Skip to content
Part 2 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Kallon ta yake yadda take shayar da jaririyar cikin farin ciki. Ya dubi jikinsa wanda awanni goma sha biyu da suka gabata yake a kalmashe. Ai sai ya ja guntulalliyar ƙafarsa ya yi sujjada ga Ubangiji Mai Girma a karo na uku. Ya ɗago ya ƙara kallon Zawwa da ke ta ƙoƙarin ganin jaririyarta na zuƙo ruwan nonon da ƙarfinta, sai abin ma ya ba shi dariya.

“Kai Zawwa! Allah shaidata ina matuƙar ƙaunarki.”
Ta ɗago ta masa farr! Da Ido.

“Ka faɗa sau goma kenan daga buɗewar bakinka zuwa yanzu… ba wani nan ma, ai marigayiya uwar Haadiru kake so.”

“To ke ban da abin ki, shekara nawa yanzun ina son yin magana ba damar yi? Ki bar ni na yi ta rera muku ita yau… Kayya! Ba na son tuna lamarin nan…, ya dan yi jim na alhini sai kuma ya nisa, Yauwa! Na faɗa miki ba a kishi da matacce fa, yanzu ai ke ce a gabana ko?”

Shiru ta yi tana duban kyakkyawar fuskar jaririyarta, a hankali ta fakaici idonsa ta ɗauke ‘yar kwallar da ta maƙale a nata gurbin idon.

“Ai an faɗa mini sa’ad da Baba ya ba ka ni, cewa ka yi ba ka so, me za ka yi da mace mai aikin maza, wai dan ina bin sa farauta.” Murmushi ya yi, ya shafi gemunsa da furfura ta fara ratsawa.

“Wannan gulma ce irin ta mutanen gari fa, ni na ƙiya ne wai ganin shekaruna sun doshi arba’in; ai na yi miki tsufa. To kuma sai kika nuna mini ban fi dan shekara 18 ba a idonki.” Ya ƙarasa yana fashewa da dariya. Sai kuma ya sauke idonsa kan jaririyar da ke gabanta.
“Wai ni wane suna za a saka wa ɗiyar nan? Na so a ce kin ji sunan mahaifiyar tata, kin ga da an mai da mata shi.”

“Yo kai ma Bawa matar da ke gaɓar naƙuda a tsakiyar titi ina za ta iya faɗar suna, wa ma zai iya tambayar ta? Kai dai mu gode wa Allah kawai da har shi Haadirun ya iya taimaka mata ta haihu da kanta kafin ta rasu. Yauwa! Ga wani zobe ma ta ba ni, ka gan shi kamar zinari ne, ta ce a saka wa ɗiyar idan ta girma.”
“Oh Allah wannan rayuwa! Ki ce har ta san abinda ta haifa kafin ta rasu?”

“Ai har ɗaukarta ta yi. Har yanzu ina tuno murmushin da ta bi ɗiyar da shi kafin ta kai ga kushewarta.”

Suka yi shiru gabaɗaya suna jinjina lamarin. Sai dai ita zuciyarta cunkushe take da tunanin ranar da Bawa zai gano a dalilin neman maganinsa ne ta sami jaririyar.

“Ai shi ke nan. Ina ganin a sanya mata Hameeda.”

Wata irin zabura ta yi ta miƙe, jaririyarta ta fashe da kukan razana. Jikinta na rawa ta dawo ta zauna daɓass tana dubansa a dugunzume.

“Wallahi Summa Tallahi ko sunan duniya ya ƙare ba za a saka mata Hameeda ba, kamar fa za a ce Hameedu ne… Haba dai Bawa… Kai jama’a! InnalilLahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!! Ban yafe masa ba wallahi, ba zan taɓa yafewa ba!!! Wato bayan kalmashe maka ƙafafu da ya yi har sace zuciyarka ya yi domin ka dinga begensa ko?” Sai kuma ta rushe da wani irin kukan baƙin ciki da ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarta. Jikinsa na rawa haka ya janyo ƙafarsa ya zo gare ta, gabaɗaya sun rikita shi; ita kuka jaririyarta kuka.

