Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Doctor Hassan by Rasheedat Usman

MAIDUGURI, BORNO STATE

Unguwar GRA

Fitowa ya yi daga toilet ƙugunsa ɗaure da towel, ɗaya kuma ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan jikin sa. Dressing mirro ya ƙaraso ya jawo table ɗin dake wajen ya zauna yana cigaba da tsame ruwan jikin sa, sanda ya tsame ruwan tas sannan ya ajiye towel ɗin a hanun bed, lotion ya jawo mai ƙamshin gaske ya fara mulke jikinsa dashi, sannan ya hau gyara gashin kansa shima da mayuka masu ƙamshi sanda ya mulke ko ina na jikin sa da lotion sannan ya ɗauki body spray ya dinga feshe jikinsa dasu sanda ya fesa kala uku kafin ya miƙe tsaye ya je drower ya buɗe ya ɗauko set ɗin kayan sa Blue Black ɗin wandon jeans ya saka tare da rigar suit fari yasa tare da ɗauko ribin dark blue ya ɗaura a wuyan rigar gyara kwalar rigar yayi sannan ya ɗauko suit ɗin ya saka , komai cikin nutsuwa yake yinsa sannan ya ɗauko takalmi sau ciki zama yayi bakin bed ɗin ya sunkuya yana ɗaura igiyar takalmin.

“Assalamu alaikum”

Ya ji sallamar ta, shuru yayi ba tare daya amsa mata ba ya cigaba da ɗaure igiyar takalmin, Sau uku take sallamar amma yayi banza da ita kamar baiji ta ba ya cigaba da abunda yake yi, sai a na huɗun ne ya amsa mata can ciki kamar wanda baya son Maganar nan ma sanin darajar Sallamar yasa ya amsa mata idan ba kana kusa dashi ba bazaka ji ya amsa sallamar ba, ita kanta ganin da tayi bakin sa yayi motsi ya sata fahimtar sallamar ya amsa mata, ƙarasowa tayi har gaban sa ta tsaya jikinta a sanyaye ta sunkuya tare da saka hanu zata karɓi igiyar takalmin ta ɗaure masa, yayi saurin bige hanunta yana cigaba da ɗaure wa, cikin sanyin jiki ta masa magana da Sweet voice ɗin ta tace.

“My Doctor breakfast is ready.”

Shuru Ya yi Still bai kulata ba, kuma sarai yana jinta sai ma ƙara haɗa fuskar sa da yayi tamau babu alamar annashuwa cikinta, ɗagowa yayi tare da ɗaukar agogon sa ƙirar gucci ya fara ƙoƙarin ɗaurawa a hanunsa, a karo na biyu ta ƙara cewa.

“I Say Doctor breakfast is ready please jiya ma fa haka ka kwana babu abunda kaci ko ruwan tea baka sha ba, haka ka kwana ya kamata kafin ka fice kasa ko da ruwan tea ne a cikin ka bana son kana fita da yunwa bana jin daɗin hakan.”

Ɗago lumshashshun idanunsa yayi masu kama dana mai bacci fuskar sa kuma a matuƙar ɗaure ya dubeta sannan ya fara magana cikin Slow VOICE ɗinsa da kuma faɗa faɗa.

“Wai meyasa ke mayya ce kam *FALMATA*!!!!, Meyasa kika addabi rayuwata ce, nace miki na tsaneki ki daina damun rayuwata ki daina shiga Cikin lamari na, Wallahi Falmata na miki tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam shiba, na tsaneki na tsani iyayen ki ina Zaune dake ne a dole Saboda kin zamo min ƙarfen ƙafa ba yanda zanyi dake, Banza ƴar Mayya, dan Allah ki fita a cikin rayuwata, nace bazan ci abincin ki ba ko ana dole ne Get Out of my room Mayya!!!!.”

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙofa, hawaye ne suka gangaro daga daradaran idanunta, ta ɗago tana kallon mijin nata cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, sunkuyawa tayi ta durƙusa da gwiwowin ta ta fara magana cikin rawar murya mai cike da alamun kuka.

“Karka min haka mijina Please ka daina hukunta ni da laifin da ba nawa ba, asali ma bani da hanu ciki, kana azabtar dani da yawa Doctor, kaine duniya ta, bani da wani farin cikin daya wuce naka, meyasa sanda ka koya min Soyayyar ka sannan zaka juya min baya, Ka ji tausayi na ka cire ni cikin LAMARIN GABAR CIKIN GIDAN MU TABBAS AN ƁATA ZUMUNCI amma ni meye nawa ciki da zaka juyawa Soyayyar mu baya, Ina soyyayar da kace kana min? Kaine fa ka ɗaukar min alkawarin cewa bazaka taɓa rabuwa dani ba komai tsanani komai wahala zaka tsaya tare dani, amma yanzu ka tsaneni lokaci guda, ina sonka MIJINA kaji ƙaina?”

Ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, tunda ta fara Maganar ya zuba mata Lumshashshun idanunsa yana mata kallon tsana da kuma tausayi sanda ta dire maganar tukunna Yaja tsaki mai sauti sannan ya sunkuyawa ya ɗebi wayoyinsa dake bedsite drower da key ɗin motar sa ya juya da niyar ficewa ba tare daya tanka mata ba, yaji ta riƙe ƙafafunsa, Runtse idanunsa yayi sanda yaji hanunta a jikinsa, Yana jin wani abu na yawo tun daga babbar yatsar sa har cikin kansa tsayawa yayi cak.

“Please My Doctor ka taimaki Rayuwata ka tausaya min, Ka dawo da Soyayyar mu ka ji ƙaina, Wallahi zuciyata ciwo take min, karka bari na mutu ta sanadiyyar ka kaine gata na, kaine rayuwata ina sonka DOCTOR.”

Cikin jin wani ƙarin tsanarta ya saka ƙafarsa ya shure ta da ƙarfi sanda ta bige kanta da jikin bed, da sauri ya saka kansa ya fice daga cikin bedroom ɗin, kanta ta riƙe tana jin yana mata zafi, hawaye kuwa wani ne yake bin wani saman fuskar ta, sosai take kuka harda shashsheƙa, takurewa tayi a gefe tana cigaba da kuka zuciyarta kuma cike take da baƙin ciki, Duniyar gabaki ɗaya ji take ta isheta, kullum baƙin ciki shine abokin hirar ta, ta rasa farin cikin ta tun sanda wannan mummunan ƙaddarar ta afku tsakanin mijinta d iyayenta, mijinta mai tsananin ƙaunar ta wanda ada baya son ɓacin ranta wanda kullum shine abokin hirarta shine amininta, shine mai share mata hawayenta amma yanzu shine mutumin daya fi kowa tsanar ta, shine ya maida ita ABOKIYAR GABAR sa, Tabbas rayuwa ta juya mata ba tunda har ta shiga tsakanin ta da mijinta, sanda taci kukan ya isheta sannan ta tashi ta goge hawayenta, ta faɗa saman bed ɗin nasa tana ajiyar Zuciya, rigarsa daya cire ta rarumo ta rungume a ƙirjin ta, tana shaƙar ƙamshin turaren sa, ji take tamkar shi ta rungume, sai famar ajiyar Zuciya kawai take, tana nan rungume da rigar har bacci ɓarawo yayi nasarar sace ta tana sauƙe ajiyar zuciya.”

Shi kuwa yafi 30 minute yana zaune cikin motar ya ɗaura kansa jikin matuƙin motar pictures ne ɗan ƙaramin elagment a ajiye cikin motar, Sosai yake ƙarewa pictures ɗin kallo kafin yasa hanunsa ya shafa sa hawaye ne yake tsiyaya saman fuskar sa, AUNTY JALILA DA UMMAN SA sune kawai suke masa yawo a cikin zuciyarsa shikenan ya rasa AUNTYN SA DA ABBAN SA anbar UMMAN SA kuma cikin jinya, taya zai iya yafe musu bayan ya rasa farin cikin sa duk ta sanadiyyar su, ya daɗe zaune cikin motar kafin ya ɗago kansa ya goge hawayen sa, motar yayiwa key, ganin tahowar sa yasa mai gadin saurin wangale masa makeken get ɗin gidan, Yana ɗaga masa hanu, shima hanun ya ɗagawa Baba mai gadi ya ciro kuɗi dubu goma ya miƙa masa cikin sanyin halinsa yace.

“Gashi Baba kuɗin da na maka alƙawari jiya kayi hkr 20k nayi niyyar baka, so yanzu babu kuɗi a gida gaskiya dole sai na biya bank na ciro, so kayi hkr da wannan sai kaje ka fara Siyan maganin kafin na ƙara maka wani abu.”

Yana godiya baba mai gadi ya amsa yana cewa.

“Mai yawan kenan ranka shi daɗe na gode sosai Allah ya ƙaro zumunci ya tsareka ya bawa Umma lafiya na gode.”

Murmurshi kawai ya masa tare da amsawa da Amin kafin ya fice daga cikin gidan rufe get ɗin Baba yayi sannan ya zauna saman tebur ɗinsa yana cewa.

“Oh ni iro har yanzu wannan yaro yaƙi sakin jikinsa tunda wannan al’amari ya faru kullum yana cikin damuwa, babu walwala kwatakwata a fuskar sa, duk da shi ba ma’abocin dariya bane amma ai kullum fuskar sa ɗauke take cike da haiba da kuma murmurshi, Allah ka daidaita lamarin waɗannan bayin naka, Allah ka kawo ƙarshen wannan lamarin ka bawa Mahaifiyar wannan bawan naka mai tausayi da jin ƙan na ƙasa dashi lafiya ka bayyana masa ƴar uwarsa da mahaifinsa, itama Hajiya ko zata samu farin cikin ta ya dawo kamar da mace mai tausayi da kyauta tana cikin damuwa.”

Ya ƙarasa maganar yana ajiyar Zuciya.

