Skip to content
Part 14 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Yaraf! Ta faɗa kan gadonta tana sakin gunshekeken kuka ta ma rasa kalar tunanin da za ta yi.  Allah ya sani ta tsani mutumin nan tun kafin tasan waye balle yanzu da taji yana shirin rabata da farin cikinta. Shin ko taje gun Zawwa ta ce mata a nemo abokin Baba ta idasa cutar kanta ko kuwa ta ci gaba da nacewa Huzaif yana tura mata Mahaifinsa? Ta tuna fuskar mutumin sa’adda suka haɗa ido ya kafe ta da kallo. Kenan daga lokacin ya fara sonta har ya zo gidansu cikin mota yana cewa ta dinga killace masa kanta.

Dake kuma zuciyar yara gare shi ba zai yi nazarin abinda ya kaita gidan ɗansa a wannan lokacin ba, ba zai yi la’akarin ko soyayya suke ba. A’a shi kawai ya ganta yana so ya kuma nemi yaronsa ya masa hanya shi ga isasshe.

Ta ja tsaki mai ƙarfi tana miƙewa zaune tsakiyar gadon. Ta rafka tagumi hannu biyu tana nazarin abinyi. Ita mace ce dole ne tabi hanyar da za ta nemawa kanta mafita kafin Abokin Baba ya bayyana lamuranta su daɗa rincaɓewa. Ita zuciyarta dan Huzaif aka yi ta, ba za ta taɓa yarda ta yi wani abu da zai hanata samunsa ba ko menene kuwa. Ta nisa da ta tuna mafita ɗaya ita ce ta samu Mai Zubin Ghost cikin salama ta faɗa masa ita surukarsa ce, ta runtse ido ta buɗe jin jikinta na rawa tsabar kunyar kanta da ta ji.

Ta sake girgiza kai tana jin kawai ta dage da zuwa gidan Huzaif har shi Abban ya fahimci son ɗan nasa take yi, tasan dai dan sun zo gidansu Baba ba wani bi takansu zai yi ba tunda yana sane da ƙudurin Zawwa.

Da wannan tunanin ta ji hankalinta ya ɗan kwanta har ta samu damar barci.

Washegari ta tashi a kasalance ga gabanta da ke yawan faɗuwa akai-akai,  haka nan ta yi dukkan abinda za ta yi ta gama zuwa ƙarfe 10:00 za ta raka su Zawwa asibiti a yiwa tsoho Bawa general test, sun gama shiri tsaf sun fito harabar gidan suna jiran Baba Direba ya gyara paking, maigadi har ya wangale gate, hannunta na cikin na tsoho Bawa da ke zaune saman kujerarsa ta guragu, a lokacin da ta fara tura keken ne dan su ƙarasa jikin motar hancin wata baƙar mota ya sanyo kai cikin gidan, gabaɗaya suka bi motar da kallo a yayin da cikin Haƙabiyya ya bada wani irin sauti a sa’ilin da taga Huzaif ya fito daga motar Babansa ya biyo shi daga baya. Ta zabura za ta saki hannun Babanta ta ji ya riƙe ta ƙam, tabi  hannun da kallo da kallo taga hannunsa na kakkarwa haka bakinsa na rawa yana nuna Abban Huzaif. Ta kai kallonta ga Zawwa da ta kula ta ƙame ƙam bakinta a buɗe, ita maida kan Abban Huzaif da shi ma ya yi tsaye yana kallonsu idanuwansa na fidda kwallar da bata san dalili ba. A sannan ne kunnuwanta suka zuƙo mata muryar Baba na Kiran sunan Hameedu, ta waiwaiya a zabure taga wanda aka kira da Hameedun ya taho da sauri ya ture ta ya duƙa ya ƙanƙame Babanta yana hawaye.

Mararta ta tamke tam! Cikin firgici ta ɗaga ƙafarta da azama za ta bar gurin Zawwa ta yi caraf t riƙe mata hannu tana girgiza mata kai.

“Abokin Babanki ne Hameedu Siddiqu, maza buɗe musu sitting room ɗin Babanki, ki nutsu kuma!”
Ta furta mata tana mai juyawa ta dubi Hameedun da ke durƙushe gaban mijinta da ya nakasta. Wata sabuwar wutar tsanarsa ta sake ninkuwa a cikin zuciyarta. Ta kalli motar da ya shigo da ita ta kalli suturar da yake sanye da ita. Ai kawai sai ta ɗaya ƙafa  a kan takunta mai ƙarfi bayan ta saki siririn tsaki ta bar musu gurin.

