Skip to content
Part 22 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Ka Cuce Ni

Babana ka cuce ni

Ka tauye mini haƙƙi

*****

‘Yata karda ki zarge ni

Allah zai baki sauƙi

*****

Babana ka cuce ni

Ka tauye mini haƙƙi

Aure nake so

Na bayyana maka ka ƙi

Ina da masu sona

Amma ka ce musu ka ƙi

Ka ce sai boko

Na gaza ce maka na ƙi

*****

Sanadin haka ne

Kai ko ka tauyan haƙƙi

Na kammala digiri

Ka ce sai na ƙara

Samarin cikin gari

Ka ce kada in saurara

Ƙawayena duk sun yi aure

Wasunsu ma fa har da yara

Babana ka cuce ni

Na gahi dole na ɓara

*****

‘Yata ki daina faɗar haka

Kin san bai kyautu ba fa

Ke ɗai ki kwanta akan gado

Ki huta akan katifa

Lemo kike so ne

Abarba ko kuma tuffa?

Share hawayenki

Tunani karda ki zurfafa

Ilimin bokon nan kin san

Ya zama dole a yanzu

Ko me kike so

Ki faɗe shi a yanzu

Na tura ki boko ne

Domin farinciki ya wanzu

Amma ke sai surutu kike

Tun ɗazu haba mana

Ki kwantar da hankali

Kin ji mai sunan mamana

Ga shi ai a yanzu

Ina kwance bana jin daɗi

Na kawo kwalin bokona

Na san kai ka ji daɗi

Amma in na mace yau

Shi ke nan ba ni da kowa

Kai ma in ka lura baka da kowa

Tunda ba ni da aure ya zama

Kaima baka da kowa

Babu ‘ya babu jika

Ya zama baka da kowa

*****

Ki kwantar da hankali

Za fa ki samu sauƙi

Kuma in sha Allah

Zan bari ki yi aure

Aure bautar Allah

Ba na ƙin ki yi aure

Ni ma na gane wallah

Ya dace na ƙara aure

Wataƙila ikon Allah

Yasa na samu matar aure

In bar kaɗaici in samu kowa

*****

Na gode Allah Alhamdulillah

Na yi murna Baba

Da ka gane gaskiya kuma ka gyara

Tun lokaci bai ƙure ba

Nima ka yafe ni na yi katoɓara

Da bata dace na faɗa ba

Zafin zuciya ce ta yara

Ta sani na ce ba da tunani ba

*****

Babu komai nima na sani

Ai ban kyauta ba

Na hau na take sani

Haƙƙin ki ban duba ba

Kuma duk za mu gyara

Tun lokaci bai ƙure ba

Astagfirullah Allahu mun tuba

Taubatun nusuha ba za mu ƙara ba

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 21Fasaha Haimaniyya 23 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×