Tunda sanyin asubahi su Farida suka bar gidan da suka yada zango a cikinsa, domin idan ma basu barshi ba yana gaf da gazawa, domin har sai da Faruk ya kwad'e wani Zombies, kwana saukai babu bacci, shi yasa duk sun fita yaccinsu, ido yayi zuru-zuru.
Suna cikin tafiya Farida cikinta ya sake d'aurewa gefe d'aya ta d'uke k'asa tana kiran sunan Allah.
D'an dakatawa sukai gaba d'aya suna dubanta, Hanan ranta a d'an b'ace da Faridar ta ce.
"Ke wai Farida miye haka kike k'ok'arin yi ne. . .