Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Doctor Hassan by Rasheedat Usman

Shigar sa tsakar gidan ya samu sai famar dambarwa ake, tare da cacar baki, MAI KANTU ta dage sai famar lailayo ashar take tana makawa yayin da FANNA take maida mata da zagin, da yawa daga cikin mutanen gidan sun fito sunyi carko-carko suna kallon faɗan, Doctor tsayawa yayi turus yana kallon su cike da ɓacin rai, wani irin mungun kallo yake jefawa ƙanwar tasa FANNA da ta tsaya harta biye wannan Yar barikin marar mutunci Iya mai kantu, cikin tsawa yace.

“Keee!!! FANNA maza zoki bar nan ko kuma na ƙaraso na taka miki wuya a wajen, ban hanaki faɗa da JAHILAI BA oya shige daga wajen.”

 Ya faɗawa FANNA Still Yana jifanta da mungun kallo bakin ta FANNA ta tura sai kuma idanunta suka ciko da hawaye cikin rau rau da ido tace.

“Yaya Umma na fa suke zagi tun ɗazu ita da KALTI YA GANA (KALTI yana nufin Umma ƙanwa ko kuma yar Mahaifin ka) shikenan yaya sai nayi shuru na barsu suna zagin Umma sai kace wanda banda Zuciya.”

Runtse idonsa kawai yayi cikin ƙunar rai da kuma tsanar family ɗin nasu, ya tsani zuwa gidan saboda, gutsiri tsome da baya karewa a cikin gidan, cikin sanyin muryar sa yace.

“Shifa jaki duk yanda akayi dashi sai yaci kara sannan kuma ai shi jahili bazai taɓa yin aiki irin na masu hankali ba dan haka wannan ya daina damunki duk wanda ya zagi uwar wani uwarsa ya zaga shige mu tafi.”

Wani raɗaɗin Maganar Doctor Hassan YA GANA DA MAI KANTU suka ji, cikin takaici ta tashi ta dinga surfawa Doctor magana, wanda shi bai san ma tana yiba tuni yasa FANNA a gaba sun shige part ɗin mahaifiyar tasu.

“Ka faɗawa Uwarka YAMURAN tana can tana kwance naɗe baƙin ciki ya kusa kashe ta itace jahilar ba muba, ɗan iska marar kunya, ina matsayin ƙanwar ubanka ko kunyar kira na jahila bakayi ba, marar mutuncin banza.”

Yagana ce tace.

“Kinga fa kumfar bakin banza kikeyi Mai kantu, shifa ya shige sashin Nakassashiyar uwar tasa, dama kin rabu dasu baƙin cikin su shine zai kashe su, kinga ni kizo ma ki rakani wajen Uwar marassa Zuciyar nan Falmata akwai maganin da Aunty YANA ta bani na kai mata, ko zata samu ɗan Iskan mijin nata Hassan ɗin ya sassauta mata jeki ɗauko mayafin ki mu tafi.”

Taɓe bakin ta Mai kantu tayi, tare da cewa.

“Ni babu inda zani, Waye zai sassauta matan wannan ɗan Iskan mijin nata mai zuciyar fir’auna shine zai sassauta mata, wanda muma da muke ƙannan Ubansa bai ɗaga mana ƙafa ba bare kuma Matar sa kina gani yanzu fa ya gama faɗa min magana, ita dai Falmata ta gamu da Wahala tunda tace ita bazata rabu dashi ba, tana kuma tare da Wahala dan ubanta, idan Soyayya zata biye haka zata ƙare cikin nadama da zubda Hawaye saboda ta gamu da ɗan iskan miji, dan haka ku ƙyaleta wannan Uban Yan taurin kan tsiyar ma, Asiri ba kamasa yake ba, dan haka kuma daina wahalar da kanku a banza ni ba inda zani na wahalar da kaina da yawun baki na a banza ita ba ganin laifin mijinta take ba kina mata magana zata fara karesa tana ɓata rai ita a dole bata son ana zagin mijinta, shegiya wai ita SOYAYYA a zamanin yanzu ana daka ta soyayya ne, Soyayyar banza Soyayyar wofi yanzu ina Soyayyar take da zaki taɓa tunanin zai wulaƙanta tane, gashi yanzu wahalar take famar kwasa kullum yana gasa mata gyaɗa a hanu ita kuma marar zuciyar banza sai famar liƙe masa take kamar ruwan gam.”