Shi kuwa doctor titi ya harba yana dreving a hankali, zuciyarsa kuma cike da ƙunci kwatakwata ya tsani dosar family Hause ɗin nasu sai dai babu yanda ya iya dole ya kamasa yaje tunda akwai Umman sa kwance babu lafiya, ringine ɗin wayar sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, kallon sa ya kai kan screen ɗin wayar yaga sunan IB ya bayyana hanu yasa ya ɗaga wayar tare da cewa.

“Ina sauraronka IB.”

Murmurshi IB Yayi daga can kafin yace.

“Kana ina ne yanzu Doctor.”

A taƙaice ya basa amsa da cewa 

“Ina hanya zanje family Hause wani abune yake faruwa.”

“Okay to shikenan idan ka fito daga Family Hause sai ka samu ka biyo Hospital domin kuwa akwai matsala wacce jiya doctor Saif ya mata oppretion sun bata ruwa tasha daga farfaɗowar ta cikin ya ɗan hau.”

Da ƙarfi Ya furta.

“What!!!!! Suka bata ruwa tasha mahaukatan inane su, bayan sanda na gargaɗe su da cewa karsu bata komai tasha idan ta farfaɗo mtssssss!!! Ka bani 30 minute ina zuwa insha Allah bari naje na duba Umma amma ka kira DOCTOR Saif yanzu maza ku shige da ita ɗakin operation nima ina zuwa.”

“Okay ba damuwa Allah ya kawo ka lafiya.”

Kashe wayar doctor Yayi yana tsuka tare da furta ” wasu mutanen sam basu da hankali” a haka ya shigo cikin unguwar tasu ta BULUN KUTU TSALLAKE wani ƙofar gida na gargajiya yayi parking ƙofar gidan cike yake da Dattawa suna zaune a babbar taburma sai wani Dattijo dake zaune a saman farar kujerar roba da alamu dai wannan gidan na sarauta ne irin sarautar cikin unguwa, fitowa Doctor Yayi ya tako zai shige cikin gidan, sai ya hango Kawu Dauda, da har zai wuce ba tare daya nufi wajen da dattijan ke zaune ba, sai kuma ya dawo yazo ya sunkuya cikin sanyin muryar sa yace.

“Kawu Dauda sannu da hutawa”

Tare da miƙa masa hanu sukayi musabaha gaisawa yayi da sauran dake zaune bai ɗaga kai ya kalli wannan dattijon dake zaune a saman kujerar ba, wanda fuskar sa take naɗe da rawani, ya miƙe zai shige cikin gidan yaji muryar kawu, Dauda yana ce masa.

“HASSAN baka da hankali ne, baka ga BAFFAN KA bane baka gaishe sa ba,ko ka manta dashi ƙanin ubanka ne kasa kai zaka wuce, rashin ɗa’a fa ba halin ka bane naga yanzu ka ɗauko wani halin banza wanda a baya baka dashi.”

Shuru Doctor Yayi yana tsaye yana sauraran Kawu Dauda, sai da ya ƙarasa maganar tukunna sannan ya saka kai ya shige da sauri ba tare daya tankawa Kawu Dauda ba domin kuwa bazai iya gaishe da wannan baƙin azzalumin ba, Kawu Dauda duban wannan mutumin yayi yace.

“YALLAƁOI kayi hkr na rasa ya akayi Hassan yafi kowa ɗaukar wannan lamarin da zafi, duk da nasan yana da zafin zuciya, amma abun nasa yayi yawa insha Allah zan masa faɗa komai zaizo ƙarshe zai gyara.”

Gyara zaman sa yayi wanda aka kira da yallaɓoi ɗin, sannan ya fara magana.

“Karma ya gyara dan ubansa idan sunga dama su cigaba da gaba damu daga su har yan uwan nasa har duniya ta tashi, ɗan banza wanda ya yi gadon tsiya a wajen uwarsa kuma wallahi idan sukayi min iskanci sai na kore su daga cikin gidan naga uban da zai dawo dasu.”

Gabaki ɗaya dattawan dake wajen kallon sa suke cike da mamaki, wai zai koresu daga gidan nasu, gidan su na gado da aka haifesu tun kaka da kakanni ikon Allah lallai ZUMUNCIN wannan gidan ya lalace, Kawu Dauda dai baice komai ba.

DOCTOR da bai ƙarasa shigewa bane yaji Abinda yake cewa ya dawo cikin sauri da ɓacin rai.

Jin muryar sa sukayi yace.

“Idan an fasa korar mu daga cikin wannan gidan kun raina Allahn daya halicce ku, idan ka isa kai mai iko ne da faɗa aji dan Allah karka barmu mu kwana a cikin gidan nan ya idan kuma ka barmu muka kwana baka ci sunanka ABUBAKAR ba mtsss…”

Yana ƙarasa maganar yayi shigewar sa cikin zafin rai gabaki ɗayan su kallon mamaki suke bin DOCTOR HASSAN dashi Lallai ɗan zaki ya girma.

Kawu Dauda ya furta tare da tashi ya bar wajen, yana Allah ya kyauta, shi kuwa wannan bawan Allah zuciyarsa takai har wuya domin kuwa gani yake Hassan ya tozarta sa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Doctor Hassan 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×