Cikin dakewa da ƙarfin hali na ke ƙoƙarin tilastawa kasalallun ƙafafuwana da ke neman nuna turjiya ga hidima da gangar jikina miƙewa tsaye. Sai dai na makara domin an bar kari tun ran tubani. Ban ƙara sadaƙarwa ce wa haƙata ba zata cimma ruwa ba sai da na fara kokuwa da ruwan hawayen da ke neman hanyar fita daga idanuna, nauyi da raɗaɗi su ka yi min dirar mikiya a kwakwalwata. A loƙaci guda tunani biyu su ka fara yi min karakaina da amsa kuwwa. Na kasa tantancewa da tabbatar da kalar zaren. . .