Skip to content
Part 1 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Ƙauyen Tandau, 1997

Cikin talatainin daren mai gauraye da hadari baƙi ƙirin take ta ratsa gonaki da kwazazzabai. Zuciyarta a bushe babu alamar tsoro ko kaɗan, sai ma idan ta ci karo da marmara ta sa ƙafa ta dake ta da ƙarfi kamar ita ke ƙara mata nisan tafiyar. Ba ta dakata ba har sai da ta isa bakin wasu bishiyoyi biyu da suka zama kamar ƙofa ga maƙabartar. 

Ta tsaya ƙyam! Tana ƙare wa cikin maƙabartar kallo, ta ɗaga kanta sama ta ga yadda baƙin hadarin ya lulluɓe hasken farin watan da ya haska doron duniyar. Ta sauke idonta a hankali tana mai da dubanta hagu da damarta; babu alamar wata halitta irin ta a illahirin gurin. Ta ƙarasa gefen bishiyar ta sunkuya cikin wasu tarin ciyayi da karare ta kama lalube a cikin baƙin duhun har sai da ta ji ta cafko ƙarfen fitilar kwai, ta janyo ta, ta aje gabanta, ta karkace gefen zaninta ta zaro ashana ta ƙyasta cikin fitilar. A take haske ya gauraye illahirin gurin. Ta miƙe ta ƙara dosar gefen ɗayar bishiyar ta kama lalube, ba daɗewa ta zaro magirbi da wani ƙaramin shebur. Ta riƙe su a hannunta ta doshi cikin maƙabartar bayan ta tsallake wani gulbi da damina ta kawo shi. Wani Kwaɗo mai rabon shan bugu ya yi tsalle ya maƙale mata ƙafa, ta haske shi da fitilarta ta sa hannu ta wafce shi ya shilla can wani yankin; ta ji kukansa da na sauran ‘yan uwansa da ke cikin gulbin da ta tsallake. Ta yi kamar ta juya, wasu shuɗaɗɗun zantuka suka wuce kamar iska cikin kunnuwanta.

“Har ki je ki dawo kar ki juya… Idan kika juya kar ki yi kuka da ni, ki yi da kanki… Na gama taimakonki Zawwa… Na gaji!!”

Ta ɗaga ƙafa da hanzari tana dosar sashen da ta tabbatar nan ake binne sabbin matattu. A cikin hancinta take zuƙo ƙamshin nasarar dukkan burinta. Wasu sasakun zantukan suka ƙara wucewa cikin zurmin kunnenta.

“Idan har kina so ki haifi ɗiya mace, sai kin yanko hantsar mace mai tsohon ciki da kuma gashin kanta… Da shi za a yi miki siddabarun da za ki haife ta… Idan har kina son Bawa ya warke, sai an yi masa wanka da ruwan farko da aka wanke wannan jaririyar, a take zai warke… Sai dai ki sani wanda ya rasa ƙafa ya rasa kenan har abada, tun da an riga an yi kuskuren yankewa, zai dai warke da ga nannaɗewar da ya yi, zai kuma buɗe baki  har ki ji ya ce miki ‘Ina ƙaunarki Zawwa!’… ‘Yar da kika haifa kuma ita ce za ta rama miki dukkan abinda kika rage… Ita ce za ta juya miki Hameedu Siddiqu da dukkan ahalinsa a tafin hannunta, yadda kika kasa, har kuwa zuwa kushewarsa. Don haka ki je a daren yau ki haƙe kabarin da yake na farko daga ɓangaren hannun damarki, ki tone shi za ki taras da mace mai ciki a ciki… Idan kika wuce yau, kin wuce burin rayuwarki kenan har abada ba ki ƙara samun wannan damar… Shekaru biyun da muka yi muna jiran wannan ranar ta tashi a tutar banza da wofi… Kar ki tsaya, ki tafi, ko da mahaifinki ne zai mutu a yau, kar ki tsaya, ki tafi!”

Kuwwar zancen ya cika kunnenta, ta tsaya ƙyam gaban sabon kabarin tana sauke ajiyar zuciya tamkar ƙadangaren da ya haɗiyi kunama.

