An Yanka Ta Tashi
“Da alama Barr. Zubaida ta zo da wasa ya Mai Shari’a, ya kamata a dakatar da shari’ar nan haka, ayi duba da tarin hujjojinmu a yanke hukunci ga Azzalumin nan.”
Barr. Jazagazi ya furta bayan ya miƙe tsaye.
“My Lord ayi mini Afuwa, amma tabbas duk abinda na faɗa haka yake, wannan rashin ganin file ɗin shi zai nuna maka maƙiya waɗanda suke da hannu a kisan suka ɗauke shi.”
“Ta ya ya za ai ki tattara abu mai muhimmanci ki aje a inda maƙiyan za su iya ɗauka? Ga ki kuma a tsaye a gabanmu cikin lafiyarki balle ki ce tare ki suka yi suka miki mugun duka suka ƙwace. Bari ki ji, idan na samu case kome ƙanƙantarsa, ko da kuwa na yara masu kame kajin unguwa ne, to kuwa duk abinda na tattara na evidence a cikin file a ƙarƙashin filona na barci nake ajewa, ko Matata ba na bata damar taɓa shi, bata ma sanin na menene”.
“Ai ni ma yanzu da na fito daga gida na rasa shi, akwai shagon da na tsa…”
“For God Sake ki fito zuwa kotu, sharia kuma kike yi ta kisa, ba ki ji kunyata ba da ta Alƙali da ta wanda kike karewar da tarin mutanenki kike cewa kin tsaya a shago…?”
Ya furta a zafafe bayan ya saki ɓoyayyen murmushi sanin da ya yi ta ƙara kwafsawa, ba wannan maganar ya kamata ta yi ba. Alƙali ya kamata ta nemi gafara dan zai iya yanke mata hukunci me tsauri, amma ba zai bata wannan damar ba, gwara ya kaita ƙarshe ayi a gama, akwai tarin abubuwa a gabansa.
“…My Lord, akwai alamun Barista ba ta san aikinta ba, ko kuma tana koyo. Wannan ya nuna ba tada wani evidence, sai ma kokarin ɗorawa wata lefin da bata ji ba bata gani ba, sannan ta zo da wasa mai girman da ba a taɓa yin irinsa a tarihin kotun nan ba, ta ɗauko takarda mai ɗauke da mummunan zagi ta baka ka karanta, wanda dole za ka ji kamar kai aka zaga, Kodayake waya sani ko hakan take nufi? Dan haka ina roƙon kotu mai adalci da ta duba tarin hujjojinmu ta yi hukunci bisa adalci.”
Kotun ta ruɗe da hayaniya, da yawansu suna Allah wadai da Zuby.
Ji ta yi kamar ƙasa ta tsage ta nutse a can ƙarshen ƙasanta, a duk kalamansa, kalmar tana koyon aiki ya fi dukanta, ji ta yi ta muzanta ta gama tozarta a idon duniya da aikinta da take ji ta bar shi kenan har abada. Wannan yasa ta kasa amfani da damarta ta roƙon afuwa duk da an sake bata dama. Sai dai bata da wannan karfin, ƙafafunta kaɗai bata jin za su iya ɗaukarta balle ta iya buɗe baki domin kare kanta. Abu ne mai girman da ba a taɓa yi mata ba, duk da kuwa ta sha ɗaukar shariar da ta fi wannan hatsari ta manyan ‘yan Fashi, amma ba a taɓa tozarta ta irin yau ba. Dan haka ta yi shiru tana juya yatsunta kanta a sunkuye. Alƙali ganin haka, sai ya ci gaba da rubuce-rubucensa.
A sace ta kai kallonta ɓarin da yake, ya naɗe fuskarsa da wani dogon Turban, ya saka kwankwamenen glass yadda zai yi wahala idan sanin TV ka masa ka shaida shi a yanzu. Shi ma idanuwansa na kanta, ɗaga mata hannu ya yi ya dunƙule yana aje shi a saitin zuciyarsa, alamun anan take har gaban abada. Murmushi ta yi me kyau tana jin yadda kome na jikinta ke dawowa daidai. Wata iska na ratsa sasan jikinta na kore zufa da ɓarin jikin da Zuby ta haddasa mata. A hankali ta miƙa hannayenta ta dafe saman akwatin shaidar da take tana kallon Zuby da murmushin gefen baki. Dama ya faɗa mata ta kwantar da hankalinta, zai iya mutuwa saboda ita.
A tun ranar da ta faska masa mari a bainar Jama’a, bayan ta dawo gida ta ga babu Hankacif ɗinta jikinta ya bata ta jefar da shi, idan ma ɗauka ne an riga an ɗauke. Hankalinta ya yi mummunan tashi, gashi har dare tana ta kiran Oboy yana rejecting.
Ƙarfe 10:00pm daidai haƙurinta ya ƙare, ta miƙe ta salla wanka ta fice zuwa gidansa. Ta daɗe tana knocking kafin ya ga damar buɗewa, sai dai fa neman rashin mutuncin da ya shirya yi mata ya yi ya rasa sakamakon tsalle da ta yi ta maƙalƙale shi tana sakin gunjin kuka. Kasa kome ya yi ya ja ta ciki yana ta aikin rarrashi. Bayan ta nutsu ne ta kwashe labarin kome ta bashi na tashin hankalin da take ciki. Shi kansa gangancin nasu ya dake shi. Sai dai saboda ya samu abinda ya daɗe yana mata ƙulafuci ya saka shi yi mata alƙawarin zai shiga cikin lamarin shi ma, zai raba Barristar da duk abinda ta tattara in dai ya dangance ta. Daɗin haka ya saka ta cukwikwiye shi tana kissing tsakiyar ƙirjinsa, ƙarshe suka zarce inda ta mallaka masa kanta, abinda tun fitowarta bariki ba ta taɓa yi da wani namiji ba, ita dama ta mata ce, data tuba kuma shi ta riƙe suke soyayya ba tare da ta yarda ta siyar masa da kome nata ba. Sai dai a yanzu a kan asirinta ya tono idan ma Dadironsa yake buƙatar ta zama za ta amince matuƙar zai tsaya mata kan lamarin.