Huzaif da ke gefe yana la’akari da ita ya bita da kallo yana jinjina inda Haƙabiyya ta gado tsiwa. Sai kuma ya matsa zuwa inda mahaifinsa yake yana saurararsu.

“Ka bar kukan nan haka Hamidu, zuciyata bata taɓa ƙullatarka ba, Allah shaidata ni zan bada labarin nagartarka, na bar kome a ƙaddararmu, na bar kome a bai faru ba, kawai dai na ji ciwon da ba ka sake nema na ba. Haba Hameedu idan na yi fushi da kai a kan dukiya ai ban cika mutum ba, abu ne fa da dukkanmu nan za mu tafi mu barta.”

Alhaji Hameed ya ƙara zurfin kukansa, ya duƙa sosai gabansa yana mai haɗe tafukan hannayensa.

“Ka yafe mini Bawa, domin mahallicinmu ka yafe mini, tabbas naso zuciyata, na so kaina a lokacin da bai kamace Ni ba, na ha’inceka irin ha’aintar da ban taɓa yafewa kaina ba. Duk wata walwalar rayuwa ina yi ne kawai ba tare da nasan daɗin hakan ba, banda sukuni Ko misqala zarratin tsawon shekarun nan Bawa ban huta ba gurin nemanka, ko wannan yaron shaida ne a saboda ban same ku ba duka farin cikin rayuwata ya tsaya cak! Ka ga yarinyar da ta yi silar zuwana nan ba tare da na san kai ne mahaifinta ba.”

Ya furta yana nuna saitin da Haƙabiyya ke tsaye tana kwalala ido, shi da Bawan suka nisa suna hango mafarin kome cikin idanuwansu.

March 1993

Awanni uku cur! Suka shuɗe yana duƙe kansa a ƙasa ya tsurawa tarin garwashin wutan da aka samar da shi ta hanyar tsafi a cikin wani kasko ido. Tun yana hawaye da zufa na azabar raɗaɗin wutar har sai da kansa ya juye ya tafi luu zai afka cikin kaskon, a sannan ne mummunan Dattijon da ke zaune daga wata kusurwa ya miƙe tsaye ya ɗaga sandar hannunsa mai mariƙin kan Mujiya ya nuna kaskon da ke gaban Huzaif da ita, a take kaskon ya ɓace ɓat! Huzaif ɗin ya kife a ƙasa.

“Wannan shi ne sakamakon tsallake wasu umarninmu da ka yi a tun fara aikin nan. Kuskure na gaba da zaka aikata zai zama a cikin garwashin wutan zan jefeka na gasa naman jikinka na bawa Mai Girma Jiji abinda ya rage ya mayar mini da kai koda sulallan Amurka ne.”

Ya nisa cikin wani irin ɓacin rai yana ɗaga sandar hannunsa ya sake nuna shi.

“Me yasa ta yi ciki? Me yasa kuma zaka ce a zubar da cikin?”

Huzaif ya cire kansa a wahalce ya dube shi da idanuwansa da suka rine da kwallar azaba.
“Ban san za ta yi ciki ba, kai ka ce mini cikin abinda zan sadaukar maka hadda kwayayen haihuwata, kai ka ce har abada ba zan haihu ba. Na so zubar da cikin ne saboda ba na son na saɓa umarninka, bana son kuma kasan da cikin.”

“Da ka zubar da yanzu kai da kaf zuri’ar taka sun ɓace daga doron duniya. Na sha faɗa maka abinda ba kuskure ba ne a gareka zai iya zama kuskure a gurinmu. Zubar da cikinta a yau ko mutuwarta a yau daidai yake da ɓacewata da ɓacewar Jiji da kuma asara ga Alhaji Hashimu da mummunar mutuwa ga mahaifiyarka, wannan shi ne abinda ya bayyana a gare mu…”

