Habib ne ya karaso cikin far'a suna gaisawa da Kamal Yayin da mai gadin yake masa kirari ."Ka ga daya daga cikin sojojin mu , ka ga jarumi Habibu dan Alaji. " Habib ya ce ."Dan Allah Haruna ka tafi ." Kamal yana dariya Sannan mai gadin ya koma bakin aiki yana sake musu kirari "To ya na same ku bro ."? Kamal ya fad'a yana kallon Habib cikin farin ciki A lokacin Khalid ya shigo yana tura kofa , yayin da me gadin shima yake masa kirari Kai tsaye Khalid ya nufo wajensu Kamal yana cewa." Ahhh Habib bako ka yi ne. . .