“Yi shiru! Ba yadda tunaninki ya ba ki ba ne… Haba Zawwa! Na fa faɗa miki ni har mancewa nake yi da wani Hameedu…”

“Ba ka mance da shi ba, da ka mance ɗazu ba za ka tura yaro gidansu ba daga miƙewarka. To bari ka ji abinda ba ka sani ba, ba za ka ƙara ganinsa ba a rayuwarka. Tun da ya yaudare ka, ya san ka gane, ya bar garin nan da duka danginsa, an ce yana ƙasar Turawa ma.” Ta furta, ta ja bakin zanenta tana fyace hanci, sai kuma ta ci gaba da rera kukanta.

“To ki yi shiru mana! Kai ni Bawa… Wai shin Zawwa me zan yi miki a rayuwa ne ki mance Hameedu da abinda ya yi da duk wata tsiyarsa?”

Tsit! Ta yi tana haɗiye kukanta. Ta zuba masa ido tana ƙare masa kallo daga sama har ƙasa, da ta iso kan dulgunminsa sai ta yatsine fuska tana shessheka,
“So nake yi ka sayar da gonarka da awakinka biyu mu bar garin nan, mu tafi can inda ba wanda ya san ba ni ce na haifi yarinyar nan ba, inda za ta yi karatu ta zama irin abinda nake mata buri. Ba ma a birnin wannan ƙaryar tamu za mu zauna ba, mu tafi wani birnin mai nisa sosai. Ni kuma na yi maka alƙawari daga ranar da muka bar nan ba zan ƙara ta da zancen Hameedu!”
Shiru ya yi yana nazarin zancenta. Ta wani ɓangaren shi kansa ya gaji da zaman ƙauyen, ta yadda labarinsa ya tamfatsa ko’ina har zuwa ake yi ana kallon sa, ga wanda amininsa ya cuta har ya nakasar. Hakan ma wata mafita ce, don haka ya gyaɗa mata kai alamun ya amince. Ta yi wani juyi tana guɗa, tamkar ba ita ke kuka yanzu ba, ta ƙara matse jaririyarta a jikinta, tana jin sonta da ƙaunarta har a ƙarshen tsokar da ke tsakanin ƙirjinta.

“Sunanta Haƙabiyya…”

Ya bi ta da wani kallo sororo.

“Haba Zawwa! Wane irin suna ne wannan? Ki saka mata na arziki mana… Ba gara irin su Hamdiyya ba, ko Huwaila, ko…”

“Allah sunanta kenan a gurina! Shi ne fa sunan da nake ce maka na yi wa kakata Habi alƙawarin zan sanya mata shi duk ranar da na sami ɗiya mace.”

Shiru kawai ya yi, tuna girman alaƙar da ke tsakaninta da Habi. Har a bayan ranta ga ta nan sabuwa dal a gurin Zawwa. Sai ya girgiza kai yana mai janyo sandunansa ya miƙe tsaye.

“Duk ranar da ta girma sai kun yi shari’a da ita kan wannan sunan, za ki ce na faɗa miki. Kuma ni da kaina zan tsaya mata ta kai ki har gaban ƙuliya manta sabo.”
Daga haka ya dogara ya fice daga ɗakin. Ita kuma ta bi bayansa da kallo, wani bushasshen murmushi na bayyana a saman fuskarta, ƙwafa ta yi, alamun abinda ke duƙunƙune a cikinta ya fi zare yawa!

KANO 1995

Ta waiga hagu da damarta, ta kasa kunne na ‘yan daƙiƙu ba ta ji motsin kome ba sai na ruwan da ke wucewa ta rariya, ta hanga ga ƙofar gidan da ke garƙame da Kwaɗo ta waje, ta maka mata harara ta murguɗa baki, sai kuma ta daka tsalle ta kama ‘yar katangar da ke gabanta, kamar kyanwa haka ta haye saman katangar, kana ta dire a ƙasa inda ta wanzu a cikin kangon ginin da ke jikin gidansu ta baya. Ta sunkuya ta tsittsince ‘yan kayanta da ta fara jefowa wajen, kana ta lafe daga lungun kangon ta buɗe jakarta ta ɗauko kazal da wata jar hoda. Ta zazzaga a hannunta ta fara ƙawata fuskarta da ita.