“Himm!!! Kinga Aunty Yana ba yadda zatayi ba, domin kuwa ta rantse da Allah sai ta, dawo da Hassan tafin hanunsu tace shiɗin ma da yake tausayin uwar tasu, nan gaba koda kallon inda take bazaiyi ba, kinga nifa ƴar aika ne, ganan laya dai ta bani tace naje a saka masa ƙarƙashin katifar sa, kuma kinga yanzu ne dai-dai sawa baya cikin gidan kinga bari ma kiga na tafi tunda ke bazaki ba.”

Yagana ta ƙarasa Maganar tana tashi, taɓe bakin ta Mai KANTU tayi tare da cewa.

“Hmm!!! Sai kuje kuta fama da sassaƙar da babu ranar gamata su dai iyayensa kunyi nasarar ganin bayan su, amma shi kam abune mai kamar wuya domin idan juninki sammako ne, to kuwa da alama shi a hanya ya kwana, kinga tafiyata.”

Ta ƙarasa maganar tana barin wajen, Yagana kafaɗarta ta ɗaga sannan ta shige part ɗin Yana mahaifiyar Falmata.

Doctor da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, *AJIRAM* ne ta amsa tana cewa.

“Sannu da shigowa Yaya.”

“Yauwa sannu AJIRAM Umman bacci take ne.?”

“Ehh yaya Bacci ne ya ɗauke ta, amma gaskiya yau tana fama da Matsalar Numfashi, jiya munyi magana da BELLO yake sanar dani akwai wani Dattijo mai bada magani a ƙauyen *BINISHED* ance yana bada magani sosai akan matsalar ciwon da aka rasa kansa, shine nace ko za’aje a gwada ko Allah zaisa a dace, tunda ciwon nata ba na asibiti bane, sannan ance yana bada taimako sosai mussaman ga mutanen da suka ɓata aka nemesu aka rasa, kaga sai mu masa zancen ɓatar Baba da Jalila ko Allah Zaisa mu dace.”

Shuru Doctor Hassan yayi yana kallon Umma dake kwance tana jan Numfashin ta da ƙyar, sosai yake jin tausayin Mahaifiyar tasa wani sa’in idan ciwon ya tashi mata kamar ciwon hauka haka zata dinga fisgar gashin kanta tana ƙoƙarin ciresa daga kanta ko kuma ta dinga ƙoƙarin zata cire kayan jikinta, wani sa’in kuma numfashin tane yake ɗaukewa, ajiyar Zuciya ya sauƙe yana duban AJIRAM yace.

“Okey zan tuntuɓi bellon naji yanda abun yake, idan har malamin Allah da Annabi ne bana shirka ba, to zamuje mu gwada, zamu kai Umma koma inane muddun zata samu lafiya, Allah ya baki lafiya Umma yasa ƙaffara ne, Allah ya yassare miki wannan ciwon Umma na.”

Ya ƙarasa maganar cike da tausayin halin da mahaifiyar tasa take ciki sannan ya jefawa AJIRAM tambaya.

“AJIRAM yaushe zaki koma gidan ki ne, dan ya kamata ki koma kar mijinki ya ga kamar mun masa rashin adalci, zan ɗauko *HAJJO* zata zo ta zauna da Ita kafin Allah ya bata Lafiya tunda ita tana zaune a gida babu aure mijinta ya rasu ina ga hakan zaifi ko, ni dama *HAJJA MERO* ta bani izini tuni da na mayar da ita gidana, to ta hana na rasa me wannan tsohuwar take nufi.?”

