Duk wanda ya riƙe Allah
Ya so manzon Allah
Ya kuɓuta daga wahala.
Na san cewa wasu daga cikinku za su ce, 'ina Haiman! Ai Sam kada ka damu sun zo ne domin su taimake ka daga hannun Sinu da Mugyambo, blah blah blah!
Erm.. Na gode da irin wannan kyakyawan tunani naku a gareni, amma kamar yadda na faɗa muku a baya, rashin sa'ata ya kai maƙura. Ina nan tsaye ina kallonsu tare da jiran ganin abinda zai faru, ai kuwa ban daɗe ba ina wannan jira sai na ga Shah Rukh Khan. . .
Gaskiya ne wallahi. Labari ya kayatar kuma mun karu sosai. Allah ya ƙara basira.
Na gode sosai. Jazakallah Khair
An outstanding finale! Kudos
Thank you very much Zee.
Gaskiya na karu sosai da wannan labari. Allah ya ƙara basira.