Skip to content

Duhun Damina 16

Cikin mutuwar jiki yake sarrafa motar, zuciyarsa ya karye, yana jin kamar babu jini a jikinsa.

Tun bayan amsar da ya karɓo daga wurin likita, da bayanan da ta yi ta zafga masa wanda zai iya cewa kashi ashirin kawai ya shiga kwanyarsa, yake jin babu wani abunda yake masa dad’i.

Sai a sannan ya ji gwanda da Juwairiyya ta ƙi zuwa tare dashi, da tana nan, bai san ya labarin zai shigeta ba.

Ƙarar wayarsa yake ji, amma baya tunanin zai iya ɗauka, musamman da ya gane ƙiran daga matarsa ce, wacce ke gida tana jiran zuwansa gareta da amsar da tuntuni take son samu.

Maganar da yake bakinsa ba magana ne da zai iya fad’uwa a waya ba, ba magana ne da zai iya sanar da ita ba tare da yana kusa da ita ba. 

Magana ce mai muhimmanci, wanda ya shafi rayuwarsu gaba ɗaya.

Bai san lokacin da ya iso gida ba, duk da dai a saninsa bai yi k’wak’k’waran gudu ba, amma gani yake ya iso da wuri.

Parking ya yi bayan an bud’e masa gate, bai iya fitowa da wuri ba sakamakon bugun zuciyarsa da ya tsananta, ga wani ciwon kai da ke ɗawainiya da shi.

Mintuna biyar ya ɗauka kafin ya fito, yana mai ɗauko dukkan takaddun da aka bashi yana rungumewa.

***

A falo take zaune cikin tagumi, ta yi nisa cikin tunaninta, bata ma ji dirin motarsa ba bare ta ji shigowarsa ciki.

Ta kai ƙololuwa cikin tsoro, bugun zuciyarta da fargabanta ya tsananta tun da ta ga ya ƙi ɗaga wayarta.

Bata san da shigowarsa ba sai da ya matso daf gareta, yana iya ƙok’arinsa na kare kansa da nuna mata damuwarsa ta saman fuskarsa.

Cikin hanzari ta mik’e, tana mai tsayawa daf da shi tare da tambayarsa dalilin ƙin ɗaga wayarta.

Ta sani, ba amsar take son ji ba, tsoron tambayarsa sakamakonta take, amma ya zata yi? Dole ta samu amsarta a yau, wanda a tunaninta rayuwar aurenta ya ta’allak’a da wannan sakamakon.

Murmushi ya sakar mata, wanda farat ɗaya bazaki ce na yak’e ba ne, saboda duk dauriyarsa da ƙarfin halinsa ya tara sannan ya jefeta da wannan murmushi.

A ranta ta ji tsoronta da fargabanta ya ragu, sai dai da ta sa ido a fuskarsa ta kula da dukkan yanayinsa, sai ta tabbatar da cewa ƙarfin hali ne kawai, akwai abun da yake ɓoye mata cikin murmushin nan nasa.

“Lafiya? Baka amsani ba. Ka san kana tsoratani da shirunka ko?”

Hawaye ta ji ya ciko idanunta, ita kanta bata san dalilin zuwansu ba. Samun kanta ta yi da zubar da hawayenta saman kuncinta.

Hannunta ya rik’e, yana ci gaba da ƙak’alo murmushinsa.

“Tell me, ba za ka yaudareni da murmushin nan naka ba. Ka sanar da ni kawai, babu anfanin ɓoyewa”.

“Kuma shi kenan baza a barni in yi enjoying wannan lokacin ba? Come closer babe, ƙamshinki ya min dad’i”.

Ya ƙarashe maganar ne yana ajje takaddun a gefe guda ya had’eta da jikinsa, ba don komai ba, sai don son samun nutsuwar da ya bar jikinsa tuntuni.

Bai bata damar bijire masa ba, duk yanda ta yi dan ta kaucewa rik’onsa ta kasa. 

Hawayenta tuni suka ƙara gudun sauk’owa, suna mai rige-rige da junansu. 

Sheshshek’a ta fara, tana jin malulun da ya mak’ale mak’ogoronta na tsikararta.

Bai kulata ba, saboda a wannan lokaci, shi ma ya rasa dukkan kuzarinsa, ƙarfinsa da ma dukkan juriyarsa.

Sautin kukanta ya tsananta, bazata iya jurewa ba, jin mijinta a haka, ta tabbatar wa kanta sakamakonta bai yi kyau ba. 

