Skip to content
Part 55 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Yau ma dai ku san kwashe daren suka yi wajen hira, kafin da asuba suka fara shirin tafiya, basu kadai ba, hatta dangin Blessing na Maiduguri ranar zasu tafi.

Sosai Fatima ta ji haushin yadda suka hana ta tafiya gida a ranar, don sosai ta so ta tafi tare dasu.

Kodayake sai da Mama ta yi mata zagar zogale sannan ta hakuran.

Tana ganin yadda suke ta shiri, yayin da Blessing ma ƴan’uwanta ke shirin komawa, wannan karon dai lafiya ake shirin rabuwa babu wani sabani.

Misalin karfe bakwai ƴan’uwan Blessing suka dau hanya, karfe takwas kuwa su Aunty Lami duk suna farfajiyar gidan, can cikin daki kuma Fatima ce, Umaima, Zainab da Ummi.

Umaima ce ke yi wa Fatima bayanin magungunan da Ammi ta sako masu, wadanda ma fi akasarinsu daga Saudiyya ne, na gyaran jiki da kuma na gyaran aure.

Ummi ta kwashi wasu, Fatima ba ta hana ta ba, don ita din tamkar uwa ce, Zainab ce dai ta ce ba ta so, ba ta su take yi yanzu ba.

Duk suka fito suna dariyar maganar Zainab din.

Zainab ta yi gaba zuwa tsakar gidan, ta bar su Umaima, ita ma Umaiman nan ta bar Ummi tsaye da Fatima tana kara yi mata maganar makarantar.

Fatima ta karaso wurin motar ganin Umaima a front seat din motar Jamil ya sanyata tuntsirewa da dariya kafin ta ce “Kin san motar waye wannan kika shiga?”

Bata rai Umaima ta yi kafin ta ce “Ai dai Aunty Lami ce ta ce in shiga”

Yadda Umaiman ta yi maganar, sai abun ya kara ba Fatima dariya. Irin ita ba ta so din ba, matsa mata aka yi.

Ita kuma Umaima dariyar Fatiman ce ta kara ba ta haushi, shi ya sa ta yi sauri bude murfin ta fito a fusace.

Sai ko Fatima ta kwasa da gudu tana dariya.

Wanda hakan ya janyo hankalin Mustapha da Jamil wanda suke tsaye can gefe da Aunty Lami da alama wani abu muhimmi suke tattaunawa.

Ganin kallon da suke musu, sai Umaima ta dakata da bin Fatima, amma ta hade fuska sosai kamar za ta yi kuka , yayin da Fatima ke can nesa da ita tsaye tana dariya.

“Har yanzu fa Fatima jin ta take yi kamar jiya aka haife ta, wlh har yanzu akwai yarinta a kanta. Cewar Aunty Lami tana kallon su Mustapha, kafin su ce wani abu ta mayar da hankalinta kan su Umaiman, tana tambayarsu.

“Me ya faru?”

Dama kamar jira Umaima ke yi, sai hawaye suka zubo mata shar. Ta kai hannu tana gogewa, Abin da ya ba Mustapha da Jamil mamaki, don a mamakancen suke kallon ta.

Ita kuma tana share hawaye, har lokacin Fatima dariya take yi.

Mustapha ya juya kan Fatima ya dan daure fuska yana fadin “Me ye haka wai? Ya tana kuka kina dariya, me kika yi mata?”

Da guntuwar dariya a muryarta ta ce “Ni ko me zan yi mata.”

Ta kai karshen maganar tata, hade da karasowa inda Umaiman take tsaye, ta kama hannun ta daya, kasancewar dayan ta dora shi a rabin fuskarta.

Jan ta, ta shiga yi zuwa falo, kan kujerar ta zaunar da ita, kafin ita ma ta, zauna a kan kujerar da ke fuskantarta tana dariya sosai.

Sai a lokacin Umaima ta dauki filon da ke kan kujerar ta wurgawa Fatima tana kuma share hawayenta.

“Haka kawai za ki ja min sharri, daga magana ki kama kuka. Sai kin ga kallon da Ya Jamil ke aiko min da shi.” Cewar Fatima cikin tsokana

Umaima na share guntayen hawayen lokaci daya kuma tana aikawa Fatima harara.

“Don Allah ba ki ji kunya ba? Kuka fa!”

“Wlh ban san na yi kukan nan ba, wani irin takaici nake ji a kasan zuciyata, don Allah ki ce ma wani daga cikin motar Abban Beauty ya fito ya koma motar wancan mutumin. Ni ba na son shiga motarshi, wlh da gaske nake yi.”

