Bayan awa huɗu da faruwar haka Shadow ne yafarka daga baccin da ya ɗaukesa tare da kurma wani raza nanne ihu.
Yana ƙoƙarin saukowa daga kan bed sai cewa yake wallahi sai na kashe ku ni zaku ciwa Amana dukan ku nine nan ajalinku.
Ayiya ce tafito daga toilet cikin sauri wanda yanzu nan ta shiga domin ta ɗauro Alwalar sallar magrib.
Kai tsaye gurin da Shadow yake tanufa cikin tashin hankali tace "Ahanaf lafiya kake kuwa? Su waye kuma Zaka kashe?" Tafada Tana kokarin rike Masa hannaye,
tureta Shadow yayi da karfi tayi baya zata Fadi ƙasa. . .