Ta daɗe tana kwalliyar kafin ta gama ta miƙe ta zaro wata shuɗiyar doguwar riga daga cikin jakar, ta ɗora akan kayan shan iskar da ke jikinta. Ta saka ɗan ƙaramin tarhar rigar, ta rataya zungureriyar jakarta. Har ta doshi hanyar fita daga kangon sai kuma ta dakata tamkar wacce aka tsayar, ta waigo tana duban can ƙarshen kangon inda wata curin ƙasa ke tare. A hankali ta saki wani yalwataccen murmushi. Ta ƙarasa ga kasar ta tone kaɗan ta zaro wani turare a kwalinsa. Ta rungume shi a ƙirjinta idanuwanta a lumshe, sai kuma ta buɗe ta fesa shi kaɗan a jikinta tamkar wacce bata so ya ƙare. Ta maida shi ma’ajiyarsa ta juyo ta fice daga gurin ta nausa hanyar da za ta maidata cikin gari. A ranta take godewa Allah da Kawunta da baya son jama’a su raɓe shi ya ƙaura daga cikin gari ya zo ƙarshen Kano yake zaune, inda babu ‘yan saka ido babu munafukai, babu handamammu, babu jarababbu, maƙotansu tsilli-tsilli ne, idan ba taro ake ba baka sanin da mutune a unguwar.

“Tun da tazarar kilomita goma tsakaninmu nake jiyo ƙamshin wanzuwarki gurin nan.”

Ya furta sa’ilin da ya miƙe ya isa gareta ya kama tattausan hannunta. Sai kuma ya saki hannun da sauri yana buɗe tafin, gashi nan wani gun ya farfashe wani gun ya yi jajur. Ya tamke fuska yana duban kwayar idanuwanta masu girma da sheƙi.

“Yanzun ma ta katangar kika fito ko? Ki daina dan Allah, zan fahimta idan har na jiki shiru na sha faɗa miki hakan.” Ya furta a tausashe.

Ta yi wal! Da ido tana duban siririn karan hancinsa. Ta sani dama sai ya yi ƙorafi, dan haka ta ɗau salon canja zancen.

“Kai kam ta yaya za ka ji ƙamshi na a tazarar kilomita goma? Ka kuwa san nisan.”

“Na sani fa, saboda hakan na mallaka miki turaren da na san zai yi wahala a samu mai irinsa domin kawai in dinga bambance ki cikin tarin mata, ke ko wani ya haɗa alaƙar jini da ke ko yake rayuwa a inda kike yi da na yi tozali da shi zan gane yana da alaƙa da ke, ina jin ko da a hali na makanta ne ba na kasa shaidaki Hamd…” Ta sanya hannu da sauri ta rufe bakinsa tana girgiza masa kai idanuwanta rau-rau.

“Allah ya raba ka da mutuwar tsaye, ina roƙon mahaliccinmu da idan da hakan a cikin ƙaddararka ya maido mini ita kaina, bana fatar wani mummunan abu ya same ka daga nan har ranar da babu ɓurɓushinmu. Ina Sonka sosai Huzaif, fiye da abinda idaniya ba ta iya ƙididdiga!”

“Ya ilahi! Hamdiyya!! Ki aure ni dan Allah, gobe, kin ji?”
Ya furta da wani irin yanayi da ya saka jikinta rawa ta dunƙule hannayenta cikin cinyoyinta tana ƙasa da idanuwanta.

“Ki dube ni dan Allah, za ki aure ni? In zo gun Kawu goben?”

Ta girgiza kai da sauri tana kallonsa da murmushi.
“Akwai lokaci, amma me ya sa tunda muke tare yau tsayin shekara guda kenan baka taɓa cewa in aure ka ba sai yau?”

“Ban sani ba fa, kawai yanzun na ji kin zama gabaɗaya rayuwata, ina jin kamar tazarar taku guda kawai za ki bada a tsakanimu da niyyar barina zuciyata ta tsarwatse na zama gawa. Da gaske da bugun zuciyarki rayuwata ke tafiya yadda ya dace. A dukkan numfashin da zan ja na fesar da tunaninki nake yinsa na kuma tabbata ke ce silar zamana hakan a yanzu. Ina sonki sosan gaske, ban ma san ta yaya zan fayyace shi ba ki gane ƙololuwar matsayinki a gare ni, ke, ko wuƙa za a siyo a tsaga zuciyar mu ƙididdiga soyayyarki da ke kewaye da ita?”