AJIRAM duban ɗan uwannata tayi cike da tausayin kansu tace.

“Yaya idan banyiwa Mahaifiyata jinya ba, waye zai Mata, shima idan har ya kasa min uziri akan mahaifiyata, bai min adalci ba, mu Huɗu ne kawai ƴaƴan data haifa daga Aunty Jalila sai kai saini sai kuma FANNA kai namiji bazaka iya mata jinya ba, domin ba komai bane zaka iya mata a matsayin ka na namiji, FANNA kuma tayi ƙanƙanta ga ɗaukar ɗawainiyar jinyar mahaifiyar mu, kaga dole ne a kaina, na jinyace ta, Amma babu damuwa idan har HAJJO zata yarda domin kuwa duk ɗaya muke, tunda itama hajjo Ƴace a wajen Umma, ƴar ƙanwar Umma ne, kaje ka tuntuɓeta idan ta amince sai na koma gidan nawa amma dole kullum nazo na dinga duba umma.”

Numfashi Doctor ya sauƙe yace.

“Hmmm!!! Ba damuwa insha Allah Hajjo bata da matsala zata amince, mu cigaba da addu’a Allah ya kawowa Umma sauƙi cikin gaggawa.”

“Ameeen yaya, FANNA tashi ki ɗauki tsintsiya ki share cikin gidan nan.”

Da to FANNA ta amsa sannan ta tashi ta ɗauki tsintsiya ta hau shara, Doctor Hassan tashi yayi tare da ciro kuɗi masu yawa ya bawa AJIRAM yace.

“Gashi ki riƙe a hanunki ko akwai Abunda zaku buƙata koda bana kusa, munyi magana da malam Sani ga wannan kuɗin kuma ki basa, yace zasuyi sauƙar ƙur’ani gobe suna so zasuyi yanka sai ki basa idan ya aiko, sannan ki tabbatar kin bata maganinta da zarar lokaci ya cika, Bari naje na gaishe da HAJJA daga can zan wuce Hospital insha Allah zuwa dare zanzo naga jikin nata.”

“To yaya a dawo lafiya Allah ya tsareka.”

“Ameeen AJIRAM.”

A tsakar gidan ya tsaya tare da kamo kunnen FANNA ya murɗe, ɗan ƙara ta saki sakamakon jin zafin da tayi, cemata yayi.

“Ke ba!!! Ina baki jin magana ta ko, nace ki daina biye musu kuna hayaniya baki ji ko, to daga yau na sake jin kunyi faɗa da wani cikin gidan nan, ko ranki sai ɓaci, kinji ko bakiji ba.”?

Ya mata Tambayar yana zaro mata Ido tare da sake mata kunnen, bakin ta ta tura tace.

“Naji yaya bazan sake ba.”

Ficewa yayi, FANNA ta tura baki tana cewa.

“Allah bazan ƙyale duk wanda ya zagi Umma na, ba sai dai ka kasheni yaya amma duk wanda ya zageta nima sai na zagesa ehe.”

Sashin su matar tasa ya nufa wajen kakarsu mahaifiyar Baban su, wanda take zaune sashin su matar tasa, *AUNTY YANA* tana zaune ita da Mairama tana tankaɗen garin tuwo, ya shigo ko Sallama babu, kansa tsaye zai shige ko inda suke bai kalla ba, ɗago kanta Aunty yana tayi ta dubesa cike da jin haushin rainin daya mata, kamar ba Uwar matar sa ba, ɗafa tayi tare da girgiza kai ta tashi tare da tare gabansa tana cewa.

“Tsaya ƙaramin marar kunya, marar mutunci”

Tsayawa Doctor Yayi ba tare daya kalleta ba, nan ma ya tsaya ne saboda ta tari gabansa, hanu ta miƙa masa tare da cewa.

