Gangar Shaidan
01.
Da sunan Allah,
Mai ikon kome da mai shi.
02.
Allahu gwani,
Wanda yai mana rai da kishi.
03.
Manzon Allah,
Wanda kaf duniya ba kamar shi.
04.
Ya zo da gargaɗi,
Akan Ibilis da mabiyan shi.
05.
Sahabbai jimla,
Har malamai duka sun tsane shi.
06.
Ita Gangar Shaiɗan,
In har ya buga sai a bi shi.
07.
Watau sautin Shaiɗan,
Ko a ina kake za ka ji shi.
08.
Taken Shaiɗan,
Da ya tashi za ko a bi shi.
09.
Mabiyan Shaiɗan,
Tabbas su ne za su bi shi.
10.
Hanyar Shaiɗan,
In yai huɗuba sai su bi shi.
11.
A zuci in har ya shigo,
Zance ya ɓaci ga mai shi.
12.
In ya kama ka,
Addu’a ce kaɗai za ta kar shi.
13.
Igiyar Shaiɗan,
In ta kama ka za ka bi shi.
14.
Ammbaton Allah,
Shi kaɗai ke maganin shi.
15.
Ya Ilahu Allahn mu,
Muna neman tsari akan shi.
16.
Ka kiyaye mu,
Ka hana mu mu bi shi.
17.
Ka tsare ahali,
Da zuriyar mu daga gare shi.
Masha Allah yah malam ubangiji Allah yah qara basira muna godiya sosai.
Amin. Jazakallah Khair.
#haimanraees
Allah ya tsare mu. Amin.