Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Dutse Daya by Rukayya Haroun

Humaira mace ce da tasan kanta domin bata barin Hydar ya kwana da kunci a cikin zuciyar shi, dole sai tasan yadda tayi ta wanke mishi zuciya da gwalagwalan kalamanta kamar yadda yake fada a kowanni lokaci. Lumshe idanu ya yi tare da yi mata kyawawan addu’o’i kamar yadda ya saba a koda yaushe.

Bayan sun gama breakfast ne Hydar ya zantawa Humaira dukkan labarin mummunan mafarkin da ya yi. Murmushi ta yi mai cike da nuna kulawa muryar ta cikin sanyi ta fara magana.

“Haba Babyn me, shifa mafarki da kake gani ba dukkan shi ne yake zamA gaskiya ba, sannan hadisin manzo sallallahu alaihi wa sallam ya nusar damu, addu’a tana canza mummunan kaddara ta zama kyakkyawa. Ina so ka sakawa zuciyarka nutsuwa, babu wani bawa da baya tafiya da wannan abubuwa guda uku, wato Arzikin shi, ajalin shi dan uwata ko aljanna. To idan har ka yadda da wannan lallai zaka zauna lafiya, sannan ka samu gamshasshiyar nutsuwa sannan komai na duniya zai dai na daga maka hankali.”

Ajiyar zuciya ya sauke da alamun ya gamsu da dukkan bayananta.

“Aishatul humaira, nasan har cikin zuciyarki kina son haihuwa, ba kya nunawa min ne kawai sabida kar ki dagamin hankali, wallahi Ina kaunarki fiye da yadda kike zato, Ina rokon ubangiji ya bamu rabinmu muma.”

Da mamakin Humaira sai taga mijin nata ya fashe da kuka, duk da ba yau ne karo na faro da yake kukan rashin haihuwar matar tashi ba, murmushi ta yi mai cike da fassara, ita ba bakin ciki ba kuma farin ciki ba.

Hakika ta tabbatar a yanzu babu abunda take da muradi irin ta ganta tana dauke da ciki. Duk kuwa da irin yawon asibiti da sukayi na kasa da wajen najeriya, ba’a gano mutum daya daga cikinsu da yake dauke da matsala ba, hasalima likitoci abun da suke fada musu kullum shi ne rabon yana nan zuwa in sha Allah. Kawar da fuskarta ta yi gefe sannan ta saka dogajen yan yatsunta ta fara goge mishi hawayen da ya cika idanun shi, maimakon ya yi shiru sai ya rungumeta dukkansu suka saki wahalallan kuka.

Kana ganin yanayin kukan nasu, zaka gane dukkansu suna jiran irin wannan ranar ne suyi kukan da babu mai rarrashin wani. Kwankwasa kofar parlour ya sa suka yi saurin raba jikinsu, saurin goge hawayensu suka shiga Yi da sauri sauri, da sanyin jiki Humaira ta nufi kofar domin budewa. Da karfi aka hankado kofar wanda ya yi daidai da shigowar mata guda biyu, fuskarsu a daure tamau babu amalar walwala. Aisha ta ja baya sannan ta yalwata razananniyar fuskarta da fara’a tare da cewa,

“Maman Hafiz sannunku da zuwa.” Babu wanda yabi ta kanta, dukkansu cikin parlour suka nufa suna yatsuna fuska, masauki suia yiwa kansu kan kayatattun kujerun dake katafaren parlourn, Aunty hauwa(Maman Hafiz) ta fara bin parlour da wani wulakantaccen kallo sannan ta watsa razanannun idanunta akan Haydar, dake zaune kan kujera.

Risinawa ya yi sannan ya gaisheta, babu yabo ta amsa, Aisha cikin rawar jiki ta gaidasu sannan ta wuce kitchen kai tsaye. Sosai gabanta yake faduwa, domin ta tabbar idan akaga Aunty Hauwa to gaskiya bafa alheri tazo da shi ba. Tun da ta shiga kitchen din duburburcewa ta yi, ta rasa abin da ya kamata ta basu su fara tabawa kafin ta yi musu abinci.

Tunowa ta yi akwai snack da ta siya a wajen jannat snack and more, da hanzari ta bude fridge din ta dauko robar samosa da spring rolls ta shiga soyawa, ruwa da lemo masu dan sanyi ta saka kan Trey ta nufi parlour zuciyarta kamar zata fito tsabar tsoro.

Har lokacin parlourn tsitt sai karar keyboard ne ke tashi, daga Rauda har Aunty Hauwa hankalinsu nakan wayoyin hannunsu.

“Sannunku da hutawa, Aunty ga ruwa.” Kamar a sama Aunty Hauwa ta tsinkayi muryar Humaira, cikin Isa da jin kai ta ce.

“Ba ishin ruwa bane ko yunwa ya kawomu ba, sanin kanki ne babu yunwa a tare damu.”

Humaira ta kara sunkuyar da kanta kasa, zuciyarta na yi mata luguden tashin hankali. Jiki a mugun sanyaye ta nufi hanyar da zata sadata da bedroom dinta, cikin tsawa ta ji muryar Aunty Hauwa na fadin.

“Eh ba shakka! wato Aisha har nakai lalacewar da Ina miki magana za ki kadamin keya wato dankwali ya bani amsa kenan? Wallahi Aliyu Haydar kaci amanar zuminci, ka zubarda dukkan nasiha da wasiyar da Hajiya tayi mana. Ka fifita mace akan yan uwanka na jini, ka bata dukkan lokacinta fiye damu, kai kai Aisha kin ci amanar zuminci, kin rabamu da Dan uwanmu guda daya tal kamar nama a miya.”

Tana kaiwa nan ta saki kuka, jikin Humaira a sanyaye ta dawo ta zauna akan carpet, dole tasa ta fara bawa Aunty Hauwa hakuri ba dan tayi wani laifi ba.

<< Dutse Daya 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×