Baki Fatima ta kyabe kafin ta ce “Da yake ni ce mai baki hala, je ki fada musu.”

“Ni ba zan iya ba.”

“Au sai ni?” Fatima ta yi saurin katse ta kafin ta kara dorawa da “Ke ce ma fa kika rike abin da ya faru tsakaninku da Ya Jamil yasin shi ya ma manta na sani.”

“Tun da fa ba ni ce na yi mishi ba. Kuma har yanzu ai bai daina yi min wulakancin ba, ko gobe ya ganni a asibitin baya nuna ya sanni wlh, abun na ba ni haushi.”

Kafin Fatima ta yi magana Blessing ta turo kofar hade da sallama ta shigo, don bayan tafiyar Ƴan’uwanta su Hana ta tafi kaiwa makaranta a motarta sai lokacin ta dawo.

“An ce ku fito.”

Fatima ce ta fara mikewa tsaye, Umaima na bin ta a baya suka nufi kofa.

Sai da motocin suka fice, sannan Blessing ta rufe gate din, Fatima ta kama hannun Ihsan da Beauty ta koma ciki, ita ma Blessing bangarenta ta shige.

*****

Tun da suka fara tafiyar Umaima ta juya kanta daya bangaren, duk hirar da su Aunty Lamin suke yi tana jin su, amma ko motsin kirki ba ta yi bare ta tofa tata.
Sosai take mamakin Jamil yadda suke hira da su Aunty Lami. Kamar ba shi ba, ita bama ta taba jin maganarshi ba sai yau.

Misalin karfe 11am daidai suka iso Kaduna, sai a lokacin ne Aunty Lami ta ce Umaima ta rinka kwatantawa Jamil hanya, don har gida zasu kai ta.

A hankali ta rika gwada mishi hanyar har suka isa kofar gidansu, ita ta fito ta yi wa polisawan da ke kofar gidan magana suka bude musu kofa.

Su Aunty Hauwa ba karamin mamakin ganin haduwar gidansu Umaima suka yi ba, Ammi kuma ta karbesu cike da mutuntawa, basu wani jima ba, suka fito, suka dau hanyar Katsina, saboda a ranar Mustapha zai dawo, Katsina zai kai su ya juyo.

Yanzu hirar tasu a kan Umaima ne, yaba kyawawan halayenta kawai suke yi. Yayin da Jamil ya yi shiru yana sauraronsu.

Misalin karfe takwas na dare gidansu Fatiman shiru, sai haske da ya kawata tsakar gidan.

A can daki Blessing ce zaune ta tasa laptop din ta gaba, yayin da Ihsan ke kwance a kan lallausan center carpet din da ke tsakiyar dakin tana game.

A can dakin Fatima kuwa, ita ma zaune take gefen gado, yayin da yaran duk suke kwance a Saman gadon, Hana da Ziyad home work suke yi, Hassan, Husain da Beauty kuma wasansu suke yi, ita kuma Fatima chat take yi.

Jin karar shigowar motar Mustapha ya sa yaran fita aguje suna mishi oyoyo.

A can ma Blessing fitowa ta yi rike da Ihsan, jikinta sanye da wando baki, wanda ya kama jikinta, sai shirt ash color ta fito mata da kyawon surarta.

Fatima da ta bude kofa da niyyar fitowa, ganin Blessing sai ta koma ta zauna kan kujera.

Tana kallon yadda suka runguda zuwa part din shi, after 30mns yaran suka dawo wurin Fatima.

Tun tana taya su surutun da suke yi, har bacci ya daukesu a kan gadon ta.

Misalin 9:30pm Blessing ta buga kofarta, ta sanar mata Mustapha na kira.

Shiru ta yi a tsakiyar falon tana tuna abun yi, Blessing kananun kaya ta sanya, kuma sosai sun karbe ta, don tana da dire, ya kamata ita kuma ta zo da sabon salo.

Komawa ta yi cikin karamar akwatinta, riga da siket na atamfa masu kyau ta saka, daurin ture ka ga tsiya ta yi, wanda ya ba gashin ta damar bayyana, powder kawai da lips ta shafa sai kwalli, sai turaren lovely da ta gogo mai sanyin kamshi.

Blessing ce ta bude mata kofar, yayin da gabanta ya fadi sosai, tun lokacin da ta fara ganin Fatima take fama da wannan larurar har yanzu kuma ba ta warke ba.
Shi gar ta yi mata kyau, babu mai ganinta ya ce ta aje yara biyar. Saurin canjin da Fatiman ta yi yana ba Blessing mamaki.