A hankali ta ɗaga shebur ɗin ta fara yashe ƙasar kabarin, zuciyarta cunkushe da mamakin ganin ba a gama rufe kabarin ba, haka kuma akwai alamun ba a fi mintuna da gama binnewar ba. Ta ɗago tana sharce gumin da ta fara yi. Ta buɗe kunnuwanta tana sauraran gefe da gefenta, sai dai ba wani motsi. Ta yi baya da sauri sa’ilin da wani zazzafan tunani ya ɗarsu a ranta. Ta haska gefe da gefen kabarin, a karo na farko da wani abu mai kama da fargaba ya daki tsakiyar ƙirjinta, ganin da ta yi babu sawayen waɗanda suka binne gawar! Ta ƙara haskawa sosai babu wata alamar da ke nuna an tako gurin. Ta aje fitilar a hankali a ƙasa lokacin da dukkan jikinta ya ba ta cewa ba ita kaɗai ba ce a illahirin maƙabartar. Ta riƙe ƙugunta tana shafa Wuƙar Iccen da ta soke a gurin. Ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce,

“Akwai mutum a nan?!” Shiru ya ratsa, sai amsa kuwwar muryarta. Ta sake cewa,

“Ko waye ya fito mu yi sulhu!” Nan ma shiru, sai ma kukan wasu firgitattun tsuntsaye da amsa kuwwar muryarta ya tashe su daga bishiyar da suke fake.

Ta yi ajiyar zuciya ta ƙarasa ga kabarin ta ci gaba da yashewa da shebur har sai da ta fara hango farin likkafanin da aka rufe gawar da shi. A lokacin ne kuma mamaki na biyu ya shige ta, ganin an haƙa kabarin ba yadda ake yi ba; wannan rami kawai aka yi mai faɗi da tsayi aka tura gawar aka mai da mata ƙasa aka rufe. Da hanzari ta jefar da shebur ɗin ta sa hannu ta fara ture  ƙasar da ita. A lokacin da hannunta ya kai jikin gawar ne abin ya faru, numfashi ta ji mai ƙarfi. Numfarfashi irin na baƙar wahala, ba ita gawar kaɗai ke numfashi ba, hatta tsohon cikin jikinta motsawa yake yi. Ta yi baya cikin kaɗuwa, kiris ya rage ta juya, wata dakakkiyar zuciyar ta tsayar da ita bayan ta harba mata jumlar,

“Idan kika wuce yau, kin wuce burin rayuwarki kenan… Har abada ba ki ƙara samun wannan damar… Har abada!”

Ta ƙara duƙawa da hanzari cikin ramin tana ci gaba da ture ƙasar, numfarfashin na ƙara kusantar dodon kunnenta. 

Ta daɗe a wannan halin kafin ta gama gabaɗaya. Ta saka hannayenta biyu ta yaye likkafanin da ƙarfi ta jefar da shi gefe. A lokacin ne ta yi tozali da ita, doguwar mace da ba ta gaza shekaru goma sha takwas ba, duk da jini ya cika fuskarta da gefen wuyanta da ke bulbular jini, hakan bai hana ta ganin kyawun surarta mai matuƙar razanarwa ba cikin hasken fitilar kwan da ta dallare ta da ita.

Hannunta ta saka ta janyo ta da ƙyar daga cikin kabarin ta shimfiɗe ta gefe, ta tsaya a kanta tana ƙare mata kallo, zuciyarta na daɗa tsinkewa. Alamar da ta gani na bakinta da ke motsi ya saka ta duƙawa da sauri ta saka kunnenta a saitin bakin.

“R-ru-ruuwa…”

Ta ɗago tana mai waigawa hagu da damarta, babu alamar ko kwantaccen ruwa balle ta ɗibar mata shi ta sha. Ta kaɗa mata kai alamar babu, a zuciyarta tana jin tana ƙara ɓata lokaci ne, wannan matar dole mutuwa za ta yi, ta yanke abinda za ta yanka kawai ta kama gabanta. Da wannan shawarar ta karkace za ta zaro wuƙar ƙugunta, a karo na biyu matar ta ƙara buɗe baki tana kallon ta cikin hasken fitilar kwan da ke tsakiyarsu. Ƙara kasa kunnenta ta yi bakinta tana saurarar ta,

“Ki-kk–yn-fid da cik-cikin jikinaa…”

Auwal marra da ta yi wata mummunar razana, ta yi baya tana ƙare mata kallo cikin taraddadin ko mutan ɓoye ke mata wasa da hankali.