Bayanta yake shafawa a hankali alamar rarrashi, ya kasa sarrafa harshensa, bai san ya zai yi da labarin da ya ke bakinsa ba, bai san ya zata yi idan ta ji zahirin bayanansa ba.

“Ka sanar… Ka sanar da ni. Nice bana haihuwa ko? Ka amsa ni ka hutar da kanka, ka amsa ni dan Allah”.

Cikin tsananin kuka ta iya maganar, kanta na bisa ƙirjinsa, majina da hawayenta duk yana malala kan suit ɗin jikinsa.

Yawu mai tauri ya had’iye, hawayen da ya ciko idanunsa na barazanar sauk’owa.

“Calm down Babe, ba abunda kike tunani ba ne”.

“Me ne to? Me yasa ka kasa furta komai a kan abunda ka je karɓowa? Me yasa duk jikinka da fuskarka ya nuna ba lafiya ba?”

“Juwee, ni ke da matsalar, trust me everything will be fine, ki kwantar da hankalinki”.

Cak kukanta ya tsaya, tana had’e kalamansa cikin kwanyarta.

Jikinta ta b’anb’are daga nasa, tana kallonsa cikin mamaki.

“What? Kai ke da matsala kuma?”

Iska ya hura ta tsakanin lebb’ansa, ya rik’o hannayenta yana mai ƙara mata ƙwarin gwiwa da idanunsa.

“Listen Babe. Da ni da ke, muna da same problem”.

“Ban gane ba, ka min dalla-dalla”

Ta buk’ata idanunta cikin nasa.

Kujerar da ta tashi a kai ya mayar da ita yana zama gefenta, hannunta bai bar cikin na shi ba ya shiga yi mata bayani kamar yanda likita ta sanar da shi.

“Kin ga ko, ehmm, results namu da ya fito ya tabbatar da cewa kwayoyin haihuwarmu ya yi raunin da sai da taimako zamu iya samun abunda muke buk’ata.

Kuma ba ke kad’ai ba Babe, da ni da ke ne dukka. But InshaAllah zamu samu lafiya, ta tabbatar min cewa in muka bi ƙa’ida komai zai wuce. Ki daina ɗaga hankalinki”.

Idanunta ta runtse, tana jin tashin hankalinta na ninkuwa. A yau da ta tabbatar da hasashenta, tana jin ina ma ranta a ka ɗauke?

Ina ma za a mayar da ita baya ta gyara laifukanta? 

Hawayenta zuba suke kamar bakin famfo, zuciyarta na zafi kamar an sa mata barkono. Tashin hankalinta ya wuce tunanin duk wani mahaluk’in da ke numfashi a doron ƙasa.

Kalaman mijinta, bai ƙara ko rage komai daga yanda take ji ba. Ko da yake, bata tab’a ɗaura masa samun wannan sakamakon ba, wata ƙila jin nasa sakamakon ya ƙara dagula dukkan lissafinta.

K’wayar idanunta ta ɗaura a ƙasa, tana jin rarrashin da yake mata cikin kunnuwanta, yana ƙarawa da kalamansa na tabbacin samun lafiyarsu, sai dai ita, bata ɗauki ko guda daga ciki ba. Wannan shine jarabawanta, jarabawa mai wahalar gaske.

Bata tab’a ɗauka haka zata ji in an tabbatar mata ba za ta samu haihuwa ba. Ashe haka iyaye mata da Allah bai basu haihuwa ba suke ji? Ashe haka zafin aikata haram yake?

Ashe haramtawa mijinta kanta na iya kawo masa matsalar da babu mai warkarwa sai Rabbil izzati?

Ta yi kuskure, ta cuci kanta kuma ta cuci mijinta.

“Ban san aikina zai kawoni nan ba Abdulwahab,da ban yi ba. Wallahi da ban aikata wannan kuskuren ba”.

Muryarta ya dashe, muryarta ya yi rauni. Kuka ya ci ƙarfinta, amma ta shirya da samun hukuncin laifinta. 

Bayan wannan sakamakon da ta ji a yau, bata tunanin akwai wani abunda zai ƙara girgizata, komai ya zo, zata iya ɗauka a tunaninta.

Idanunta ta ɗaura a nashi, tana goge hawayenta, duk da sabbi na ci gaba da sauk’owa.

Kallonta ya ke yi ba tare da ya gane maganar da take son isar masa ba.

Daga sama ya ji ci gaban kalamanta, wanda zai iya rantsuwa, zuciyarsa bata tab’a bugawa irin lokacin da kalamanta suka shiga dodon kunnensa kuma ya fahimta ba.