Yau ne ta taba shiga dakin Mustaphan, da alama shi ma komai sabo ya zuba.

Daya daga cikin kujerun ta zauna tana gaishe da Mustapha hade da yi mishi sannu da zuwa, ya amsa a sake cikin hada baki ita da Blessing suka shiga gaishe da juna, dalilin da ya sa Fatima katse tata gaisuwar ta amsa ta Blessing din.

Dakin ya yi shiru bayan gaisuwar kafin Mustaphan ya katse shirun da cewa “Ku din ba bakin juna ba ne, ina alfahiri da ku, da kuma farin ciki da zaman lafiyar da kuke yi, zaman lafiyan da ke tsakaninku yana daya daga cikin matattakalar samun nasarata, a yanzu da zama yake kokarin hada ku wuri daya, don Allah ina rokonku da ku kara hakuri da juna hade da ninka zaman lafiyar da kuke yi.”

Duk suka yi shiru babu wanda ya yi magana, shi ya sa ya ci gaba” Fatima za ki karbi girki daga yau, za ki yi kwana biyu ƴar’uwarki ta amsa, sannan ba na son raba abinci, ko wacce ranar girkinta za ta dafa mana abinci, ba na son yara su bukaci abinci ace ba a gama ba, ba na, son yarana na zama da yunwa”

Ya karasa maganar duk yana kallonsu.

Jin sun kuma yin shiru ya ce “Akwai mai magana?”

Ku san a tare suka girgiza kai, alamun babu.

Daga nan sai kowa ya yi shiru, shi kam mikewa ya yi zuwa bedroom, ita ma Blessing sai ta dauki Ihsan dake bacci tana fadin “Sai da safe”

“Allah Ya kai mu” cewar Fatima a hankali.

Tana zaune a wurin Mustapha ya leko is yana fadin “Hajiya ko sai na shigo da ke don na lura yau sarautar uwargidan ce ta tashi, sai wani kasaita kike yi”

Karamin murmushi kawai ta yi, wani ba dadi take ji a can kasan kirjinta, kuma ta rasa me ye ainihin abin da yake damun nata.

Shi ne da kansa ya kamo hannunta zuwa dakin na shi, gefen gado ya zaunar da ita yana fadin “Yarinyar nan kullum kyau kike karawa, nawa za a siyar min da wannan kwalliyar?”

Ido ta dan juya kafin ta ce “ai ka biya.”

“OH really?”

Kai ta jinjina alamar kafin ta ce “Ban san kalmar da zan yi amfani da ita wajen gode ma ba Ya Mustapha.”

“Da na yi me?” ya yi saurin tambaya yana zama gefen gadon shi ma.

“Da ka fitar da ni kunya, daga jiya zuwa yau farin cikin da nake ciki ban san iyakarshi ba, ka canja min kayan daki, wadanda ban taba tunanin zan mallaka ba, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi, Ya kara maka arziki mai yawa mai albarka”

“Amin.” ya fada da sauri kafin ya ce “Ai Fatima duk abin da zan yi miki a yanzun dai wlh ban biya ki ba, tamkar dai ina biya miki bashin da kika ba ni ne a can baya, duk abin da ke faruwa a tsakaninmu na sabani ban mance alkairinki gare ni ba. Har Inna ta bar duniya tana fadin kada in bari ki wulakanta ke din ta gari ce. Kuma sha Allah ba zan bar hakan ta faru ba idan har ina numfashi. Kin yi min komai, kika auran tun ina almajirina, kika sayar da kayanki don karatuna, kika rike min kanwata, wacce ko yanzu na mutu idan har kina raye na san Ummi ba za ta yi kuka ba. Ina son Ummi da tausayinta fiye da yadda nake son su Hana da tausayinsu. Shi ya sa ba na wasa da mai kyautata mata, haka duk wanda ya kuntata mata yana cikin mutanen da zuciyata ke ƙi. “

” Har ma ka tuna min? ” ita ma ta tari numfashinshi.

” Me? Ya tambaye ta.

“Ummi ta ce tana son komawa makaranta ita ma”

Baki bude Mustapha ya ce “Karatu kuma, I amma ke kika sanya mata a baka ko?”

Karamar dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Allah dama na san haka za ka ce, amma babu ruwana”

Kallon da yake mata ne ya sa cikin dariya ta kuma cewa “Allah Ya Mustapha babu ruwana”

Mikewa ya yi tsaye, yana rage kayan jikinshi.

“Amma fa ke da ita akwai bambanci, ina za ta aje yarinyar?”

