita fes abun ta.

Fatima hijab kawai ta zura, sai a lokacin ta dakko manyan ledojin jiya tana fadin “Kar ki manta da wannan fa”

Blessing din ta yi dariya “Na ki ne. Wannan (tanuna Leda milk color me kyau) , daga Dadyn Ziyad ne, wannan kuma tsarabata ce, I’m sorry ban san abubuwan amfaninki ba.”

Ta fadada fara’arta, kafin ta ce “Na gode sosai”

Sosai Blessing na mamakin Fatima gano kalarta akwai aiki, wani lokaci ta kan yi abu a takaice, sannan ka rasa kansa, wani lokacin kuma ta yi shi kai tsaye, kuma kai tsayen za ka fahimci ina ya dosa.

Amma sha Allah ba za ta sare ba, sai komai ya daidaita kamar yadda take son daidaitarshi.

Har tasha Fatima ta raka Blessing kuma ita ta biya kudin motar, ta jira motar ta tashi sannan ta dawo gida.

Ta kasa fassara wannan ziyara ta Blessing amma sosai zuwan Blessing din ya tayar mata da hankali, Anya kuwa ba ta sakaci ba, cikakkiyar mace kamar wannan tana tare da mijinta tsawon lokaci haka, ya kwana da ita ya tashi da ita a gida daya, ita tana nan wai tana karatu.

Anya ba ganganci a wannan lamari, yaranta hudu kuma ko wanne da inda yake.

Tana kaiwa nan a tunanin sai ta fada kan katifa hade da rushewa da kuka, kuka take yi sosai, wani irin daci take ji, Lallai yana da kyau ka yi amfani da damarka a lokacin da ta same ka, yanzu tun asali da ace ta yi karatunta me zai sa tabar mijinta da wata mace har tsawon wannan lokacin.

Ko ba a fada mata Blessing na samun yadda take so, jikinta kadai ya isa shaida, kamar an wanko ta da injin, tana kaiwa nan a tunanin sai ta yi saurin kallon fatar jikinta.

“Ba hadi.” ta fada a zahiri. Sannan ta ci gaba da kukanta.

Sai da ta ƙoshi da kukanta ne ta janyo ledar da Blessing din ta kawo mata, lafayoyi ne kala uku masu kyau, daya baka an ci bakin da farin zare, daya kuma fara irin ta Blessing din, dayar kuma omo blue.

Tabe baki ta yi “Ni ina na iya na da wannan abu. Ni ba tubani ba, in bi in wani nade jikina kamar gawa, ku dai da ku ka ga zaku iya ku je ku yi fama.

Ta rika bin turarurrukan da kallo da sauran maya-mayan, sannan duk ta hada su cikin leda ta tura gefe.

Ledar da aka ce Mustapha ya kawo ta janyo, lesussuka masu kyau kala biyu, sai atamfa ma super Holand masu kyau, sai kuma takalma da hijabai. Sai wani dan karamin kwali a can Kasar ledar.

Shi ta dakko, lokaci daya kuma ta bude shi, sabuwar wata dal android wacce ba kowa ne ke da ita ba a lokacin, a kaf gidan nasu ma ba ta taba ganin kowa da ita ba, gara ma kwanaki ta ganta a hannun Umaima yanzu kuma ba ta ganin ta.

Ta shiga jujjuya wayar, har ga Allah ta yi mata kyau, a can kasan kwalin ta ga ƴar farar takarda.

Ta shiga warware ta, ta zubawa rubutun ido, don kuwa hannunshi.

“I’m still love you Fatima. Take care!”

Ta kafe rubutun da ido, yayin da zuciyarta ta karye, sai ta matse takardar a hannu hade da fadawa kan katifar ta kuma fashewa da kuka.

Tana son Mustapha sosai, ko ba komai shi din uban yaranta ne, amma ta rasa dalili yanzu sosai haushin shi take ji, duk yadda ta so ture wancan haushin ta faranta mishi sai ta kasa.

Ita da kanta ta rarrashi kanta, sannan ta yi wanka ta shiga school library Don samun sauki cunkushewar zuciyarta.

A lokacin da su
Fatima suka fara exam ne Mama kuma ta fara rashin lafiya, dole Aunty Hauwa ta kwashe su Hassan zuwa wajenta, babu wanda ya fadawa Fatima ciwon Maman, basu son tayar mata da hankali ga jarabawa.

Babu laifi jarabawar dariya kuka ce, kasancewar ta ta farko, sosai ta yi mata wahala, har yar rama ta yi, don ma wannan karon cikin ba laulayi, kusan komai ci take yi idan ka dauke indomie, ko kamshin tafasarta ba ta so.

Yau kam Aunty Lami ta je duba Mama, duk da Maman na samun sauki sosai, saboda tana samun kulawa, musamman yanzu da aka gano ciwon sugar ne ke damunta.

Aunty Hauwa, Aunty Sadiya sai Aunty Lami ne a dakin, yayin da Aunty Lamin ke basu labarin rigimar Fatima da Mustapha a kan zubar da ciki.