“Istimna’i ke kawo hakan, i mean masturbation”.

Kallonta yake yi, bugun zuciyarsa na tsananta.

Ina ta sani? Me yasa take magana kamar ta san yana aikata istimna’i? Me ma take nufi? 

Kwata-kwata ya kasa gane manufarta, ya kasa gane maganar da take son sanar da shi.

Bai iya cewa uffan ba, ta ci gaba da yi masa bayanin da ta tabbata zai shiga kwanyarsa, kuma ya ajje hankalinsa ya gyara kurensa.

“Eh, ina nufin duk mai yin masturbation hakan na iya faruwa da shi, musamman kai da ke namiji, masturbation na sa sperms rauni, haka zalika yana bawa organs ɗin da ke sarrafa kwayoyin haihuwar wahala, inda daga nan zasu fara samun matsala su ma su yi rauni. Hakan kuma yake a gareni ni da nake mace.”

Kamar yanda kalamanta suka mata nauyi, haka harshenta ya mata nauyi yana sark’ewa, kukanta na ƙara bawa kalamanta daman cijewa lokaci zuwa lokaci.

Ba ta yi gigin goge hawayenta ba a wannan karon, ta bar su suna ci gaba da zubowa.

Alal hak’ik’a bata tab’a ɗauka rana irin ta yau zai zo babinta ba, bata tab’a ɗauka zata tsinci kanta cikin wannan yanayi a dalilin aikin mintuna ƙalilan da ta saba yi a da ba.

A yau ga shi tana fama da abubuwa biyu manya, wanda tun tasowarta bata tab’a ɗauka ana iya samun wannan sauyi ta dalilin istimna’i ba.

A yau da take da aurenta, sha’awarta ya ragu matuk’ar raguwa, ga shi yanzu haihuwar ma ta rasa. Wannan musiba da ta ɗaurawa kanta ya fi gaban tunaninta.

Kanta ta ajje a cinyarta, ta shiga rera kukanta mai sauti. Har ila yau Abdulwahab na kallonta, cikin tsoro da kuma mamakinta.

Ƙirar sallah yake ji, amma hakan bai sa shi mik’ewa daga mazauninsa ba, haka zalika ita ma bata iya rarrashin kanta ta daina kukan da ta sani ba zai taimaketa da komai ba.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”.

Ya tsinci kanshi da furtawa, yana shafa fuskarsa cikin tashin hankali. 

Billahi shi shaida ne, tashin hankalinsa ya zarce wanda Juwairiyya ke ciki a yanzu.

Ta juya masa kwanyarsa, ta sauya tunaninsa ta kuma ƙara dagula lamarinsa.

Mik’ewa ta yi dan ta isa ga mahaliccinta, a yanzu ta sani, bata da gatan da ya wuce na Rabbinta, bata da inda zata kai kukanta sai wurinSa, kuma babu wanda ya cancanci sanin damuwarta sama da Shi. Shi ta yi wa laifi, kuma ya jarrabeta ta hanya mafi girma, ya rage a gareta ta yi ƙok’arin cinye wannan jarrabawa.

Hannunta ya rik’e da ta zo wucewa gefensa, ko kallon ɓangarensa bata yi ba, hankalinta kacokan ya koma ga mahaliccinta da ya yi ƙiranta dan ta bauta masa.

“Ki sani, akwai tambayoyi masu yawa a bakina, banda maganganun da suka kasa samun damar fita a yanzu.

Ban sani ba ko ni na yi mummunar fahimta a kalamanki, amma maganganunki ya rud’ani. Idan ni kin bani masturbation matsayin dalilina na karb’a, ba don komai ba, sai don ya kamata ki san aikin da…”

“Na sani tuntuni”

Ta katsesa ba tare da ta juyo ba.

“Ina nufin abunda kake aikatawa, na dad’e da sani. Aikinka, ya tab’a zama aikina a can baya, ina nufin tun kafin aurenmu”.

A wannan gab’a, hannunsa da ke rik’e da ita ya saki, hakan ya bata damar sa gudu zuwa ɗakinta, kukanta na ci gaba da ƙaruwa.

Zuciyarta da dukkan duniyarta ya kife. Kunya ya dabaibayeta. Bata san wani irin duba zata yi wa mijinta ba, bata san ya ya ji da ta sanar da shi gaskiyar da bata tab’a ba shi ƙofar sani ba. 

Ina makomanta? Amsar ne dai bata sani ba.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.