“Mutum ce ke?”

Sai da ta yi tambayar ta gane ba ta buƙatar amsarta ga wacce ta yi wa din.

Gabanta ta ƙara komawa ganin tana ta ƙoƙarin ɗaga hannunta saitin cikinta. Ta tsura wa cikin ido tana ganin yadda yake motsawa ta cikin doguwar farar rigar alharinin jikinta da ta gama rinewa da jini. Wani haske ya wulga cikin idanuwanta sa’ilin da ta tuna maganarta ta ƙarshe da shi.

“Amma ta ya ya zan gane kabarin mace mai ciki a cikin jerin kaburburan?”

“Kin manta yau shekara biyu kenan da na ce miki ki dawo zan ba ki rana? Ki tafi kawai… Ki je ga kabarin da na wassafa miki.”

Ta miƙe har ta kai ƙofa ta ji wasu zantukan nasa masu wuyar fahimta.

“Kin ga! Komai kika tarar cikin kabarin ki yi amfani da shi naki ne, halalinki ne Zawwa!”

Kamar ta farka daga mafarki haka ta zabura ta ɗora hannunta kan cikin tana shafawa. Idan har za ta fassara yarensa wannan abin da ke cikin matar shi ne dukkan maganin damuwarta. A karo na farko da ta kira sunan Allah cikin zuciyarta tana ƙarasawa da sauri ta tallafo kan matar,

“Waye uban cikin da kike so a cire? Zan cire tun da yana da rai, bai kamata ku mutu tare ba da ma… Amma waye Babansa, me ya kawo ki wannan yanayin, ina ne garinku?” Ta gaza magana sai mammotso baki da take yi, da ƙyar harafin ‘Haa’ ya fito, jini ya biyo bayansa tamkar suna kwata.

“Haadirru ko Haalliru? A ƙaryar nan suke? Tufafinki bai yi kama da na nan ba… Ina ne garinku?” Ta ƙarasa mata da hanzari. Kaɗa mata ido ta yi tana mai ƙara buɗe baki, ‘Huu.’ Sai kuma ta yi yaraf, numfashinta na ɗaukewa tana zuƙo shi da ƙyar.  Idonta ta kalla ta gane magana take yi mata, don tana ta son motsa hannunta. Hannun ta riƙo tana kallon Zoben Zinarin da ke jiki, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa ganin an saka abu kamar almakashi an tsaga hannun nata tun daga gaɓar farko ta hannu, a karo na biyu da ta yi mamakin yadda aka yi take numfashi har kawo yanzu. Ta kalli matar,

“Wannan kike so a cire?” Ta kaɗa mata ido. Da hanzari ta saka hannunta ta zare zoben. Zarewar ya yi daidai da wata tsawa da aka tafka mai haɗe da walƙiya wadda ta cika illahirin maƙabartar. Matar ta yi wata irin miƙa mai gauraye da atishawa jini na daɗa bulbulowa ta cikin hancinta, kafin kuma jikinta ya saki, rayuwarta ta koma ga mai shi!

A firgice ta yi kanta ta jijjiga, sai dai ina ta riga ta tafi. Ta sauke idanuwanta kan cikinta da yake wani irin motsin neman agajin gaggawa, a lokacin ne kuma ta ji sautin muryarsa.

“Ya Laɗeefu, Ya Hakeemu, Zawwa! Mai za ki yi da gawa?”

“Ubanka zan yi!” Ta furta a matuƙar fusace tana juyowa saitin da yake. Yana tsaye hannunsa aka, rataye yake da wata jakar fata alamar daga tafiya yake, a shekaru ba zai gaza ashirin da biyu ba.

“Haadiru me ya sa ka biyo ni? Yaushe ma ka dawo? Me ya sa wai ka raina ni… Duk sa’ad da zan yi abinda ke gabana sai ka shiga tsakiya?”