Mama da ke kwance ta yi zumbur ta mike zaune “Fatiman ciki gare ta?”

Aunty Lami ta ce “Ai kam, shi ne ta ce za ta cire, Mustapha yana ta bala’i.”

Aunty Hauwa da ta, saki baki cike da mamakin maganar cikin ta ce “Yo wane cirewa kuma ai sai ta hakura kawai ta haihu”

“Yanzu Fatiman ciki ne da ita Lami?” Mama ta kuma tambaya.

“wlh kuwa” Aunty Lami ta amsa.

“Ai kuwa to Allah Ya isa.” cewar Mama lokacin da ta koma t a kwanta.

Aunty Sadiya ta tuntsire da dariya tana fadin “Gidanmu gidan shagali in ji Aunty Ayyo. To Allah Ya isar kam ma waye Mama?”

Su Aunty Hauwa ma suka fashe da dariya a tare, Aunty Lami ta ce “Allah Ya kawo mu suruka na yi wa suruki Allah Ya isa.”

Cike da kunar rai Mama ta ce “Ba ku san irin haushin da Mustapha yake ba ni ba ne shi ya sa.”

“To Mama ina sauran fada an cire ido, aure ne Mustapha ya yi, ba shi kenan sai a hakura ba.”

Mama ta galla ma Aunty Hauwa harara tana fadin “Ku kenan barayin na tsinta, ai dama ke ce kanwa uwar gamin da kika hada auran.”

“To Mama yana iya, wlh ni ma ba a sona ba, ta ya zan so a yi wa Fatima kishiya, uwar daki Mustapha ya dauke ni, maganar nan ta taso idan ban bayar da goyon baya ba, sai ace don Fatima yar uwata ce”

“To yanzu kuma da kika yi mishi aure, ya dauke ki, uwar garinshi ma ba ta daki ba.”

Aunty Lami da Aunty Sadiya suka fashe da dariya, Aunty Hauwa ce kawai ta yi shiru.

Mama ta katse dariyar tasu da fadin “Mustapha bai kyautawa yarinyata ba, ta dauki yarda ta bashi, amma ya kwance mata zane a kasuwa. Shi ya sa ko me Fatima za ta yi mishi a yanzu wlh ba zan sa baki ni bana ganin laifin ta, ta je can tai ta yi mishi “

“Har da cire cikin?” Aunty Hauwa ta kuma tambaya.

“Ban da shi kam, shi ma fa kawai saboda ina tsoron kar ta cutu ne.”

Hannu a kan Haba Aunty Hauwa ta ce “Lallai borin namiji ne.”

“Kwarai ma kuwa.
Duk lokacin da na tuna Fatima na makaranta Mustapha na Abuja cikin daula da matarshi suna cin duniyarsu da tsinke hankali kwance wlh haushi nake ji kamar in yi aman zuciyata. Sam Fatima ba ta cancanci wannan sakayyar ba.”

“Mama don Allah ki daina irin wannan tunanin,, kina kyautata mishi zato. Kuma shi ai bai hana Fatima komawa Abuja ba, ita ce ta ki zuwa, in don Allah ne fa.” cewar Aunty Sadiya
Cikin kwantar da murya.

“Ke da Allah can!” Mama ta gwale ta, kafin ta dora da

“Gaskiyar Fatima ke kyanwar Lami ce, ba kya cizo ba kya kashe bera, don na tabbata za ki iya ba Mustaphan aron kudi ma ya cika ya yi aure, naka dai naka ne ko baya ba ka komai.”

Aunty Hauwa ta yi dariya, jin akwai wacce ake munanawa zato fiye da ita.

Aunty lami ta ce” To sai ma ga Blessing din a Katsinar, kwana ma ta yi”

Duk suka bude baki suna kallon Aunty Lamin “To yin me?” suka hada baki gabadaya.

“Wai ziyara ta kawo ma Fatiman.”

“Ta dai zo ganin sirrin ta, ai ƙonannen wayau ne da ita.”

“Gaskiya kam tana da wayau.” Aunty Lami ta fada, Aunty Hauwa dai da Aunty Sadiya basu ce komai ba.

Karar wayar Aunty Hauwa ce ta katse mama daga maganar da ta yi niyya.

Aunty Hauwa ta tsirawa sakon Jamil din ido, lokaci daya kuma ta ce “Innalillahi Wa’inna Ilaihir Rajiun!”

Duk suka zuba mata ido, Mama da ke kwance ta kuma tashi zaune jiki a sanyaye ta ce “Me ye kuma?”

Aunty Hauwan ta yi shiru, cikin jimami ta ce “Jamil ne wai Aliya ta haihu mace, amma kuma Aliyar ta rasu.”

Gaba daya suka dauki sallallami suka dire a tare, sannan shiru ya ziyarci dakin.

<< Daga Karshe 45Daga Karshe 47 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 46”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×