Ta saka dariya sosai tana duban wasu baƙin turawa da ke can gefensu suna ta ciye-ciye.

“Ni dai ina son irin Lemon can.. “

“An gama, da kuma me?”

“Da kuma zamowarka nawa ni kaɗai tal!”

“Kin samu, har abada ba na haɗa ki da wata, har abada, na rantse da Allah!”

Ta kyalkyale da dariya sosai tana dukan teburin da ke tsakiyarsu.

“Yanzu to menene na rantsuwar saboda Allah? Na yarda fa, na sani babu wata da za ka duba da sigar da ka dube ni. Na yarda da kai irin yardar da nake jin ko ba na raye ba za ka nemi wata da sunan soyayya ba.”

“Ai fa ki barni na rantse, kina gani jikina har rawa yake, ban taɓa jin son wata halitta ba irin yadda nake jin naki, kin kanainaye dukkan ruhina, ba na kaffara idan na rantse miki da mahallicina wannan iskar da nake zuƙa ina fesarwa da alfarmarki nake yi, da babu ke da tuni na daɗe da zama tarihi, ke ce tsanin cikar dukkan buri na, burin da saboda shi nake ƙara kusantarki a kowacce thaniya. Kar ki guje ni domin Allah Hamdiyya, kar ki juyan baya a kome da zai faru watarana, ki zamo mai yafiya gare ni. Dan Allah.”

“Huzaif! Ya isa dan Allah, kana sawa ina jin ba daɗi, ina saƙa wasu cunkusassun lamura marassa ma’ana, waya ce maka zan iya barinka? Wane ya ce maka za ka iya ɓatan ran da har zan ƙullace ka? Babu wannan abin, idan ma akwai ba zai yi tasirin da zai taɓa alaƙarmu ba ko da kuwa menene shi, ko da kuwa girmansa ya kai tafkin Nilu ba zan taɓa juya maka baya. Wallahi ka ji rantsuwa ba dan Kawu ba gobe zance ka fito. Amma baya so, haka ina son dukkan abinda yake so fiye da zatonka, banda haka…”

“Na gode Allah da ba fiye da ni kike son ba.”

Ya tari numfashinta yana kashe ta da ƙayataccen murmushi.

Hararsa ta yi tana miƙewa.

“Shi ke nan ma to ka ja na fasa maganar, kuma tafiya zan yi, Kawu ya kusa dawowa.

“To ‘yar Kawu, na ji, bari na rakaki har kwanar unguwar.”

“In dai ba ƙofar gida za ka rakani ba ai da sauki, ina maraba.”

Suka fara takawa a hankali.

“Ko za ki yi mini rakiya gida?”

“A’a, ka bari sai wani lokacin, yanzun sauri nake dan na ci tuwo miyar zogale da zafinsa, yauwa na tuna, yaushe za ka kai ni gurin Umman naka?”

“Garinmu da nisa sosai, kullum kina mantawa da hakan.”

“Amma tunda ka zo tsayin shekara guda ban ji ka ce mini ka tafi ganin gida ko ganin Umma ba.”

“Waya faɗa miki? Idan na ce miki a kowane dare ina zuwa can ba lalle ki yarda ba.

“Ehn.. Za ka fara cukurkuɗa magana irin ta masu lalura ko? Bari dai na kawo ƙarshen kome, watarana da daren za ka ganni tsulum a gidanka, sai na rakaka ziyarar ganin gidan da kake zuwa.”

Ya yi dariya sosai mai haɗe da tari.

“Ina fatar hakan, wannan ma buri nane.”

“Ka kula kana da burirrika da yawa…?”

“Amma kuma ke kike lulluɓe da dukkan burikan ai, ke dai Allah Ya nuna mini ranar da za ki zo da daddaren.”

“Amin Huzaifatu.”

Ta furta tana mai harɗe hannunwansu tamkar turawan da aka gayyata rawa tsakiyar taro.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 1Hakabiyya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×