Zainaib da ta san shiriritar Fatima a gida, tana mamakin natsuwarta a makaranta, sosai take mayar da hankalinta gurin karatu.
Kamar wannan lokacin ma da tattara komai ta watsar ta fuskanci karatunta, tana son samun result me kyau da zai taimaka mata zuwa makaranta gaba da secondary.
Tana son zama malamar jinya ko ta makaranta, so take ta ji alert na shigar mata duk wata tana kashe matsalolin gabanta ba tare da ta jira miji ba, kamar dai yadda yan'uwanta mata kan yi.
Hankalinsu kwance su sanya sutturar da suke so takalmin da suke so, turarurruka, da sauran kayan. . .