“…Sau biyu kana sakani karya alƙawarin abu mai girma, sau biyu kuma kana canja ra’ayinmu daga abinda muka niyyata, ba mu san irin asirin da kake da shi ba da yake yawan sawa kana samun galaba kan ra’ayinmu, duk da a wancan lokacin da muka baka zaɓi mun faɗa maka hatsarin abinda ka zaɓa, mun sanar maka kuskure ɗaya da za ka yi a tafiyar zai iya tarwatsaka ya tarwatsa dukkan lamuranmu, sai dai a saboda kafiya irin taka ka gwammace ka killace tsohuwar halittar da ta gama gajiya da zaman duniya ka ba mu sabuwar halitta, a sabuwar halittarma sai da ka hilacemu da irin daɗaɗan kalamanka muka sake ɗaga maka ƙafa kan mutuwarta da wani abu daban, to ka sani a yanzu ka riga da kayi kuskuren da dole ne ta mutu a ranar da muka ƙididdige, dole ne kuma ta mutu ita da abinda ke cikinta da haihuwarsa kai kanka zai iya zame maka bala’in da bai gama bayyana gare mu ba, ta yiwu idan mu ba muyi silar mutuwarka ba, shi ya zama silar mutuwarka, wannan wani abu ne da nake maka hasashensa idan har za ka yi kuskuren barin abinda ke cikinta a raye. Babu wani abu da muke buƙata a tare da su sai wannan jinin nata da zan ɗiba a ranar Ɗaya Ga Watan Ɗaya na shekarar Alif Ɗari Tara Da Casa’in Da Bakwai (1997), kaga kenan cikin jikinta watanni goma  nake so ta yi da shi, a ranar da ta fara naƙuda za ta mutu, a rannan kuma za ka tsira daga garemu Hashimu ma ya tsira da abinda yake so. Sai dai ka sani a saboda kuskuren haɗa kwan haihuwarka da ka yi da nata har ya samar da Ɗa, dole ne ka sadaukar mana da wata gaɓa na halittar da kake jinta tamkar uba gare ka, ka gane wa nake nufi, ka kuma gane abinda nafi buƙata gurinsa, nan da awanni 24  muke buƙatar hakan, wannnan ne kaɗai zai sanyaya zuciyar Jiji da ni kaina daga damuwar daka haifar mana…”
“…Tashi ka tafi, ka kuma cigaba da ƙoƙarin ganin ta gudun ko bata damar da za ta canja maka ra’ayi, da sannu watarana za ka wayi gari babu wata halitta koda ta kiyashi da za ta iya tsayuwa a kusa da kai.”

Huzaif ya fashe da kuka sosai yana ɗora hannunsa biyu aka, sai kuma ya zube a gabansa yana saka goshinsa a ƙasa tamkar zai yi masa sujjada ya kama buga kansa da ƙarfi yana mai tsananin roƙarsa da ayi masa afuwa.

Mummunan Dattijon ya juya zuwa kujerarsa ya zauna yana mai runtse idanuwansa. Bayan shuɗewar mintuna talatin ya buɗe idon yana mai ɗaga masa hannu daya tashi ya tafi.

Koda ya dawo tana nan kwance yadda ya barta hannuwanta a saman mararta idanuwanta a runtse, sai dai a yanzun babu hawayen sai wanda ya bushe a fuskarta.

Ya bita da kallo abubuwa da yawa na sake zame masa ciwo cikin ransa.

Ya sauke ajiyar zuciya yana mai ƙoƙarin bagarar da tashi damuwar. Dole ne ya kawo kayan girki ɗakin da kayan abinci da ruwan sha dan ta rayu cikin koshin lafiya zuwa lokacin da aka ware mata.

A yanzu hankali ya gama shigar shi har ya rasa inda zai aje shi dan yawa, a yanzu lokaci ne da baya buƙatar kowanne irin kuskure da zai sake nesantashi da cikar burinsa.

Sai dai fa akwai yiwuwar ya aikata wani abu kaɗan da zai tseratar masa da jininsa dake cikinta ba har haka zai bari a dama kunun da shi ba, ba kuma har haka zai bar bayansa ya ɓaci ba.

