Skip to content
Part 6 of 28 in the Series Falsafa by Haiman Raees

ZAZZAFA 

Ke ce zazzafa ta

Kin wuce duk ‘yan mata,

Kin fi su aji na shaida.

Ke ce zazzafa ta,

Ke ce mai haske mata,

Duniya ma ta shaida.

Mata ku fito ga zazzafa,

Ku fito dukka ku yo caffa,

A wurin yayarku zazzafa.

Wani sha’anin sai shinkafa,

Don ta burge ku tattafa,

Domin ta cika zazzafa.

Aikin banza wankin tifa,

Ki bar haɗa kanki da zazzafa,

In kuma kin ƙi ki sha kuka.

Na san mai dai kika shafa,

Ita ko da Vaseline ta shafa,

Ta zarce kalar su wane karfa.

Idan ta tsaya ga kyan diri, 

Komai cascas ba kuri, 

Wata ko duba kamar gatari. 

Na yo dace da zazzafa, 

Allahu tsare ni kula karfa, 

Mai janjani kuma ga mita. 

Zazzafa ce ke da zafi, 

Mai kamun kifi je rafi, 

Abin dai ina ga zai fi. 

Zazzafa ta muku nisa, 

Sama ta yi wa yaro nisa, 

Kamar masu baccin kasa. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Falsafa 5Falsafa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×