“Wannan ai ba matsala ba ce Ya Mustapha”

“To mijinta ya amince ne?”

“Bai san ma da maganar ba, ina jin a wannan karon ne ta fara tunanin.”

“Saboda ta ga kin canja ko, kin zama ƴar gayu, ba irin Fatiman da mai yawo da zane a kirji ba”

Kafin ta ba shi amsa ne ya shige toilet, hakan bai hana ta fadin “Ai mu da zama da zane a kirji amana ce, gaba muka ba shi ba baya ba.”

Ita ma fita ta yi zuwa wurin yara, amma ga mamakinta Blessing duk ta kwashe su illa Beauty da ta bar mata.

Ita ma sai ta yi shirin baccin ta koma dakin Mustaphan.

Ba Mustapha ba, hatta Fatima jin ta take yi kamar wata amarya, to komai sabo, da alama ma komai na dakin Mustaphan ita ce ta rare shi.

Bangaren Blessing kam dakyar bacci ya dauke ta, shi ma sai gab asuba, gaskiya kishi cuta ce mai zaman kanta, sannan ba karamin aiki ba ne, wata mace ta kwana da mijinka, babu abin da ka isa yi, sai dai fatan Allah Ya kara mana hak’uri da juriya.

Tana idar da sallah ta shiga shirya yara don zuwa school, har ta kai su, su Fatima basu fito ba, kila sun manta zuwan yara school.

Da Blessing ba ta yi niyyar zuwa wurin aiki ba, amma jin zuciyarta za ta iya fashewa ta sanya shirin tafiya wajen aikin.

Fatima kam sai karfe tara ta bude kofar ta fito, tana kokarin bude tata kofar Blessing ta fito cikin shiri, doguwar rigar atamfa ce a jikinta, hade zumbulelen hijab mai hannu, fari dogo har kasa, sosai ta yi kyau.

Tsayawa Fatima ta yi, suka gaisa da Blessing din yayin da su Hassan suka yo kanta, Ihsan ma sai ta taho.

Cikin danne kishin da take ji suka gaisa da Fatiman, sannan ta sanar mata za ta je wurin aiki.

Allah Ya kiyaye hanya ta yi mata sannan ta nemi da ta bar Ihsan idan dai ba za ta yi kuka ba.

Cikin fara’a Blessing din ta ce “sai dai a jaraba kam, dama gidan raino nake kai ta”

Fatima tsaye a bakin kofa tana kallon yadda Blessing ke takawa zuwa wurin motarta, karon farko da ta ji kwalliyar hijab ta burgeta.

Har Blessing din ta shiga motarta ta fice gidan cike da kwarewar tuki Fatima na kallon ta.

A duniyarta tana son ta ganta a cikin motarta, musamman ace ta ci kwalliya, kamar misalin Blessing a yanzu ko Umaima.

Sosai Umaima ma na burge ta, idan ta, sanya doguwar rigar nan ta nada veil din rigar, ta dafe kan sitiyari, sai ta ji ina ma ace ita ce.

Ko yaushe wannan burin nata zai cika oho.

Idan ta koma Katsina abu na farko da za ta, fara yi shi ne koyon tuki wajen Umaima, don ba zama wai an saci dan ɓarawo. Lokacin da motar za ta zo ta iya tuka ta. Da wannan tunanin ta shige dakinta.

Mustapha kuwa yana wanka ya ji fitar Blessing, wannan ya tabbatar mishi da kishin ya motsa, haka nan banza ba ta fita sai ta zo sun gaisa.

Shi ya sa yana fitowa wankan ya kira layinta, a lokacin isar ta farfajiyar ma’aikatar tasu kenan, tana ganin kiran na shi ta ki dagawa, har sai dai kiran na shi ya kara shigowa a karo na biyu, time din zaune take a kan kujera tana cika attendance book.

Shiru ta yi bayan ta daga kiran, shi ne ya ce “Amarya ba kya laifi, muna fada ne kika fita ba tare da na ga kwalliyar ba?”

Har cikin ranta ta ji dadin maganar ta shi, cikin sauri ta canja abin da ta yi niyyar fada da cewa “Na makara ne, kuma na dauka ba ka ta shi ba, amma za a yi ma wata idan na dawo.”

“OK thanks take care”

“I will” ta amsa shi hade da yanke kiran.

Ya sauke ajiyar zuciya, a fili ya ce “Na kashe wannan wutar, idan mutum na da mace sama da daya, sai ya zama munafiki-munafiki haka sannan za a zauna lafiya.

<< Daga Karshe 54Daga Karshe 56 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 55”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×