Dole ne ya cigaba da nunawa tosasshiyar ƙwaƙwalwarta hanyar tsira ko za ta fahimta ta gudu domin kanta, menene hanyar? Yawan Sallah da yawan Addu’a, kenan akwai buƙatar ya nuna mata hakan cikin dabara, akwai kuma buƙatar ya shigo da Alƙur’ani mai girma cikin wannan ɗakin, ya sani dukkan maganin wata lalura yana cikinsa,  ya sani kuma idan har ba shi ne ya buɗe baki ya ce ta tafi ba su Oga Tunjim ba lalle su gane shi ya mata hanya ba. Zuwa yanzu ya fara gane da yawa-yawan kalamansa ƙarya ne, idan har zai ce masa yana da ciwo alhalin ba yada shi, zai ce masa ba zai taɓa haihuwa ba alhalin shi bai san mustaqbal ba, ashe zai iya ce masa wani abu zai samu mahaifiyarsa ya zo kuma bai same tan ba.

Kenan ɓacewar Hamdiyya daga rayuwarsa ba lalle ya shafi wani nasa ba. To ko kuma ya yi ƙoƙarin ganin cikin ya zube ya sani idan wani abu bai faru ba za su yafe masa. To amma kuma har yaushe zai sake sadaukar da wani nasa saboda ita? Har yaushe zai sake ɗaukar lokaci yana aikata zunubin da bai san yadda zai bi ya nemi gafara ba?

Ya runtse ido da ƙarfi daya tuna a yanzu ma ɗan wannan kuskuren da ya yi an buƙaci ya sake ɓatawa wani nasa. To shin gaba kuma me zasu buƙata? Anya ya yiwa kansa adalci? Shin wai shi me ke hana shi yiwa nasa kan addu’a?,Me yasa tun fari bai tuna da addu’ar ba sai yanzu?

Wasu siraran hawaye masu ɗumi suka sauko masa ya fakaici idonta ya goge ganin ta tsura masa ido.

Cikin azabar ciwon mara ta shiga ƙoƙarin tashi, gaboɓin jikinta jinsu take tamkar an bubbuge mata su haka ta dafe bango ta miƙe tsaye ta tako a hankali zuwa inda yake tsaye.

“Ba na jin akwai azabar da za ta wanzu a rayuwata da zan ji tashin hankali ya same ni ko fargaba in dai har ina tare da kai. Ina nan akan bakana Huzaif ka zo mu gudu, ka kalli goshinka fa na tabbata sune suka ji maka ciwo.”

“Ke ki ƙyaleni dan Allah, ba ki tuna su Iya da ke can hankali tashe suna miki addu’ar jana’iza sai shashanci. Ba dai ba za ki tafi ba? To ki zauna anan zuwa lokacin da za ki haihu, sai na karbi ɗan ke kuma a kashe ki.”

Ya yi shiru ganin fuskarta ta wadatu da faraCikin fusata ya matso kusa da ita sosai.

“Wai kin yarda ki mutu saboda abinda baki san rayayye ba ne ko matacce, babu wani abu da za ki iya yiwa kanki ba tare da ni na sakaki a hanya ba? Ke wai anya kina da hankali?”

“Na yarda mana, fatana dama in bar Wanda zai mini Addu’a a bayan mutuwar tawa. Haka me zai dameni tunda ina tare da kai, na sani ba za ka taɓa bari a cutar da ni ba. Sai dai dan Allah kar ka sake buguna…”

‘…Yauwa Huzaif faɗa mini wanene Kai? Menene hadinka da matsafan?”

Ya mata wani banzan kallo yana nufar kan gadon da ta ɓata ya hau gyarawa, “ban sani ba, ba ki da hurumin yi mini wannan tambayar idan ba wani labarin ƙaryar kike so na baki ba, ki je kiyi sallah kiyi addu’a kuma.”

“Zan yi addu’a sosai, zan yi addu’ar da za mu ƙuɓuta tare. Ka yarda da Ni idan har abinda ke cikina zai rayu wallahi Huzaif na yarda na sadaukar da tawa rayuwar saboda shi, amma domin Allah ka faɗa muni gaskiyar da  gaske so na ko?”

Ya ja tsaki mai ƙarfi  yana ƙoƙarin bar mata ɗakin ta yi hanzarin tare shi.

“Ka kawon maganin ciwon mara.”

“Zan kawo wanda ya da ce da ki sha, kisa ranki a ruwan sanyi, ke yanzu ai har sai kinfi sarki jin daɗi, ba a son ko kuda ya taɓa lafiyar jikinki.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 13Hakabiyya 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×