Gishiri-gishirin da ta ji saman laɓɓanta ne ya ankarar da ita kuka take. Da sauri ta hau sharewa zuciyarta na tabbatar mata ba kukan tausayinsu take yi ba.
Da maghriba tana zaune zuciyarta cike da zullumi Malam tunda ya fita har yanzu bai dawo ba ta 'ji sallamar Aminyarta. Da hanzari ta tashi tana washe baki duk wani ƙunci da take ji tana yana wucewa.
"Salame ina kika shiga ke kuwa yau kwana biyar nake cigiyarki ?"
Tutturnan bakar matar dake amsa sunan Salame ta washe baki makaken wawulon dake bakinta ya bayyana.
"Hmm ke dai bari, Ɗan. . .