“Bani Takardar sakin ƴata, mun gaji da Auren tsiya Auren da babu mutunci Auren tarkace dan haka sakar min ƴata idan kana da zuciya nacaccen banza kawai marar zuciya.”

Runtse idonsa Doctor Yayi yana jin wani irin tsanar surkar tasa yana ƙara shiga cikin zuciyarsa, gefen ta ya matsa zai raɓe ya shiga ta ƙara matsawa ta taresa tana cigaba da cewa.

“Nace ka Sakar min ƴata ko, kai wani irin marar zuciya ne kam, ka saketa, ta fara gajiya da ganin baƙin cikin ka, dan wallahi bazan tsaya na zuba ido ina kallo ka kashe min yarinya ba, Dan haka sakar min ita.”

Dariya maganar ta, taso bawa Doctor, idanunsa ya ɗago da suka sauya kala ya fara mayarwa Surkar tasa magana son ransa kamar wanda yake magana da sa’arsa, wannan shine karo na farko daya fara kiranta da sunanta darect ba tare daya lulluɓe ba.

“YANA ya kamata zuwa yanzu ace kin fita a hanya ta, ki daina garajen tare min gabana domin kuwa daf nake dana tureki ki faɗi har ƙasa muddun baki fita cikin rayuwata ba, ƴarki kuma nace bazan saketa ba, sai randa ta yanki jiki ta faɗi hawan jini ya kayar da ita ko kuma ciwon zuciya ya kamata, a wannan ranar sai kizo zan baki takaddar ƴarki, sannan ina miki Albishir da cewa yanzu ma FALMATA ta fara ƙunsar baƙin ciki a cikin gida na.”

AUNTY YANA sake baki da hanci tayi tana kallon Doctor, wai yau ita HASSAN yake kallon tsabar idonta yake faɗa mata maganar da yake so, mutumin da a baya yake mata biyayya tamkar uwar da ta haifesa yau shine yake neman zaginta haushi ne yasa ta cakwami wuyan rigarsa tana cewa.

“Idan ka fasa yasar dani a ƙasa ka raina Uwarka *YAMURAN* kuma wallahi dole sai ka sakar min ƴata ko kaƙi Allah.”

Murmurshi yayi yana duban hanunta dake riƙe da rigarsa, zuciyarsa tana tunzurasa daya tankaɗeta kawai ta faɗi ƙasa, HAJJA dake cikin ɗakinta ne taji hayaniyar AUNTY YANA ya sata fitowa da sauri, tsayawa tayi tare da riƙe baki ta rafka salati tare da tafa hanu.

“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!!! Ni Mero yau kuma ina ganin wani baƙar lalacewa wai Surukace ta riƙe wuyar rigar Mijin ƴarta, Lallai Yana baki da ta ido, ta sakesa kafin na ɓata miki rai shashancin banza kawai.”

 Aunty YANA ƙin sakar masa riga tayi tana jijjiga tace.

 ” Allah HAJJA bazan sakar masa riga ba sai ya Bani takaddar FALMATA tunda ba ƙanwar uwarsa bane sai ya Rabu da ita ai, akan me zai zauna yana wahalar min da yarinya dan ubansa shi wayee.”

 Doctor leɓen bakin sa ya cije yana kallon AUNTY YANA kallo na tsana da kuma wulaƙanci, kafin ya dubi HAJJA yace.

 ” HAJJA idan wannan matar bata sakar min riga ba ko, to wallahi za’ayi mummunan abun kunya yau a cikin gidan nan domin kuwa zan hankaɗa matar nan hankaɗar da idan ta faɗi wallahi sai ta karye sannan ta daina zagin ubana yafi ta ita da wannan shashashan mujin nata daraja da mutunci.”

 HAJJA cike da haushi da kuma fara gajiya da masifar iyalan gidan nasu ta taho tana cewa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Doctor Hassan 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×