Skip to content
Part 18 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Alhamdulillah

Alhamdulillahi na gode rabbani

Alhamdulillahi ya Jalla mai girma

Alhamdulillahi godiya ga rabbani

Alhamdulillahi ya Azizu mai girma

*****

Farko da sunanka sarki gwanin girma

Mulkinka ya zarce na dukkannin kowa

Ikonka ya wuce iko da dukkan girma

Kai ne ka yo komai kuma kai ka yo kowa

*****

Salati ga Manzona abin faharin girma

Gata ga duk duniya da ya zarce duk kowa

Habibi abin ƙauna Muhammadu sha girma

Kai ne macecin mu bai da aibu gun kowa

*****

Na gode Allah na don ya yi min komai

Ko da bani da komai Allah ya yi min komai

Ko da akwai komai Allah ne da yin komai

Allahu na gode don ka yi min komai

*****

Alhamdulillahi na gode rabbani

Alhamdulillahi ya Jalla mai girma

Alhamdulillahi godiya ga rabbani

Alhamdulillahi ya Azizu mai girma

*****

Cikin halittu dubbai ka zaɓe ni sarkina

Cikin mutane dubbai ka keɓe ni sarkina

Cikin musulmai biliyan ka ƙago ni Allah na

Allahu na gode tabbas kai ne maƙagina

*****

Cikin mutane miliyan ka yi ni da bakina

Cikin mutane biliyan ka yi ni da hancina

Cikin mutane tiriliyan ka yi ni da kunnena

Cikin dubun dubatar jama’a ka yi ni da idanuna

*****

Ka yi ni ba tawaya Alhamdulillahi

Ka yi ni ba naƙasa Alhamdulillahi

Ka yi ni ba hauka Alhamdulillahi

Ka bani imani Allah Alhamdulillahi

*****

Alhamdulillahi na gode rabbani

Alhamdulillahi ya Jalla mai girma

Alhamdulillahi godiya ga rabbani

Alhamdulillahi ya Azizu mai girma

*****

In na yi numfashi kai ne silar yin shi

In na yi yo barci kai ne silar yin shi

In na yi yo ciwo kai ne silar yin shi

Haka ma in na warke komai kai ne kake yin shi

*****

Bani da buƙatar da ta fi gafararka sarkina

Bani da burin da ya wuce rahamarka sarkina

Bani da burin da ya wuce in ganka Manzona

Ko da a mafarki ina cikin baccina

*****

Allah daɗo tsira wurin ɗaha Manzona

Alihi sahabbansa da masu son Manzona

Allahu mun gode da komai da komai na

Cikin wanga duniya da lahira gobena

*****

Alhamdulillahi na gode rabbani

Alhamdulillahi ya Jalla mai girma

Alhamdulillahi godiya ga rabbani

Alhamdulillahi ya Azizu mai girma

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 17Fasaha Haimaniyya 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×