“Dawowa ta ke nan fa na gan ki kina ta sauri kin yanki daji, shi ne na biyo ki. ɓace mini ma kika yi sai yanzu na gano ki a nan… Yanzu Zawwa ba za ki daina biye wa Tsohon can ba? Na tabbata shi kaɗai ne zai haɗa ki da gawa a wannan talatainin daren kan abinda ya fi kowa sanin Allah ke…”

“Rufa mini baki shashasha marar kishin ubansa!” Sai kuma ta yi shiru tuna cewa da ma dole tana buƙatarsa, domin idan babu shi, sai dai ta bi ta hanyar da asirinta zai tonu watarana, dan haka ta yafito shi,

“Zo ka ga…” Ya matso a hankali yana leƙa gawar matar.

“Ta mutu, amma abinda ke cikinta na motsi… Ta buƙaci kuma da a cire mata shi don ya rayu. Ina kimiyyar da kake koyo, ba an koya muku fiɗa ba? To maza zo ka farka ta ka zaro abinda ke cikinta!”

Baya ya yi yana kaɗa kai da sauri da sauri.

“A’a ban iyawa… Wannan zalunci ne… A’a Zawwa ki tashi mu tafi, idan fatalwa ce za mu rayu da jininta a zuriyarmu, idan Aljana ce za ta buwaye mu… Ba a ma gama koya mana ba, ba kuma a ba mu shaidar mun iya ba.”

“Haadirr! An dai koya ko?”

“Eh!”

“To so kake na zagi Tsohonka a karo na biyu?”

“A’a…”

“To maza ka zo ka tsaga ta ka ciro abinda ke ciki. Kar ka damu, ta riga da ta zama gawa… Idan ka cire to wani ran ka agaza wa… Na kuma san cikin jakarka ba ka rasa abin aikin ba, idan ma babu ga wuƙata ta icce… Zo ka yanka ta.”

“Anya zan iya…”

“Za ka iya… Ka sa a ranka za ka iya komai!!”

“To ai kar na je na yanki abinda ke cikinta… To dai hasko mini sosai…” Ya furta a sanyaye yana sauke jakar ƙasa.

“Yauwa akwai zabira cikin jakata da ita ake yi… Kai ni kam fa ina tsor…”

“Ba na son kalmar nan ka sani ko… Ba na so!! Ita ce silar kwantar da rayuwarka da tawa. Zo ka yi aikinka!!!”

Ta furta masa a tsawace, idanuwanta sun yi jajur tamkar da hayaƙi aka lulluɓe ta.

“Ki haska mini sosai to…”

Suka duƙa gabaɗaya jikin gawar. A sannu ya saka zabirar ya tsaga ta daga saman mara, ya ce wa Zawwa ta danno masa cikin daga ƙirjinta, ta turo shi ya yo ƙasa. Ta saka ƙarfinta ta danno cikin ya taho, shi kuma ya ƙarasa janyo shi, ya saka zabirar ya raba cibiyar da mabiyarsa, a sannan aka fasa wata irin tsawa mai haɗe da rugugin aradu, wata baƙar guguwa da ta taho daga yamma ta lulluɓe su, ya haɗe da sautin kukan jaririyar da ta kwalla da dukkan ƙarfinta, ruwan saman ya kece tamkar da bakin kwarya yana sauka da ƙarfinsa a illahirin maƙabartar.

Zawwa ta yi wani kukan kura cikin zafin nama ta warce jaririyar daga sandararren hannunsa ta rungume ta a ƙirjinta, ya kai kallonsa ga jakarsa, ya yi gun ta da sauri ya zaro wani mayani mai kauri ya rufa musu, a tare suka doshi wata babbar bishiyar ceɗiya da ke kusa da su suka zube ƙasanta suna sakin numfarfashi. Idanuwansu ya shilla kan gawar da cikinta ke buɗe ruwa na ta sauka kanta, Haadiru ya runtse idonsa da ƙarfi yana gudun nuna tsoronsa a fili. Ya so ya rufe cikin gawar a mai da ta kabarinta. Zawwa kam ɗauke kanta ta yi ta sake rungume jaririyarta gudun kar ruwa ya taɓa ta ya tafi da wankan farko da za a yi mata dan bai wa Bawa ruwan ya yi maganin lalurarsa.