Sai dai har safiyar yau bata ji labari daga gare shi cewar ya yi wani abin ba, shi ya sa duk hankalinta bai kwance duk da a bayansu ta ga shigowarsa kotun. A yanzu kam ya gama wanke mata rai da ya tozarta Zuby a bainar jama’a, tabbas saboda hakan ana fita daga kotu za ta saka masa ta hanyar ba shi a karo na biyu, dama tun ranar yake kwakwarta.
“A section 224 of the penel code, a sakamakon kama Sagir Muhammad Maƙarfi da aka yi da hujjoji, kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ƙarashe sauran rayuwarsa a firsin (Life Imprisoment.)”
Innalillahi Wa Inna Ilahhir Raji’un Shi ne abinda Sagir, Babban Mutum, Zuby suka furta, tuni hawaye suka fara zuba a fuskar Babban Mutum. Sagir kuwa rintse idanuwansa ya yi yana jin dama ba a haife shi ba, yana jin ya zo duniyar ne a banza zai koma a wofi, yana tuna Alhajinsa da Hajiya, yana tuna asalin ranar ma da ya fara ganin Faɗime,
yana jin kome da ya faru daga lokacin da ya fara mallakar hankalinsa na dawowa tar-tar cikin kwakwalwarsa. Hawaye masu ɗumi suka zuba masa, shi kam da wannan bala’in ji ya yi dama rataye shi aka yi ya mutu lokaci guda akan dai a aje shi a prison har mutuwarsa.
Faɗime kam ƙirjinta ya yi wani irin mugun bugu sa’ilin da ta haɗa ido da Babban Mutum ta ga yana hawaye. Zuciyarta ta karye, wani abu mai kama da guduma ya daki tsakiyar kwalkwalwarta a lokacin da ta ji a cikin kanta ana tambayarta ‘yanzu idan yaron ya gane ita ce silar mutuwar ubansa? Dame za ta kare kanta?’. A karo na biyu da ta ji ta yi kuskure mai girman da ba zai goge ba. Ranar ta dawo tar! Cikin kwakwalwarta, ranar da ita da kanta ta kai kanta ɗakinsa, ita da kanta ta amince kome ya farun, tana da damar da za ta yi ihu amma ba ta yi ba saboda tana jin daɗin abinda yake mata, Sagir ba fyaɗe ya mata, ba kuma danne ta ya yi ba bare ta ce ya saka mata ƙarfi. Tana da damar da za ta faɗawa mahaifiyarsa, amma ba ta yi ba ta biyewa zuciyarta da gudun ɓacin ransu ta tafi. Kenan a yau ta zama cikakkiyar Azzaluma, idan an zalunceta, to ita ma kuwa ta yi zalunci me girma, za ta iya cewa ta kashe rai guda, ta aikata abu irin na Uwale duk da ita ce uwar goyonta kenan ba a ƙasa ta ɗauki zalunci ba.
Toshe kunnuwanta ta yi da ƙarfi da ta ji zuciyarta na haɗa ta Uwale. Idan har zaluncinta zai zama irin na Uwale za ta gwammace ta mike yanzun a gaban kotun ta ƙaryata kome, sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe, haɗa ido da ta yi da Sagir ta ga yana kwalla da maganar Alƙali na karshe ya sakata dafe kanta da hannu biyu wasu zafafan hawaye na bin kuncinta, nadama ta same ta a lokacin da ba tada amfani.
“Ita kuma Barista Zubaida Rabe a sakamakon laifin raina hankalin kotu da tayi ta hanyar ciwa Alƙali mutunci, kotu ta yanke mata zaman Gidan Yari na kwana uku dan ya zama jan kunne ga ‘yan baya.”
“FamFamFam! Nan ne ƙarshen soyayyar.” Shi ne abinda Zuby ta furta tana ɗora rinannun idanuwanta da babu ɗigon hawaye cikin na Sagir. Ta yiwa Alƙali lefi, kamata ya yi ta nemi gabararsa ya yafe amma bata yi hakan ba saboda yanayin da maganar ya haifar mata. A hankali ta janye idanuwanta tana sauke su kan na ‘yar sandar da za ta tafi da ita.
Sagir kam ji ya yi kamar ya cewa Alƙalin a haɗe hukuncin Zuby cikin nasa, ko kuma ya bashi tabbacin shi ya sa a canja takardun, amma kuma wane hankali ne zai ɗauka? Sai dai a hakan cikin kwarin gwiwa ya buɗe baki zai nemi alfarmar a lokacin da kowa ya miƙe sakamakon miƙewar da Alƙali ya yi ya juya zai fice ta ƙofarsa. A lokacin ne kuma waccar ƙofar ta baya ta buɗe, yaro ɗan kimanin shekara 8 ya shigo, biye da shi wani dogon mutum ne da wani gajere a bayansa.
“Laa ga Uncle Slim!”
Ya furta da ƙarfi yana kwace hannunsa daga na mutumin ya zura da gudu gun Sagir da wasu ‘Yan sanda suka riƙe.
“Abbati!”
Shi ne abinda Faɗime ta furta bayan ta yi wata wawar miƙewa da ya saka Alƙali dafe handle din ƙofar ya juyo, Barista Zuby da Jagazi miƙewa tsaye suna ware idanuwa.