Ba daɗewa ruwan ya ɗauke, sai na sassanyar bishiyar da ke kaɗawa tamkar ana wani yayyafin. A tare suka sauke ajiyar zuciya suna duban juna kafin kuma su janye kallon zuwa ga gawar, ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa.

“Kai, mai da gawar cikin kabarinta ka rufe yadda ba wanda zai gane an yi haƙa a gun.”

“Eh hakan za ayi, amma fa cin mutuncin rai ne a saka ta a haka ba tare da an ɗinke inda muka tsaga ba.”

“Babu wannan lokacin Haadirr, ta mutu shi ke nan, ba ta buƙatar wani ado a tare da ita…”

“Amma Zawwa ya za a yi…”

Wani kallo da ta wurga masa ya saka shi datse zancen, ya miƙe kawai ya isa ga gawar, gefen doguwar rigarta ya kalla, babu inda zai iya yaga a jiki. Don haka kawai ya zare rigar jikinsa ya sunkuya ya naɗe cikin gawar da ita ya ɗaure tsam, kana ya ja ta a hankali ya jefa cikin kabarin. Ya ɗaga shebur ɗin ya fara mai da mata jiƙaƙƙiyar ƙasar. A lokacin ne aka haska wata walƙiya mai tsananin haske, ta haska masa can gabansa, cikin wata duhuwa ya ga alamar mutum a tsaye yana dubansa. Sakin Shebur ɗin ya yi ya juya a guje zuwa inda Zawwa ke tsaye rungume da jaririyarta.

“Naa…naa rantse da Allah ba mu kaɗai ba ne a nan… Kin ga…” Ya furta, bakinsa na rawa yana nuna mata saitin duhuwar. Ta ɗaga fitilar kwanta tana haske gurin, sai dai wayam babu kowa, babu ma alamar akwai wani mahaluƙin da zai iya wanzuwa a gurin. Duhuwar a tsakankanin wasu kaburbura masu tudu take.

A tare suka kalli juna, a karo na farko da ta saka hannunta ta sharce wani sassanyan gumi da ya tsiyayo mata tun daga lokon hancinta. Ba Haadiru kaɗai ba ne ya san da wani a tare da su, hatta ƙofar tsiron duk wani gashi da ke jikinta abinda yake ta ankarar da ita kenan tun farkon bayyanarta cikin maƙabartar!

“Haadiru mu ɓace daga gurin nan…” Ta furta a hankali tana takawa kusa da shi sosai.

“Idan ma da wani bibiye da mu za mu gane a nan gaba.”

Ya tsura mata ido cikin tsoro mabayyani, kafin kuma ya sunkuya ya ɗauki jakarsa da sauran kayan aikin su fara tafiya ba ko waiwaiye. Ba wanda ya ƙara cewa da ɗan uwansa komai har suka fita daga cikin maƙabartar. Suna gab da isa gidan, Haadiru  ya ja ya tsaya yana duban Zawwa da ke ƙoƙarin shigewa ta ƙofar baya da aka rufe ta da wani kakkauran buhu na algarara.

“Zawwa me za a ce wa Baba wai? Kar kalamanmu su saɓa.”

Juyowa ta yi ta dawo saitinsa ta tsaya, a sannan ne kunnuwanta suka daɗa zuƙo mata wani abin. Ta yi wani murmushi cikin duhun bishiyar da suke ƙasanta, ta matsa jikin Haadiru sosai, daidai saitin kunnensa ta masa raɗa,

“Ruga da gudu cikin ɗakina daga can ƙurya za ka ga wani shantu ka ɗauko mini.”

Daga yanayin sautinta ya gane ba ta buƙatar tambaya, don haka ya zura da gudu domin cika umarninta, ita ma ta mara masa baya, sai dai ba ta kai ga yaye buhun ba ta ji ana kici-kici da nishi. Da sauri ta dawo saitin bishiyar tana ɗaga fitilarta sama ta haske fuskar Basamuden mutumin da ke biye da su tun daga cikin maƙabarta. Tarkon da suke haɗawa don kama ɓarayi ya kama shi. Wata igiya kakkaura ya taka da aka sakalo ta tun daga saman bishiyar aka binne ta a wani rami. Kafarsa a ɗaure tana reto a sama a yayin da kansa ke ƙasa. A haka Zawwa ta haske shi tana kashe shi da wani shu’umin murmushi.

“Ki kunce ni dan Allah. Ni ba da sharri nake nufinki ba, wannan jaririyar kawai za ki ba ni in binne. Saboda kar a haife ta aka ba ni umarnin binne uwarta!”

“Idan ba ka san sirrin wuri ba ka daina bibiya, idan ba haka ba kuwa watarana za ka je inda zai kai ka ga kushewarka.”

Abinda ta furta masa kenan Haadiru ya iso, ta ba shi umarnin ya yi ta muƙa wa mutumin shantun har sai jini ya fita a jikinsa, idan kuma ya sake ya yi ihu a take za ta yanke masa ‘yan maraina. Ta furta masa tana nuna masa wuƙarta da ke soke a ƙugu. Jin haka ya sa mutumin matse bakinsa yana jin ana bugunsa ko ta ina amma ba damar ihu. Sai da ta tabbata ya bugu, shi kansa Haadiru ya gaji, sannan ta ce ya dakata.

Ta dubi mutumin da bakinsa ya kumbura suntum,

“Wane ne kai, waye ya ce ka binne ta?”

“Ni ɗan aike ne, sai dai ko za ki kashe ni na gwammace na mutu a kan na faɗa miki wanda ya aiko ni.”

“To na ji… Wane ne uban wannan yarinyar, a ina waccar budurwar take?”

“Ki taimaka ki bar tambaya ta abinda ba zan taɓa amsawa ba. Ki kunce ni ki ba ni wannan jaririyar kafin Ogana ya sami labari, wallahi kin ji na rantse, idan ya san an haifi yarinyar nan dukkanmu kashe mu zai yi.” Ya furta da ƙyar wani jini mai yauƙi na fita ta bakinsa.

Haadiru ya yo bayanta a tsorace ya tsaya,

“Zawwa ki ba su yarinyar nan, kin ga daga ganin zubin mutumin nan kin san ba irin mutanenmu ba ne, kar mu je mu jawo wa yankinmu annoba.”

Wata muguwar harara ta maka masa ta cikin duhun. Sai kuma ta karɓi shantun hannunsa ta laluba daga can ƙarshensa ta fara warware wani siririn murfi da aka yi mata a jikin shantun. Ba daɗewa ta zazzago wasu kwayoyi guda biyu daga cikin shantun; suna kama da sabulun salo, ‘yan ƙanana, sai dai ɗaya baƙa ce ɗayar kuma fara. Ta ɗauki baƙar ta sunkuya saitin fuskar mutumin,

“A karo na ƙarshe zan ƙara tambayar ka… Wane ne oganka, me ke tsakaninsa da waccar budurwar da ya sanya ka binne ta, a ina kuke? Domin ban san ka a wannan ƙauyen ba.”

“Na ce ki kashe ni idan kina son…”

Kafin ya ƙarasa ta jefa masa baƙar kwayar a bakinsa, ta sa hannu ta matse bakin nasa har sai da ya haɗiye, sannan ta miƙe daga kansa tana sakar masa murmushin mugunta. Ta zaro wuƙarta ta yanke igiyar da ta riƙe masa ƙafa, sai ga shi ya faɗo tim! Ta ƙara haske shi da murmushi bayan ta dallare fuskarta da fitilar kwan,

“Tashi ka yi tafiyar ka. Ba Oganka ba ko ma waye ka ba shi wannan labarin idan har za ka iya. Yauwa, idan ka kasa ba da labarin kar ma ka sha wahalar neman magani, ka ga makarin maganin a cikin shantun wannan, ni kaɗai ce kuma nake da irin maganin nan. Oganka ko yana tafiya tsirara don tsafi bai isa ya samar maka magani ba, dole sai an neme ni. Ni din kuma ko labarina ba zai taɓa samu ba, tun da ba za ka iya faɗa masa ba. Na barka lafiya.”

Daga haka ta juya ta yi shigewar ta gida, Haadiru ya rufa mata baya yana waiwayensa.

Hakabiyya 2 >>

4 thoughts on “Hakabiyya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×